"Yan Arewa ba Wawaye ba ne": Kwankwaso Ya Taso El Rufai a Gaba kan Sukar Shugaba Tinubu

"Yan Arewa ba Wawaye ba ne": Kwankwaso Ya Taso El Rufai a Gaba kan Sukar Shugaba Tinubu

  • Maganganun da Nasir El-Rufai ya yi a kan gwamnatin mai girma Bola Tinubu na ci gaba da tayar da kura a fagen siyasar kasar nan
  • Babban kusa a jam'iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso ya shiga cikin sahun masu sukar tsohon gwamnan na jihar Kaduna
  • Jigon na APC ya bayyana cewa Malam El-Rufai ba zai yi nasara ba a kulle-kullen da yake yi don ganin gwamnatin Tinubu ta fadi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Babban kusa a jam’iyyar APC a Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso, ya ragargaji tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai kan sukar Bola Tinubu.

Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya zargi Malam Nasir El-Rufai, da amfani da karya da kazafi kan Shugaba Bola Tinubu.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya ragargaji El-Rufai
Hotunan Nasir El-Rufai, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Musa Iliyasu Kwankwaso Hoto: Nasir El-Rufai, Musa Iliyasu Kwankwaso, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Kano ranar Talata, 2 ga watan Agustan 2025, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Biyan 'yan bindiga kudi: Baba-Ahmed ya yi wa El Rufai raddi mai zafi

Musa Kwankwaso ya ragargaji Nasir El-Rufai

Ya bayyana hanyar da El-Rufai ya dauka a matsayin tsohuwar dabara wadda tuni aka daina amfani da ita.

"Ba za ka iya kifar da Shugaba Bola Tinubu daga kujerarsa a 2027 ta hanyar amfani da dabarar da ka yi wa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan a 2015 ba."
"Wato ta hanyar amfani da talauci, rashin tsaro da durkushewar tattalin arziki. Sharrinka a fili yake ga kowa."
"A bayyane yake ga 'yan Najeriya cewa Shugaba Tinubu ya cimma abubuwa da dama ta hanyar sauya salon mulki, inda wurare da dama suka fara samun tsaro, farashin kaya kuma suna raguwa a hankali."
"Ana shawo kan rashin tsaro da Shugaba Tinubu ya tarar da shi a lokacin da ya hau mulki, godiya ga Malam Nuhu Ribadu. Amma mutane irin su El-Rufai ba sa farin ciki da wadannan nasarorin."

- Musa Iliyasu Kwankwaso

Kwankwaso ya kalubalanci Malam El-Rufai

Kara karanta wannan

"Ana yiwa Arewa aiki," Musa Kwankwaso ya hango manyan 'yan adawa za su koma APC

Kwankwaso ya kalubalanci El-Rufai da ya kawo hujjar zargin da yake yi cewa gwamnatin Tinubu tana daukar nauyin ‘yan bindiga da sauran miyagun ayyuka a fadin kasar nan, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya soki El-Rufai
Hoton jigon APC a Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso Hoto: Musa Iliyasu Kwankwaso
Source: Facebook
"Idan ba ka da wata shaida kan wadannan zarge-zarge, ka rufe bakinka ka bar gwamnati ta ci gaba da aikata alherin da take yi wa ‘yan Najeriya."

- Musa Iliyasu Kwankwaso

Kwankwaso ya yi zargin cewa El-Rufai kawai yana kokarin tunzura 'yan Arewa ne kan gwamnatin Tinubu.

Sai dai ya bayyana cewa 'yan Arewa ba wawaye ba ne, don suna gani abin da gwamnatin Tinubu ke yi daga Birnin Gwari zuwa Sokoto har zuwa Borno.

Musa Kwankwaso ya magantu kan tazarcen Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso, ya tabo batun tazarcen mai girma Bola Tinubu a zaben shekarar 2027.

Jigon na jam'iyyar APC ya bayyana cewa babu wasu 'yan kulle-kulle da makirce-makircen siyasa, da za su hana Shugaba Tinubu sake darewa kan mulki a wa'adi na biyu.

Kwankwaso ya nuna cewa shugaban kasan ya samu nasarori masu yawa wadanda ya kamata su sanya ya sake lashe zabe a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng