Rashin Tsaro: El Rufa'i Ya Yi wa Ribadu da Uba Sani Wankin Babban Bargo

Rashin Tsaro: El Rufa'i Ya Yi wa Ribadu da Uba Sani Wankin Babban Bargo

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi martani ga ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro da gwamnatin jihar Kaduna
  • Ya ce ONSA da gwamnatin Kaduna sun kasa magance matsalar tsaro, yana mai cewa suna ɓoye gaskiya ga ’yan ƙasa
  • Malam Nasir El-Rufai ya jaddada cewa dole ne a kawar da matsalar rashin tsaro a Najeriya, ba a fara rufe bakin masu sukar gwamnati ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake zafafa suka kan mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da gwamnatin Kaduna.

Hakan ya biyo bayan wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin, inda ya bayyana cewa ana biyan kuɗin fansa ga ’yan bindiga a wasu jihohin Arewa.

Kara karanta wannan

'Kalamanka na da haɗari,' CAN ta taso El Rufai a gaba kan yawan Kiristocin Kaduna

Nasir El-Rufa'i da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro
El-Rufa'i da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro. Hoto: Nasir El-Rufa'i|Nuhu Ribadu
Source: Facebook

Legit ta gano cewa Malam Nasir El-Rufa'i ya yi martanin ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

Martanin Nasir El-Rufa'i ga Nuhu Ribadu

El-Rufai ya ce maimakon ofishin NSA da gwamnatin Kaduna su mayar da hankali wajen magance matsalar tsaro, sun fi mayar da martani ta hanyar neman boye abin da ya faɗa.

Ya ƙara da cewa shi mutum ne da ke daraja sojoji da jami’an tsaro, saboda ’yan uwansa uku sun yi aiki a rundunonin tsaro na ƙasar, ɗaya ma ya kai matsayin Janar.

Daily Trust ta rahoto ya ce:

“A bayyane yake ga ’yan Najeriya masu hangen nesa cewa siyasantar da harkar tsaro a ƙasar nan ta fara ne da ofishin NSA a ƙarƙashin wannan gwamnati.

Maganar zargin biyan kuɗin fansa

Tsohon gwamnan ya jaddada cewa ba shi ne mutum na farko da ya bayyana batun gwamnati na biyan kuɗin fansa ga ’yan bindiga a jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina, Sokoto, Kebbi da Niger ba.

Kara karanta wannan

"Mayunwata ne": Hadimin Tinubu ya caccaki El Rufai da masu son kifar da shugaban kasa

A cewarsa, akwai bidiyo da saƙonnin murya daga sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da malamai da ke sukar wannan al’ada.

Gwamnan Kaduna, Uba Sani a wajen wani taro
Gwamnan Kaduna, Uba Sani a wajen wani taro. Hoto: Kaduna State Government
Source: Facebook

A cewarsa, ba don siyasa ya yi kalamansa ba, sai don bayyana damuwar al’ummar da ke fama da hare-haren ta’addanci da garkuwa da mutane.

“A kawar da rashin tsaro,' El-Rufa'i

El-Rufai ya ce abin da ya fi damunsa shi ne yadda gwamnati ke ƙoƙarin kakabawa masu adawa yin shiru, maimakon ta magance matsalar rashin tsaro.

Ya bayyana cewa harin da aka kai wajen taron ADC a Kaduna ranar 30 ga watan Agusta, 2025, ya nuna yadda wasu jami’an gwamnati da na tsaro ke shiga cikin ayyukan danniya.

Ya tambayi dalilin da ya sa ofishin NSA ba ya ganin wannan a matsayin babban barazana ga tsaron ƙasa.

El-Rufa'i: Dalilin kawo Muslim Muslim

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya bayyana dalilin da suka kawo gwamnatin Muslim Muslim a 2023.

El-Rufa'i ya yi magana ne yayin da ya ke amsa tambayoyi game da rawar da ya taka wajen kawo gwamnatin Bola Tinubu.

Ya bayyana wa manema labarai cewa sun kawo gwamnatin Muslim Muslim ne domin cin zabe ba domin addini ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng