Gwamnatin Tinubu ta Bada Hutun Maulidin Annabi Muhammad SAW, Ta Aika Sako ga Musulmi

Gwamnatin Tinubu ta Bada Hutun Maulidin Annabi Muhammad SAW, Ta Aika Sako ga Musulmi

  • Gwamnatin Najeriya ta taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar watan Maulidin Fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W)
  • Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ya sanar da cewa gwamnati ta ba da hutun kwana daya domin murnar haihuwar Annabi
  • A lissafin fadar Sarkin Musulmi ta Najeriya, ranar Juma'a, 5 ga watan Satumba, 2025 ita ce ta zo daidai da ranar 12 ga watan Rabi'ul Awwal, 1447AH

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta ba da hutun Maulidin Annabi Muhammad (S.A.W).

Gwamnatin ta ayyana ranar Juma’a, 5 ga Satumba, 2025 daidai da 12 ga watan Rabi'ul Awwal, 1447AH a matsayin ranar hutun bikin Maulidi na bana.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Hoton Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr Magdalene Ajani, ta fitar ranar Talata a Abuja, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

"Yan Arewa ba wawaye ba ne": Kwankwaso ya taso El Rufai a gaba kan sukar Tinubu

Sanarwar ta ce Ministan Cikin Gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo, shi ne ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya.

Gwamnatin Tinubu ta aika sako ga Musulmi

Dr Tunji-Ojo ya mika sakon fatan alheri ga musulmi a Najeriya da ma duniya baki ɗaya bisa zagayowar wannan rana mai daraja.

Ministan ya bukaci al’ummar Musulmi su yi koyi da kyawawan halayen Manzon Allah (SAW) na zaman lafiya, kauna, tawali’u, hakuri da jinƙai, yana mai jaddada cewa waɗannan dabi’u su ne ginshiƙai wajen gina ƙasa ɗaya mai ci gaba.

Ya kuma kira ‘yan Najeriya masu bin addinai daban-daban da su yi amfani da wannan lokaci wajen roƙon Allah ya kawo wa ƙasar zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali.

Minista ya ja hankalin 'yan Najeriya lokacin Maulidi

Tunji Ojo ya kuma bukaci daukacin yan Najeriya da su mara wa gwamnati baya wajen tabbatar da haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa.

Sanarwar ta kuma nakalto Tunji-Ojo yana cewa:

Kara karanta wannan

An yi rashi: Mace ta farko da Tinubu ya nada shugabar ma'aikatan Abuja ta rasu

“Bikin Maulid na ba mu damar ƙarfafa zumunci, inganta zaman tare cikin lumana da kuma koyon darussa da kyawawan dabi'un Manzon Allah na mutunta juna da sadaukar da kai.”
Ministan cikin gida, Tunji-Ojo.
Hoton ministan harkokin cikin gida, Dr. Tunji-Ojo yana gabatar da jawabi a wurin taro Hoto: @BMOOfficial
Source: Facebook

Haka kuma, ya shawarci jama’a da su kasance masu bin doka da oda, su kasance masu kula da harkokin tsaro, tare da mara wa manufofin gwamnati baya domin inganta walwalar kowa da kowa.

Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ya kuma yi wa musulmi fatan alheri, farin ciki da zaman lafiya a bukukuwan Maulidi da suka fara na bana a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito wannan.

'Yan sanda sun shirya ba yan Maulidi tsaro

A wani labarin, kun ji cewa yan sanda sun tabbatar da cewa an ɗaukin tsauraran matakan tsaro domin gudanar da bukukuwan Mauludi cikin kwanciyar hankali a Jigawa.

Rabi’ul Awwal shi ne wata na uku a kalandar Musulunci, kuma Musulmai a duniya ke girmamawa saboda shi ne watan da aka haifi Annabi Muhammad S.A.W.

Kungiyar Zawiyya Islamiyya ta gana da rundunar 'yan sanda a Jigawa domin tattauna muhimman batutuwa kan Maulidin bana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262