Masu Garkuwa Sun Sato Bala'i a Kano, Wanda Suka Kama Ya Tona Musu Asiri

Masu Garkuwa Sun Sato Bala'i a Kano, Wanda Suka Kama Ya Tona Musu Asiri

  • ’Yan sanda a Kano sun cafke wani mutum da ake zargi da garkuwa da mutane tare da wasu abokan harkallarsa a karamar hukumar Shanono
  • Mutumin da aka kama ya amsa cewa shi da wasu sun yi garkuwa da mutane da dama ciki har da kisan wani mutumi da yake kauyen Faruruwa
  • Rahotanni sun nuna cewa har yanzu ana ci gaba da kokarin kamo sauran abokan mutumin da aka cafke bayan sun tsere da aka kama shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani gungun masu garkuwa da mutane bayan samun bayanai daga wanda ya tsere daga hannun su a Shanono.

Lamarin ya faru ne bayan Kabiru Umar na kauyen Faruruwa, wanda aka yi garkuwa da shi tun watan Mayu, ya bayyana sunan wani daga cikin wadanda suka sace shi.

Kara karanta wannan

Manyan jami’an gwamnatin Kano da ake zargi da rashin gaskiya a zamanin Abba

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Bakori
Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Bakori. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanai kan yadda aka kama 'yan ta'addan ne a cikin wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa bincike na ci gaba tare da tabbatar da an cafke wadanda ke da hannu a wannan aika-aika.

Yadda asirin masu garkuwa da mutane ya tonu

Wanda aka yi garkuwa da shi, Kabiru Umar, ya shaida cewa ya gano daya daga cikin wadanda sace shi mai suna Inuwa Yusuf, dan shekara 30 daga kauyen Faruruwa.

Bayan fara bincike game da dan ta'addan, ’yan sanda sun tabbatar da cewa an kama Yusuf a ranar 31 ga watan Agusta 2025.

A lokacin da ake tambayarsa, ya amsa cewa shi ne ya taka rawa a garkuwa da Kabiru da kuma wasu mutane da dama a yankin.

Wasu bayanan da bincike ya gano

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa Yusuf da abokan harkallarsa sun kasance cikin wani gungu na garkuwa da mutane da kuma kisan kai.

Kara karanta wannan

An gudu ba a tsira ba': Sarki ya faɗi yadda mutane 13 suka mutu a kogi a tsarewa yan bindiga

Ya bayyana cewa sun kashe wani mutum mai suna Malam Isyaku na kauyen Faruruwa, lamarin da ya girgiza mazauna yankin.

Wasu daga cikin makaman da aka kama a Kano a Agusta
Wasu daga cikin makaman da aka kama a Kano a Agusta. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Wannan ya sa aka cafke wasu karin mutane da ake zargi da hannu a harkar, ciki har da Ibrahim Shuaibu, Aminu Sani, Kabiru Moh’d dukkansu daga Faruruwa da kuma Buhari Habu daga Katsina.

Ana shirin cafke sauran masu garkuwa

Majiyoyi sun tabbatar da cewa jami’an tsaro na ci gaba da bin sawun sauran mambobin gungun domin kawo ƙarshensu a Kano.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da tabbatar da tsaro a dukkan fadin Kano, musamman ganin cewa lamarin garkuwa da mutane ya fara ƙaruwa a jihar.

An kama masu garkuwa da mutane a Kano

Mun rahoto cewa a watan Agustan da ya wuce, 'yan sanda sun kama wasu mutane takwas da ake zargi da garkuwa da mutane tare da kwato bindigogi takwas a Kano.

Kakakin 'yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da labarin, inda ya ce za su cigaba da kokarin kawo karshen lamarin.

Baya ga haka, an kama 'yan daba sama da 60, barayin babura da motoci, tare da kama wasu makamai daban daban a jihar cikin wata daya kacal.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng