'Yan Sanda Sun Kama Bindigogi, Masu Garkuwa, Barayi da Sauran Miyagu a Kano
- Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta samu gagarumin nasara wajen dakile laifuffuka ta hanyar aikin Operation Kukan Kura
- An kama mutane 107 da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban, ciki har da ‘yan fashi, masu safarar miyagun kwayoyi da ‘yan daba
- Rundunar 'yan sandan ta kwato bindigogi, miyagun kwayoyi, motocin sata, babura da kayayyaki masu yawa a Agustan 2025
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana sakamakon nasarorin da ta samu ta hanyar sabon tsarinta na yaki da aikata laifuka da ta lakaba wa suna Operation Kukan Kura.
Wannan ya fito ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedkwatar ‘yan-sanda da ke Bompai, Kano.

Source: Facebook
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya wallafa a Facebook cewa tsarin ya taka rawar gani wajen rage aikata laifuffuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa nasarorin da aka samu sun samo asali ne daga hadin kai tsakanin jama’a da rundunar.
An kama masu garkuwa da mutane a Kano
Shirin da aka kaddamar a ranar 1 ga Yuli 2025, ya mayar da hankali ne wajen dakile fashi da makami, garkuwa da mutane, fataucin miyagun kwayoyi, da sauran manyan laifuffuka.
A cikin watan Agusta kadai, rundunar ta kama mutane 107 da ake zargi da aikata laifuffuka. Cikinsu har da:
- Yan fashi da makami – 8
- Masu garkuwa da mutane – 8
- Masu fataucin mutane – 3
- Masu safarar miyagun kwayoyi – 14
- Barayin motoci – 2
- Barayin babura – 6
- Sauran barayi – 5
- 'Yan daba – 61
Baya ga haka, rundunar ta kuma tabbatar da kubutar da mutum guda daga hannun masu fataucin mutane.
An kwato bindigogi a jihar Kano
Daga cikin kayayyakin da aka samu akwai bindiga kirar AK-47 guda 1, bindigogi kirar gida 7, harsashi 11.
Bayan haka, an kwato motoci 8, babura 8, shanu 8, adduna 102, wukake 74 da miyagun kwayoyi iri-iri ciki har da tabar wiwi, sholisho da sauran su.
Haka kuma an kwato wayar hannu 59, na’urorin POS guda 3, da katunan cire kudi na Opay guda 17.

Source: Facebook
Bukatar hadin kan jama'an Kano
An yaba wa al’ummar Kano bisa irin hadin kan da suka bayar, musamman wajen mika bayanai da suka taimaka wa rundunar wajen kama masu aikata laifi.
Sanarwar 'yan sanda ta ce bayan kaddamar da wannan tsari an kwato muggan makamai 473 da miyagun kwayoyi masu tarin yawa.
Rundunar ta kuma bukaci jama’a da su ci gaba da kai rahoto kan duk wani abin zargi ga ofishin ‘yan-sanda mafi kusa ko ta lambobin da aka bayar.
An kama mai safarar makamai a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta kama wasu mutane biyu da tarin makamai.
An kama mutanen ne dauke da wata babbar bindiga da tarin harsashi da aka fito da su daga Jigawa zuwa Katsina.
Rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana cewa za ta zurfafa bincike domin gano wuraren da aka nufi kai makaman.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

