Katin Zaben 2027: Borno Ta Zarce Jihohin Arewa, Osun Ta Wuce Kano da Kaduna

Katin Zaben 2027: Borno Ta Zarce Jihohin Arewa, Osun Ta Wuce Kano da Kaduna

  • Hukumar INEC ta bayyana cewa sama da ‘yan Najeriya miliyan 2.5 ne suka fara rajistar zabe ta yanar gizo tun daga 18 ga Agusta, 2025
  • Rajistar matasa da dalibai ta fi yawa inda kaso 63 ke tsakanin masu shekaru 18 zuwa 34, dalibai kuma sun kai kashi 25 na masu rajistar
  • INEC ta bayyana yadda jihohin Kudu ke cigaba da jan ragamar rajistar yayin da jihohin Arewa kamar Borno da Kaduna ke bin su a baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja Abuja – Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa sama da ‘yan Najeriya miliyan 2.5 ne suka riga suka fara rajistar katin zabe ta yanar gizo.

Hakan na zuwa ne bayan shafe mako biyu da kaddamar da tsarin rajistar masu kada kuri’a a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ba imani: Mahaifiya ta daure jaririyar da ta haifa ta birne ta da rai a dajin Kebbi

Katin zabe da hukumar INEC ke samarwa a Najeriya
Katin zabe da hukumar INEC ke badawa a Najeriya. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in INEC, Sam Olumekun, ya fitar a ranar Talata, 2 ga Satumba, 2025 a shafin hukumar na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, zuwa ranar Lahadi 31 ga watan Agusta, adadin masu rajista ya kai 2,532,062 inda mata suka fi rinjaye da kaso 51.88, yayin da maza suka kai kaso 48.12.

Yadda tsarin rajistar INEC ke tafiya

Olumekun ya bayyana cewa tsarin rajista ta yanar gizo shi ne matakin farko, amma dole ne mai rajista ya bayyana a ofishin hukumar da ke kananan hukumomi ko jihohi.

Mutum zai bayyana a ofishin INEC ne domin hukumar ta dauki hoton fuskarsa da kuma bayanan yatsunsa.

Ya ce hukumar na da ofisoshi 811 a fadin kasar nan da za su karbi masu rajista daga ko ina suka fito a fadin Najeriya.

Ya kara da cewa shafin yanar gizo na hukumar yana aiki a kowane lokaci, har da karshen mako, don baiwa ‘yan Najeriya damar shiga daga ko’ina suke a duniya.

Kara karanta wannan

NDLEA ta kama tsoho mai shekara 70 da miyagun kwayoyi, an lalata gonar wiwi

Jihohin da suka fi rajista katin zabe

A cikin jerin jihohin da suka fi yin rajista, Osun ce ja gaba da adadin mutane 474,372, sannan Lagos 355,372, sai Ogun mai 265,399.

Babban birnin tarayya Abuja (FCT) ya samu masu rajista 52,250, Borno 135,661, Oyo 128,231, da Kaduna mai mutane 127,852.

Sauran su ne Kogi 124,239, Kebbi 113,884, Yobe 101,622, Kano 29,042, yayin da Enugu ta samu 856, sai Ebonyi kuma 490.

Za a cigaba da rajistar ne har zuwa shekarar 2026 domin ba 'yan Najeriya damar mallakar katin zaben 2027.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu. Hoto: INEC Nigeria
Source: Getty Images

Hukumar INEC ta yi wa jama'a godiya

INEC ta nuna gamsuwa da irin yadda ‘yan kasa suka nuna sha’awar rajista, tare da yabawa kungiyoyin farar hula da ke tallafawa wajen wayar da kan jama’a.

Tashar Arise ta wallafa cewa INEC ta ce:

“Mun gode wa ‘yan kasa da kuma kungiyoyin da ke karfafa yin rajistar masu kada kuri’a,”

Kara karanta wannan

2027: INEC ta fadi me ya sa Osun ta fi Kano, jihohi 34 yawan rajistar katin zabe

Legit ta zanta da Fatima Muhammad

Wata daliba 'yar asalin jihar Gombe, Fatima Muhammad ta bayyanawa Legit cewa har yanzu ba ta yi rajista ba.

Ta zantawa Legit cewa:

"Har yanzu ban yi rajista ba, ban ma taba katin zabe ba, amma zan yi a gaba."
"Zan samu lokaci kafin zuwa lokacin da za a rufe na yi, saboda yanzu muna makaranta"

Osun ta fi Kano rajistar katin zabe

A wani rahoton, kun ji cewa kakakin 'jam'iyyar adawa ta ADC, Bolaji Abdullahi ya yi magana kan yawan masu yankar katin zabe a Osun.

Hukumar INEC ta yi martani da cewa ba yau aka fara samun masu yankar kati suna da yawa a jihar Osun ba, saboda haka ba abin mamaki ba ne.

A makon farko da aka yi da bude shafin masu yankar katin zabe ta yanar gizo a Najeriya, jihar Osun ta wuce Kano, Kaduna da sauransu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng