Garambawul a Jihohi: Gwamnonin Najeriya 6 Sun Rushe Majalisun Zartarwa a 2025

Garambawul a Jihohi: Gwamnonin Najeriya 6 Sun Rushe Majalisun Zartarwa a 2025

  • Daga Janairu zuwa 1 ga Satumbar 2025, akalla gwamnoni shida a Najeriya ne suka rusa majalisun zartarwa na jihohinsu
  • Gwamnonin sun yi wannan babban garambawul din a wani mataki na inganta mulki, aiki tare da kwararru da ci gaban jama'arsu
  • A wannan rahoton, Legit Hausa ta kawo bayanai game da jihohin shida, ciki har da Neja, da aka samu sauyin majalisar zartarwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A shekarar 2025, Najeriya ta shaida sauye-sauye masu girma, yayin da gwamnoni akalla shida suka rusa majalisun zartarwa na jihohinsu.

Gwamnonin sun rusa majalisun a matsayin wasu dabaru na inganta shugabanci, ko daidaita mulki da manufofin siyasarsu, a yunkurin kawo ci gaba ga jiharsu.

Gwamnoni 6 sun rushe majalisar zartarwar jihohinsu daga Janairu zuwa Satumbar 2025.
Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, da gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, da gwamnan Neja, Umar Bago. Hoto: @_PastorUmoEno, @HonBago, @NasarawaGovt
Source: Twitter

Gwamnoni 6 da suka rusa majalisar zartarwa

Legit Hausa ta tattaro bayanai kan yadda kowanne gwamna ya rusa majalisar zartarwa tasa, da matakan da aka ɗauka daga baya, bisa bayanan da aka samu har zuwa 1 ga Satumba, 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna Bago ya kori dukkan kwamishinoni da ya rusa majalisar zartarwar Neja

1. Nasarawa – Gwamna Abdullahi Sule

A ranar 3 ga Janairu, 2025, Gwamna Abdullahi Sule ya rusa majalisar zartarwa, inda ya umurci kwamishinoni su mika mulki ga manyan sakatarorin ma'aikatunsu.

Gwamna Sule ya bayyana cewa matakin yana daga cikin dabarun sabunta gwamnati da kuma shigar da sababbin dabaru domin ci gaban al’ummar jihar Nasarawa, inji rahoton This Day.

2. Ondo – Gwamna Lucky Aiyedatiwa

A ranar 15 ga Janairu, 2025, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya rusa majalisar zartarwa, yayin da ya yi shekara daya a kan mulki, bayan rasuwar tsohon gwamna Rotimi Akeredolu.

Mun ruwaito Aitedatiwa ya ce ya dauki matakin ne don ya nada mutanen da suka yi imani da hangen nesansa, tare da tabbatar da hadin kai da ci gaba a gwamnatin jihar.

3. Akwa Ibom – Gwamna Umo Eno

Gwamna Umo Eno ya rusa majalisar zartarwar Akwa Ibom a ranar 10 ga Janairu, 2025, inda ya umurci 'yan majalisar su gaggauta fice wa daga ofis.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Gwamnonin Arewa sun hango masifa a 2026, sun roki Tinubu

Ya bayyana cewa hakan zai ba shi damar tantance ayyukan kwamishinoni tare da tabbatar da sabuwar gwamnati mai inganci, gaskiya da kuma daukar alhakin aikinsu.

4. Benue – Gwamna Hyacinth Alia

A ranar 30 ga Yuli, 2025, Punch ta rahoto cewa Gwamna Hyacinth Alia ya rusa majalisar zartarwa, matakin da ya zo wa kwamishinoni a baga-tatan.

Gwamna Alia ya ce yana so ya sake fasalin gwamnati tare da tabbatar da cewa masu jajircewa ne kadai za su ci gaba da aiki, kamar yadda muka ruwaito.

Gwamna Hyacinth Alia ya rusa majalisar zartarwar jihar Benue
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, a dakin taron kungiyar gwamnonin Najeriya, a Abuja. Hoto: @HyacinthAlia
Source: Twitter

5. Ekiti – Gwamna Biodun Oyebanji

A ranar 21 ga Agusta, 2025, Gwamna Biodun Oyebanji ya rusa majalisar zartarwa, ya umurci kwamishinoni su mika duk kayan gwamnati da ke hannunsu.

Gwamna Oyebanji ya ce wannan ba horo ba ne, dabara ce ta sake fasalin gwamnati, inda ya tabbatar da kafa majalisar da za yi aiki tukuru ga ci gaban jihar, cewar rahoton shafin gwamnati.

6. Neja – Gwamna Mohammed Umaru Bago

A ranar 1 ga Satumba, 2025, muka ruwaito cewa, Gwamna Mohammed Umaru Bago ya rusa majalisar zartarwa yayin taron majalisar a birnin Minna.

Kara karanta wannan

Tajudeen Abbas na fuskantar matsala, rigima na neman barkewa a Majalisa kan abubuwa 2

Sai dai, a nan take ya sake nada manyan mukarrabai kamar Sakataren Gwamnati da Shugaban Ma’aikata, yana mai cewa matakin zai kawo karfin gwamnati da inganci.

Uba Sani ya yi garambawul a gwamnatinsa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an samu sauyin mukaman kwamishinan shari’a da na tsaro da harkokin cikin gida domin inganta ayyukan a Kaduna.

Gwamna Uba Sani ya dage Sule Shuaibu daga ma’aikatar shari'a zuwa ma'aikatar tsaron cikin gida, inda yanzu James Kanyip ya zama sabon babban lauyan jiha.

Gwmanan jihar ya bukaci kwamishinonin su zage damtse wajen kawo sauyi a aikin gwamnati, musamman yaki da ‘yan bindiga da gyaran shari’a a jihar Kaduna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com