Fadar Shugaban Kasa Ta Bayyana Dalilin Baiwa Jihar Legas Fifiko wajen Ayyukan Raya Kasa
- Fadar Shugaban kasa ta yi martani ga koken jama'a a kan yadda ta zuba manyan ayyukan ci gaba a jihar Legas fiye da sauran jihohi
- A jawabinsa, hadimin Shugaban Kasa, Daniel Bwala ya ce jihar Legas na da muhimmanci na daban ga dukkanin Najeriya
- Ya bayyana cewa duk aikin da aka yi a Legas, dukkanin 'yan kasa ne za su ci gajiyarsa saboda rawar da jihar ke taka wa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Legas – Mai ba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan sadarwar, Daniel Bwala, ya bayyana Jihar Legas a matsayin “ƙasar kowa” kuma alfaharin tattalin arzikin Najeriya.
A cewar Bwala, mayar da hankali da gwamnatin Bola Tinubu ta yi wajen zuba manyan ayyukan gwamnatin tarayya a Legas ba nuna wariya ba ne ga sauran bangarori.

Source: Twitter
Ya bayyana haka ne a shirin Daybreak a Arise Television a ranar Laraba, inda ya ce ya kamata al’umma su fahimci cewa duk abin da aka zuba a Legas, ƙasa baki ɗaya ce ke cin gajiyarsa.
Bwala ya kare gwamnatin Tinubu
Jaridar Punch ta wallafa cewa dukkanin ayyukan da ke jihar Legas a yanzu, jari ne ga kasar nan da kowa zai amfana da su.
Bwala ya ce:
“Abin da ya bambanta Legas da sauran jihohi shi ne kasancewarta ƙasar kowa. A zaben baya ma, Shugaban Ƙasa Tinubu wanda ya fito daga yankin Yarbawa bai samu Legas ba. Wannan ya nuna irin haɗin kan al’ummomi da Legas take da shi.”

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa:
“Mai kudin Afrika, wanda ba daga Kudancin Najeriya ba ne, ya kafa manyan kamfanoninsa a Legas. Haka kusan dukkannin manyan attajirai na ƙasar suna da jari a Legas. Idan ba don yawan masu magana da Yarbanci ba, mutum zai iya zaton Legas na da alaƙa da kowane yanki.”
Daniel Bwala: Legas ta kowa ce
Bwala ya kwatanta Legas da cibiyoyin tattalin arziki na duniya kamar Landan, New York da Paris, inda ya ce a kowace ƙasa akwai wuri guda da ya fi sauran jihohi ko yankuna kayayyakin more rayuwa.
Ya ce:
“Landan tana da jari fiye da dukkannin sauran jihohin Ingila. New York ta fi sauran jihohin Amurka, har da California, samun jari. Paris ma haka take."
"Don haka, idan ka ga gwamnati na mayar da hankali wajen zuba jari a cibiyar kasuwanci, ba wai fifiko ba ne, jari ne da zai ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.”
Bwala ya jaddada cewa adadin ayyukan gwamnatin tarayya da ya kai kusan Naira tiriliyan 3.9 da aka zuba a Legas cikin shekara biyu abin kwarai ne.
Ya ce hakan ya tabbatar da matsayin Legas a matsayin cibiyar kasuwanci da ginshiƙin cigaban ƙasar.
A cewar sa:
“Don haka tunanin cewa Legas na samun ayyuka fiye da sauran jihohi bai dace ba. Legas ƙasar kowa ce. Ita ce cibiyar Najeriya kuma ita ce alfaharin ƙasar.”
An sako gwamnatin Tinubu a gaba
A wani labarin, mun wallafa cewa Salihu Tanko Yakasai, wanda aka fi sani da Dawisu, tsohon hadimin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya soki gwamnatin APC.
Ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna jerin ayyukan raya kasa a Arewa da bai dace ba, inda ya zargi cewa wasu daga cikin kwangilolin da aka lissafa bogi ne.
Dawisu ya bayyana cewa an shirya “yaudarar jama’a” ta hanyar ƙirƙirar bayanai marasa tushe game da manyan tituna a yankin Arewa wadanda idan aka je wurin, babu su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


