Har da Abuja, Mummunar Ambaliya Za Ta Shafi Gombe, Neja da Jihohi 27 a Satumba

Har da Abuja, Mummunar Ambaliya Za Ta Shafi Gombe, Neja da Jihohi 27 a Satumba

  • Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa jihohi 29 da Abuja za su fuskanci ambaliya daga ranar 1 zuwa 15 ga Satumba, 2025
  • NiHSA ta rahoto cewa cewa kananan hukumomi 107 da garuruwa 631 ke fuskantar barazanar ambaliya a wannan lokaci
  • Hukumar ta lissafa jihohin da wannan ambaliya za ta shafa da suka hada da Adamawa, Anambra, Bauchi da dai sauransu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kula da harkokin ruwa ta kasa, NiHSA, ta fitar da gargadi kan ambaliya da zata shafi babban birnin tarayya Abuja da wasu jihohi 29.

Rahoton gargadin ya nuna cewa ambaliyar za ta afku daga ranar 1 zuwa 15 ga watan Satumba, 2025, inda ta lissa yankuna mafi hadarin ambaliyar.

Gwamnati ta ce ambaliyar ruwa za ta shafi jihohi 29 daga ranar 1 zuwa 15 ga Satumba, 2025
Jami'an ba da agajin gaggawa na kokarin ceto wasu da ambaliya ta rutsa da su. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

Jihohin da za a iya samun ambaliya

A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, hukumar ta ce kananan hukumomi 107 da garuruwa 631 ne suke cikin barazanar ambaliya a wannan tsakanin lokacin da aka ambata.

Kara karanta wannan

An yi rashi: Mace ta farko da Tinubu ya nada shugabar ma'aikatan Abuja ta rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta lissafa jihohin da ke cikin hadarin ambaliya, da suka hada da Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, da Benue.

Sauran sun hada da Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger da Ogun.

Hakanan an ce ambaliyar za ta shafi jihohin Ondo, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da kuma FCT Abuja.

Barnar da ambaliya za ta yi a jihohi 29

NiHSA ta bayyana cewa akwai yiwuwar samun ambaliya mai karfi wanda zai iya kawo cikas ga muhimman hanyoyi da gadoji a fadin kasar nan.

An ce ambaliyar za ta iya haifar da lalacewar gonaki, lalata kayayyakin more rayuwa da kuma haifar da matsalolin kiwon lafiya ga jama’a.

Rahoton ya kuma nuna yiwuwar gurɓatar ruwan sha wanda zai iya kawo barazana ga lafiyar al’umma a yankunan da suka fi fuskantar hadarin.

Shugaban hukumar NiHSA, Arc. Umar Mohammed, ya ce:

Kara karanta wannan

Lahadi: Ruwan sama da iska mai ƙarfi zai sauka a Abuja, Neja, Yobe da wasu jihohi

"Wannan gargadin ya yi daidai da hasashen ambaliyar shekarar 2025 (AFO) da aka fitar, kuma ya dogara ne da bayanan saukar ruwa, cikar rafuka, da alkaluman ambaliya da aka tattara."
Hukumar NiHSA ta bukaci NEMA da hukumomin SEMA na jihohi su dauki matakan kare al'umma kafin afkuwar ambaliya
Jami'an hukumar NiHSA suna tatara bayanai kan ambaliya da kyawun ruwa a jihar Kebbi. Hoto: @nihsa_ng
Source: Twitter

Shawarwari ga gwamnati da al’umma

NiHSA ta shawarci hukumar NEMA da SEMA a jihohi, su tashi tsaye wajen daukar matakan gaggawa kafin faruwar ambaliyar, inji rahoton Vanguard.

Ta bukaci shugabannin kananan hukumomi da garuruwa su gano hanyoyin tseratar da jama'arsu, su kuma shirya tarukan gaggawa don wayar da kan al'umma.

Hukumar ta gargadi mazauna yankunan da ke cikin hadarin ambaliya su guji kwana a wuraren da ruwa zai iya mamaye wa, tare da bin umarnin hukumomin tsaro da na lafiya.

Karanta sanarwar a nan kasa

Ambaliya za ta shafi jihohin Arewa 9

A wani labarin da muka fitar a makon jiya, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa jihohi tara da yankuna 14 a Arewa za su fuskanci ambaliya.

Ma'aikatar muhalli ta tarayya ce ta fitar da rahoton, inda ta ce jihohin za su fuskanci ambaliyar ne a tsakanin 25 zuwa 29 ga Agustan 2025.

Jihohin da ma'aikatar ta ce ambaliyar za ta shafa a lokacin sun hada da Adamawa, Borno, Gombe, Kano, Katsina, Sokoto da kuma Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com