Allah Bai Karbi Addu'ar Sanku ba, Mai Wasan Barkwanci Ya Mutu a Haɗarin Mota
- Fitaccen ɗan wasan barkwanci, Sanku, ya rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyar Oyo–Ogbomoso
- Kafin rasuwarsa, ya wallafa bidiyo a shafukansa na sada zumunta, yana addu’a kada ya mutu kafin ya ci gajiyar sana'ar barkwancinsa
- A tare da Sanku, akwai wasu abokansa da haɗarin ya rutsa da su, inda aka ji halin da suke ciki bayan da aka sanar da rasuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Oyo - Fitaccen ɗan wasan barkwanci na Najeriya, Sanku, ya rasu a wani haɗarin mota mai muni da ya faru a kan hanyar Oyo–Ogbomoso a garin Ibadan, a ranar Litinin.
Lamarin ya bazu cikin sauri a kafafen sada zumunta, inda aka ga hotuna da bidiyon motar ɗan wasan barkwancin da ta afka cikin rami yayin haɗarin.

Source: Instagram
Sanku: 'Dan wasan barkwanci ya mutu
Jaridar Punch ta rahoto cewa, Sanku na cikin motar tare da wani abokinsa lokacin da motar ta afka cikin wani rami a kan hanyar Oyo–Ogbomoso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce an garzaya da ɗan wasan ban dariyar da abokin nasa zuwa asibiti, inda aka yi kokarin ceto rayukansu.
Sai dai kuma, likitoci sun tabbatar da mutuwar Sanku, lamarin da ya girgiza masana’antar nishadi da masoyansa na ciki da wajen Najeriya.
Har yanzu ba a tabbatar da halin da abokinsa yake ciki ba, amma wasu rahotanni a shafukan sada zumunta sun ce yana cikin mawuyacin hali.
Martanin abokan sana’ar Sanku
Mai wasan barkwanci, Ozain Comedy ya tabbatar da labarin, inda ya rubuta cewa, "Ubangiji ya ba ka salama, sai wata rana."
Haka zalika, jarumar Nollywood, Funmi Awelewa, ta bayyana cewa ta tura ɗaya daga cikin dalibanta zuwa asibitin Bowen domin tabbatar da labarin.

Kara karanta wannan
'Gado na yi': Malamin addini da ake zargi da aukawa ƴarsa tsawon shekaru 4 ya magantu
Channels TV ta rahoto Jaruma Funmi Awelewa ta ce:
"Lokacin da na ka labarin a yanar gizo, na gaggauta tura daya daga cikin dalibanta da ke zaune a kusa da asibitin Bowen, ya je ta dubo mun gaskiyar lamarin.
"Dalibin nawa ya hadu da wani abokin Sanku a asibitin, inda ya shaida masa cewa yanzu haka yana samun kulawar likitoci. A lokacin na yi addu'ar Ubangiji ya tashi kafadunka."
Sai dai, jarumar ta ce duk da irin addu'o'in da ta yi, Sanku ya zo ya mutu, bai iya tsallake kaddararsa ba.

Source: TikTok
Bidiyon karshe kafin mutuwar Sanku
Kafin rasuwarsa, bidiyon ƙarshe da Sanku ya wallafa a shafinsa na TikTok mai mabiya fiye da miliyan 1.9 ya kara bazuwa a kafafen sada zumunta.
A cikin bidiyon, Sanku ya yi addu’ar kada Ubangiji ya karbi rayuwarsa, har sai ya ci gajiyar wahalar da ya sha ta kafa kansa a masana'antar nishadi.
Sanku, wanda ya fara harkar barkwanci a 2021, ya yi fice sosai a 2024, inda ya tara mabiya masu yawa, kuma ya samu farin jini da yabo saboda irin salon barkwancinsa.
Kalli hotunan hadarin motar da Leadership ta wallafa a X, a kasa:
'Yar wasar barkwanci ta mutu a wajen taro
A wani labarin, mun ruwaito cewa, fitacciyar yar wasan barkwanci, Mrs. Nwandinma Dickson, wadda aka fi sani da “Nwayi Garri,” ta mutu.
Rahotanni sun nuna cewa yar wasan ta yanke jiki ta fadi ne tana tsakiyar nishadantar da mutane a wurin wani taro a Ugwunagbo, jihar Abia.
An ce matar gwamnan Abia ce ce ta dauki nauyin shirya wannan taron, sai dai ya taron ya rikide zuwa alhinin bayan mutuwar 'yar wasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

