DSS Ta Gurfanar da Manyan Wadanda Ake Zargi da Hannu a Hare Haren Jihohi 2 na Arewa
- Hukumar DSS ta fara kokarin ganin an hukunta duk wanda ke da hannu a kashe-kashen da suka faru kwanakin baya a jihohin Filato da Benuwai
- Tun bayan faruwar mummunan lamarin, jami'an tsaro sun cafke wasu mutane, wadanda ake zargi da hannu a kashe-kashen
- Mutane da dama sun rasa rayukansu a hare-haren da miyagu suka kai garuruwa daban-daban a jihohin guda biyu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hukumar Tsaro (DSS) ta gurfanar da mutum tara da ake zargi da hannu a kashe-kashen rayukan bayin Allah a jihohin Filato da Benuwai.
Wadanda DSS ta maka a Kotu su ne manyan wadanda ake zargi da kitsa wannan danyen aiki daga cikin mutanen da aka kama da hannu a tashin hankalin jihohin biyu.

Source: Facebook
Channels tv ta ce an gurfanar da su ne a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar Laraba, 3 ga watan Satumba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
DSS ta gurfanar da mutum 9 a gaban Kotu
Hukumar DSS ta kuma tuhumi wani da ake zargi da safarar makamai da aka kama da bindigogi M16 guda bakwai.
A cikin wadanda aka gurfanar akwai Haruna Adamu da Muhammad Abdullahi, ‘yan asalin karamar hukumar Awe a Jihar Nasarawa.
Ana tuhumar wadannan mutane biyu da aikata laifuffuka hudu da suka shafi kashe rayukan fararen hula a kauyukan Abinsi da Yelewata na karamar hukumar Guma, jihar Benuwai.
Hukumar DSS na zargin sun aikata laifin ne a ranar 13 ga Yuni, 2025 tare da wasu da har yanzu ba a kama ba.
DSS ta kuma tuhumi Terkende Ashuwa da Amos Alede, ‘yan asalin Guma a jihar Benuwai, da laifuka uku da suka shafi harin ramuwar gayya ga wadanda ake zargi na farko a Ukpam.
Yadda DSS ta shigar da tuhume-tuhume a kotu
Ta kuma gurfanar da Halima Haliru Umar, mai shekaru 32 daga karamar hukumar Faskari a Katsina, kan laifuffuka hudu na rashin tona asirin Alhaji Sani, wanda ake zargi da safarar makamai, ta’addanci da satar mutane.
Bugu da ƙari, DSS ta shigar da tuhume-tuhume guda shida kan Silas Iduh Oloche daga karamar hukumar Agatu, jihar Benuwai, bisa zargin mallakar bindigogi 18 da ƙananan bama-bamai ba tare da lasisi ba.

Source: Facebook
Sai kuma Nanbol Tali, mai shekaru 75, da Timnan Manjo, ‘yan asalin Jihar Filato, wadanda DSS ta gurfanar kan tuhume-tuhume guda hudu na cinikim bindigogin AK-47 guda biyu ba tare da lasisi ba.
Danjuma Antu, mai shekaru 62 daga Jos ta Arewa, Jihar Filato, shi ma ya fuskanci tuhume-tuhume guda biyar bisa zargin mallakar bindigogi na gida guda biyu da wasu makamai ba bisa ka’ida ba, rahoton TVC News.
A watannin baya-bayan nan, ‘yan bindiga sun kai hare-hare a Filato da Benuwai, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.
DSS ta kama shugaban kungiyar Mahmuda
A wani labarin, kun ji cewa jami'an DSS sun samu nasarar kama shugaban Mahmuda, kungiyar yan ta'addan da ta bulla kwanakin baya a Najeriya.
Wasu mazauna jihohin Kwara da Neja, musamman a yankunan da ke iyaka da Jamhuriyar Benin sun yi farin ciki da kama jagoran Mahmuda.
Wasu daga cikin mazauna jihohin sun ce jami’an DSS sun kama jagoran Mahmuda da ransa, sannan suka garzaya da shi zuwa wani wurin da ba a bayyana ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

