Shettima @59: Ba Kamar yadda Ake Zato da, Tinubu Ya Faɗi Dalilin Zaben Kashim

Shettima @59: Ba Kamar yadda Ake Zato da, Tinubu Ya Faɗi Dalilin Zaben Kashim

  • A yau Talata 2 ga watan Satumbar 2025, Kashim Shettima ya ke bikin murnar ranar zagayowar haihuwarsa
  • Shugaba Bola Tinubu ya taya mataimakinsa, Kashim Shettima murnar cikar sa shekaru 59, yana yabawa da jajircewarsa
  • Tinubu ya tuna irin jagorancin Shettima a Borno da majalisar dattawa, ya ce shugabanci hidima ne da kalubale

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tura sako na musamman da yabo ga mataimakinsa, Kashim Shettima.

A yau Talata, 2 ga Satumba 2025, Kashim Shettima yake murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Tinubu ya taya Shettima murnar cika shekaru 59
Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Kashim Shettima.
Source: Twitter

Bola Tinubu ya yabawa jajircewar Kashim Shettima

Hakan na cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X a yau Talata 2 ga watan Satumbar 2025.

Shugaba Bola Tinubu ya ce wannan rana ta sake ba shi damar taya mataimakinsa, Kashim Shettima murnar cika shekaru 59.

Kara karanta wannan

"Mayunwata ne": Hadimin Tinubu ya caccaki El Rufai da masu son kifar da shugaban kasa

Ya ce tun da suka fara tafiya tare da burin gina kasa don cigaba, ya ce Shettima ya nuna jarumta, jajircewa da gaskiya ga Najeriya.

Shugaban ya ce Shettima ya yi wa al’ummar Borno jagoranci tsawon shekaru takwas a matsayin gwamna sannan ya wakilci Borno ta tsakiya a majalisar dattawa.

Shugaba Tinubu ya kwarara yabo ga Kashim Shettima

Tinubu ya ce a cikin wadannan mukamai, Kashim Shettima ya tabbatar da shugabanci hidima ne ga jama’a ba gata ba, duk da kalubale sun yi yawa.

Shugaban ya kara cewa hidimar Shettima ga Najeriya ta fito fili saboda kishinsa na dimokuradiyya, shugabanci nagari da habaka tattalin arziki a kasa.

Ya bayyana godiya ga jajircewa da amincin Shettima a matsayin mataimaki, yana mai cewa zabinsa ya kasance ta fannin kwarewa da cancanta.

A cewar Tinubu, kowace rana Shettima na tabbatar da zabin nasa ta hanyar kawo sababbin ra’ayoyi, da karfafa ayyuka ga al’ummar Najeriya gaba daya.

Ya kara cewa suna aiwatar da manufar “Renewed Hope”, daga kafa sababbin kawance a kasashen waje zuwa karfafa tsaron abinci da jari-hujja a gida.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa bai kamata Jonathan ya fafata da Tinubu ba a 2027'

Tinubu ya kwarara yabo ga Kashim Shettima
Tinubu da Kashim Shettima yayin taro a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Karin alkawuran Tinubu ga 'yan Najeriya

Tinubu ya ce a watanni masu zuwa, gwamnati za ta kara samar da makarantu, asibitoci, ayyuka da sababbin hanyoyin kasuwanci bisa hadin gwiwar Shettima.

Shugaban kasar ya bayyana Shettima a matsayin abin koyi ga masu neman shugabanci, saboda sanya Najeriya a gaba da kyautata rayuwar jama’a.

A karshe, Tinubu ya yi masa fatan karin hikima, lafiya da shekaru masu amfani yayin da ya cika shekaru 59 a duniya.

Tinubu ya sha alwashin yin adalci ga kowa

A baya, mun ba ku labarin cewa Bola Tinubu ya ce rantsuwar da ya yi a matsayin shugaban kasa ta shafi kowa a Najeriya, ba wani yanki kadai ba.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa dukkan ayyukan da gwamnati ke aiwatarwa a sassa daban-daban na Najeriya na nufin ci gaban kasa baki daya.

Mai girma Shugaban na Najeriya ya ce babu wani dan kasa da ya fi wani daraja, kuma babu wani yanki da za a bari a baya a tafiyar mulkinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.