Gwamnatin Kaduna Ta Gagara Hakura, Ta Aika da Kashedi Mai Zafi ga El Rufai

Gwamnatin Kaduna Ta Gagara Hakura, Ta Aika da Kashedi Mai Zafi ga El Rufai

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta tanka bayan da Nasir El-Rufai ya zarge ta da daukar nauyin 'yan daba don tarwatsa taron jam'iyyar ADC
  • Kwamishinan harkokin cikin gida a gwamnatin Uba Sani ya zargi tsohon gwamnan da yunkurin kawo hargitsi a jihar Kaduna
  • Dr. Sulaiman Shuaibu ya bayyana cewa El-Rufai yana zarge-zargen ne kawai bayan da mutanensa suka sha kashi a zaben cike gurbi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Gwamnatin Kaduna ta yi martani ga tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, kan zarge-zargen da ya yi na baya-bayan nan.

Gwamnatin Kaduna ta zargi El-Rufai da shirin tayar da tarzoma da kawo rikice-rikice a jihar ta hanyar tsokana, yaudara da tunzura mutane.

Gwamnatin Kaduna ta ragargaji El-Rufai
Hoton gwamnan Kaduna, Uba Sani da Nasir El-Rufai Hoto: @ubasanius, @elrufai
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Dr. Suleiman Shuaibu, ya fitar a ranar Litinin, 1 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

'Kalamanka na da haɗari,' CAN ta taso El Rufai a gaba kan yawan Kiristocin Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Kaduna ta yi wa El-Rufai martani

Kwamishinan ya ce abubuwan da El-Rufai ya yi a baya-bayan nan barazana ne kai tsaye ga zaman lafiya da ci gaban jihar, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

A cewarsa, tsohon gwamnan ya kara kaimi wajen irin waɗannan kalaman ne bayan abokan siyasarsa sun sha kaye a zaɓen cike gurbi na ranar 16 ga watan Agustan 2025.

"Yan takararsa da aka ki zaba sun sha mummunan kaye a zaɓe mai ’yanci, nagari kuma na gaskiya wanda ya tabbatar da amincewar jama’a ga jagorancin jam’iyyar APC da kuma mulkin ci gaba na Sanata Uba Sani."
"Maimakon karɓar wannan sakamakon na dimokuraɗiyya cikin mutunci, El-Rufai ya zaɓi yin aiki da yaudara da cin amanar kasa."

- Dr. Sulaiman Shuaibu

An taso El-Rufai a gaba kan sukar gwamnati

Gwamnatin ta kuma zargi El-Rufai da cewa a ranar 30 ga Agusta, ya shirya wani taron siyasa wanda ya rikide zuwa tashin hankali, har da harbe-harbe da suka jefa rayukan jama’a cikin haɗari.

Kara karanta wannan

Zargin badaƙalar N6.8bn: Ganduje ya nemi a fara shirin tsige Gwamna Abba a Kano

"El-Rufai ya yi kokarin dora alhaki kan gwamnati ta hanyar yin karya cewa ita ce ta ɗauki ’yan daba domin tarwatsa taron."
"Amma tambaya ita ce, meya sa gwamnan da ya riga ya samu amincewar jama’a ta hanyar sahihin zaɓe zai bukaci tarwatsa taron waɗanda suka sha kaye?"

- Dr. Sulaiman Shuaibu

Gwamnatin Kaduna ta yi wa El-Rufai raddi
Hoton tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Sanarwar ta ce wannan labari ba wai raina hankalin al’ummar Kaduna ba ne kawai, har ma da nuna manufar El-Rufai ta mayar da jihar zuwa rikicin da ya rika aukuwa a lokacin mulkinsa.

Gwamnatin Kaduna ta ja kunnen El-Rufai

Kwamishinan ya gargadi El-Rufai kan ya daina abubuwan da za su iya kawo rikici, inda ya jaddada cewa tuni aka ankarar da jami'an tsaro.

"Gwamnatin jihar Kaduna ba za ta amince da hakan ba. Wannan gwamnatin za ta yi duk abin da ya dace bisa doka don kare zaman lafiyan da mutanenmu suka sha wahala wajen sake samarwa."
"Ba wani mutum komai girmansa ko girman mukamin da ya taba rikewa a baya, da za a bari ya kawo hargitsi a jihar nan. Zaman lafiyar jihar Kaduna ba abin wasa ba ne."

Kara karanta wannan

El Rufai ya nuna yatsa ga Uba Sani bayan 'yan daba sun tarwatsa taron ADC a Kaduna

- Dr. Sulaiman Shuaibu

El-Rufai ya yi zargi kan gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da daurewa 'yan bindiga gindi.

El-Rufai ya yi zargin cewa gwamnatin tana biyan 'yan bindiga kudade wanda hakan yake kara karfafa su.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa wadannan kudaden da ake ba su ne ya sanya suke sayan mugayen makamai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng