Abba Gida Gida zai Ƙaddamar da Majalisar Shura ta Jihar Kano
- Gwamnatin Kano ta bayyana cewa shirye shirye sun yi nisa wajen kafa Majalisar Shura da za ta rika tallafa wa Abba Kabir Yusuf da shawarwari
- Sanarwar da Kwamishinan yada labaran jihar, Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ta bayyana cewa tuni aka sanya ranar kaddamarwar
- Ya ce Majalisar ta kunshi manyan mutane da ake sa ran za su karafafa salon mulkin gwamnatin Kano domin ci gaban al'ummar da su ka zabe ta
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta shirya kaddamar da sabuwar majalisar shura da aka sake kafa wa domin inganta harkokin gudanarwa.
Bayanin hakan na kunshe a cikin sanarwar da Kwamishinan yada labarai na Kano, Kwamred Abdullahi Ibrahim Waiya ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan
Likitoci sun shata wa gwamnatin Tinubu layi, za su dauki mataki a cikin kwanaki 10

Source: Facebook
Sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Fcaebook na cewa za a kaddamar da kwamitin a ranar Litinin, 8 ga watan Satumba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba zai kaddamar da majalisar shura
Sanarawar ta kara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ne zai jagoranci kaddamar da kwamitin a gidan gwamnati da ke Kano.
Ta ce an kafa majalisar shura ne domin karfafa mulkin dimokradiyya da hadin kai da kuma bayar da shawarwarin da za su kawo ci gaba a Kano.
Ana sa ran za ta zama majalisar ba da shawara ga gwamnatin jihar, tare da ba haska manufofi da shirye-shirye da za su ci gaba da tafiyar da manufar ci gaba a jihar.
Sanarwar ta ce:
"Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da jajircewa a wajen gudanar da mulkin da ya shafi jama'a, zai yi amfani da wannan dama wajen bayyana manufofin majalisar, tare da sake jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da rikon amana, da adalci da kuma shigar 'yan kasa tsarin tafiyar da mulki domin tabbatar da cewa aiki ya isa ga jama'a."
Su wanene wadanda Majalisar shura ta kunsa?
Sanarwar ta kara da cewa Majalisar shura ta kunshi manyan mutane, wadanda ke wakiltar muhimman bangarori daban-daban.
Ta kara da cewa haka kuma ana ganin wannan zai tabbatar da daidaito da wakilci a dukkannin bangarori na al'ummar Kano.

Source: Facebook
Sanarwar ta ce dukkanin 'yan majalisar, da kuma baki da aka gayyata, za su halarci taron, da ake fatan zai kara hade kan mutanen Kano.
An ji cewa gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da daukar wani muhimmin mataki na karfafa akidar dimokuradiyya ta taimakon 'yan kasa.
Gwamnatin Kano ta raba mukamai ga malamai
A wani labarin, kun ji cewa a wani mataki na tabbatar da haɗin kan al'umma da inganta tsarin mulki, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya samar da 'yan majalisar Shura ta jihar.
An tsara majalisar domin bayar da shawarwari kan al'amuran da suka shafi tattalin arziki, zamantakewa, da addini, tare da tabbatar da ingantaccen jagoranci a jihar.

Kara karanta wannan
Ana hallaka jama'ansa, Gwamna Radda zai kashe Naira miliyan 680 a gyaran maƙabartu
An nada Farfesa Shehu Galadanci a matsayin shugaban Majalisar, yayin da Farfesa Muhammad Sani Zahraddeen zai kasance mataimakinsa sai Gwani Shehu Wada Sagagi, Sakatare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
