Kura Kuren da ke Fitowa daga Aso Rock Sun Sa an Taso Tinubu da Hadimansa a gaba
Salihu tanko Yakasai, tsohon hadimin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, taso gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a gaba.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa jerin ayyukan da fadar shugaban kasa ta fitar na dauke da bayanai da ba gaskiya ba ne, kuma wasu daga cikin kwangilolin duk na bogi ne.

Source: Twitter
A sakon da ya wallafa a shafinsa X, Salihu Tanko Yakasai ya zargi gwamnatin Tinubu da ƙirƙirar bayanai da shirin yaudarar jama’a” game da wasu muhimman manyan tituna a Arewa.
A kalamansa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ya kamata a ce kun daina wannan bayanin bayan kun goge sakonku na farko, amma kun dawo da shi tare da sababbin ƙarairayi. Don haka bari mu sake warware wannan magana."
Salihu Tanko Yakasai da aka fi sani da Dawisu ya jero wasu daga cikin kura kuran da ya ke zargin an maka a cikin sanarwar da Fadar Shugaban Kasa ta fitar.
Sun hada da:
1. Hadimin Ganduje ya magantu kan titin Abuja–Kaduna–Kano
Dawisu ya bayyana cewa tsawon titin da ya taso daga Zuba zuwa Kano ya kai kilomita 420, kuma gwamnatin Muhammadu Buhari ta kusa kammala sashen Kano zuwa Kaduna mai kilomita 240.
Ya kara da bayyana cewa wannan na nufin cewa abin da ya yi saura a aikin shi ne Kaduna zuwa Abuja mai kilomita 180.

Source: Facebook
Ya ce:
“To daga ina kuka samo 350km? Kuma kuɗin kammala aikin da aka ba Infoquest shi ne Naira biliyan 250, to daga ina kuka samo N764bn?”
2. Akwai kuskure a aikin Kano zuwa Daura
Dawisu ya bayyana cewa aikin karkashin tsarin harajin BUA ne, amma tun bayan da Tinubu ya hau mulki a 2023 an daina aiki a kan hanyar.
Ya ce:
“Na bi wannan hanya a makon jiya zuwa Daura don bikin Ranar Hausa, babu aikin komai a kan hanya,” in ji shi.
3. Dawisu ya soki batun aikin Zaria zuwa Hunkuyi
Salihu Tanko Yakasai ya soki yadda ya ce gwamnati ta yi kuskure a wajen bayyana tsayin hanyar da ta ce ana aiki a kai.
Ya ce:
"Kilomita 156, gwamnati ta duba Google Maps don ganin ainihin tsawon hanyar."
4. Menene aikin Kaduna zuwa Katsina?
Salihu Tanko ya bayyana cewa da alama gwamnatin ta yi kuskuren maimaita wannan aiki da wani suna daban.
Ya ce:
Wannan aikin da aka wallafa ba shi da bambanci da aikin Zaria zuwa Hunkuyi."
Jama'a da-dama sun yi wa gwamnati raddi da ta ce tsawon titin ya kai kilomita 156.
5. Salihu: 'Babu aikin Bypass a Kano'
Hadimin tsohon Shugaban APC ya ce babu wani aiki a wannan wuri kamar yadda gwamnatin Bola Tinubu ta yi ikirari.

Source: Twitter
Ya ce:
"Ku daina wallafa wannan aikin a jerin ayyuka, babu shi a kasa. Ku nuna mana hujja idan akwai shi "
6. 'Dan siyasar ya ƙalubalanci aikin titin Sokoto-Badagry

Kara karanta wannan
Kano: Abdullahi Rogo ya maka Jafar Jafar a kotu saboda labarin 'satar Naira Biliyan 6'
'Dan takarar gwamnan na Kano a 2023 ya kalubalanci gwamnati ta nuna hoto ko bidiyo na aikin hanyar Sokoto zuwa Badagry kamar yadda ake nuna na Lagos zuwa Calabar.
"Yyar magana, babu komai saboda kun ki saka masa kuɗi, aikin ya zama labari kurum."
Salihu Tanko Yakasai ya ce duk abubuwan da ya zayyana, wadanda su ka shafi Arewa maso Yamma ne kawai.
Ya ce ya bar sauran ‘yan Najeriya su yi tsokaci kan ayyukan da aka lissafa a yankunansu.
An zargi gwamnati da watsi da tituna
A baya, kun ji cewa direbobi da sauran matafiya sun bayyana damuwa da takaici a kan halin da titin Kano–Gwarzo–Dayi, ke ciki, saboda lalacewa.
An bayar da aikin fadada hanyar zuwa babbar hanya mai nisan kilomita 82.3 amma, kamar yadda aka yi korafi, ‘yan kwangilar sun kwashe duk kayan aikinsu.
An fara aikin domin sauƙaƙa zirga-zirga da jigilar kayayyaki, musamman don haɗa Kano da jihohin Katsina, Sakkwato, Zamfara, da Kebbi har zuwa Jamhuriyar Nijar
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

