NiMet: Za a Sheka Ruwan Sama a Kebbi, Zamfara da Jihohin Arewa 19 a Ranar Laraba
- Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama da tsawa a sassa da dama na Arewa da Kudancin Najeriya a yau Laraba
- Hakanan, hukumar ta ce wasu jihohin kasar nan za su iya fuskantar ruwan sama tun daga safiya har zuwa dare, watau narke-gari
- NiMet ta shawarci mazauna wuraren da ruwa ke yawan taruwa da su yi taka tsantsan, saboda akwai yiwuwar samun ambaliya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Hukumar NiMet ta fitar da rahoton yanayi na ranar Laraba, 3 ga Satumba, 2025, inda ta ce za a samu ruwa da tsawa a jihohi daban-daban na ƙasar.
Rahoton ya bayyana cewa hasashen yana da inganci daga ƙarfe 00:00 na safiya zuwa 23:59 na daren Laraba, kuma ya shafi jihohin Arewa da da Kudu.

Source: Original
Legit Hausa ta samu bayanai game da hasashen yanayin a rahoton da NiMET ta wallafa a shafinta na X a daren Talata, 2 ga Satumba, 2025.
Hasashen ruwan sama a jihohin Arewa
A safiyar Laraba, ana sa ran ruwan sama hade da tsawa zai sauka a jihohin Kebbi, Zamfara, Sokoto, Gombe, Bauchi, Taraba, da Adamawa.
Hakanan, za a ci gaba da samun ruwan a wasu jihohin, ciki har da Jigawa, Borno, Bauchi, Gombe, Adamawa, Taraba, Yobe, Katsina, Kano, Kaduna, Zamfara, Sokoto, da Kebbi.
NiMet ta ce ana iya samun ruwan sama mai karfi tare da iska, wanda zai iya kawo ƙarancin gani yayin tuki, kuma zai iya jawo ambaliya.
Hasashen ruwa a Arewa ta Tsakiya
A shiyyar Arewa ta Tsakiya kuwa, NiMet ta ce Abuja da jihohin Plateau, Nasarawa, Niger, da Benue za su samu ruwa da tsawa mai sauƙi.
A yammacin yau kuwa, za a samu ruwa mai matsakaicin karfi, na tsawon lokaci, a Abuja da jihohin Nasarawa, Benue, Niger, Plateau, Kogi, da Kwara.

Kara karanta wannan
Lahadi: Ruwan sama da iska mai ƙarfi zai sauka a Abuja, Neja, Yobe da wasu jihohi
Hukumar ta shawarci mazauna wannan yanki da su yi taka tsantsan yayin tafiye-tafiye, kuma su kaurace wa wuraren da ke da hadarin ambaliya.
Hasashen yanayi a jihohin Kudu
A safiyar Laraba, hadari da ruwan sama mai ɗan ƙarfi zai sauka a Imo, Abia, Anambra, Enugu, Bayelsa, Cross River, da Akwa Ibom.
A yammacin ranar kuwa, ruwan sama mai zai sauka a Ondo, Ekiti, Ebonyi, Osun, Imo, Anambra, Abia, Cross River, Rivers, Akwa Ibom, Delta, da Bayelsa.
NiMet ta ce ana iya samun ruwa mai tsanani a wasu wurare, don haka mutane su dauki matakan kare lafiyarsu da dukiyoyinsu.

Source: Twitter
Shawarwarin hukumar NiMet ga jama'a
Hukumar ta shawarci al’umma da su kasance cikin shiri, musamman wadanda ke zaune a garuruwan da ke gabar teku, ko inda suka saba fuskantar ambaliya.
An shawarci gwamnati ta shirya kai dauki a wuraren da ka iya fuskantar ambaliyar, yayin da aka shawarci kamfanonin sufurin jiragen sama su nemi bayanan yanayi daga NiMet.
Ana fargabar ambaliya a jihohi 29
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta yi hasashen cewa za a samu ambaliyar ruwa a babban birnin tarayya Abuja da kuma wasu jihohi 29.
Rahoton da hukumar NiHSA ta fitar ya nuna cewa jihohin 29, ciki har da Gombe, Kaduna, Kogi, da Neja, za su fuskanci ambaliyar tsakanin 1 zuwa 15 ga Satumba, 2025.
Hukumar ta ce kananan hukumomi 107 da garuruwa 631 ne suke cikin barazanar ambaliya a tsakanin wannan lokacin da aka ambata, don haka ta gargadi mutane.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

