An Kama Tarin Makamai Ana Kokarin Shiga da Su Katsina daga Jigawa
- ‘Yan sanda sun cafke mutane biyu da ake zargi da safarar manyan makamai daga Jigawa zuwa Katsina
- Rahotanni sun bayyana cewa an kwato bindigogi da harsasai 1,295 daga cikin mota kirar Golf mai launin shudi
- Gwamnatin jihar Katsina ta jaddada goyon baya ga hukumomin tsaro wajen dakile miyagun laifuffuka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina – Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta samu nasarar cafke wani gagarumin shirin safarar makamai da ka iya haifar da barna a fadin jihar.
Wannan mataki na zuwa ne da sanyin safiyar Litinin a yayin da jami’an tsaro ke sintiri a hanyar Ingawa zuwa Karkarku.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan Katsina, Ibrahim Kalaha Muhammad ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kama masu safarar makaman
Ibrahim Kaulaha ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar tare wata mota kirar Volkswagen Golf mai launin shudi da aka boye makaman cikin ta.
Binciken farko ya nuna cewa an dauko makaman daga Hadejia a jihar Jigawa zuwa karamar hukumar Safana ta Katsina.
Makaman da aka kwato a Kastina
Jami’an tsaro sun gano manyan makamai da suka hada da bindiga mai karfin gaske wato GPMG mai lamba Z8826, harsasai 1,063 na bindigar AK-47, da kuma harsasai 232 na bindigar PKT.
Makaman sun kasance a cikin motar da lambar rijista RSH 528 BY ABJ, wacce ake amfani da ita wajen safarar kayan daga Jigawa zuwa Safana.
An kama mutane 2 da safarar makamai
An kama Abdulsalam Muhammad mai shekaru 25 da Aminu Mamman mai shekaru 23, dukkansu mazauna garin Baure a karamar hukumar Safana.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun tabbatar da cewa su ne ke jigilar makaman zuwa inda aka nufa.
Bincike ya nuna cewa akwai wasu da ke da hannu a cikin gungun masu safarar makamai, lamarin da ya sa rundunar ‘yan sanda ta fara zurfafa bincike domin gano su.
Matsayar gwamnatin jihar Katsina
Kwamishinan tsaro na Katsina, Dr. Nasir Mu’azu, ya ce nasarar alama ce ta kudirin gwamnati na ganin an katse duk wata hanyar da ‘yan ta’adda ke bi don kawo cikas ga zaman lafiya.
Ya jaddada cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da bai wa hukumomin tsaro dukkan goyon baya da tallafin da suke bukata domin tabbatar da tsaro.

Source: Facebook
A halin yanzu bincike ya soma gudana domin gano inda ake shirin kai makaman da kuma wadanda ke da hannu a shirin.
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da fadada bincike tare da hada kai da sauran hukumomin tsaro domin ganin an kawo karshen harkar safarar makamai a jihar.
'Yan bindiga: Ribadu ya karyata El-Rufa'i
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta karyata cewa tana ba 'yan bindiga kudin fansa a kasar nan.
Ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ne ya yi magana, kuma ya ce zargin da aka musu ba gaskiya ba ne.
ONSA ya yi magana ne bayan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da ba 'yan ta'adda kudi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

