Rashin Tsaro: El Rufai Ya Fallasa Abin da Gwamnatin Tinubu Ke Yi Wa 'Yan Bindiga
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna ya sake yin magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a sassa daban-daban na kasar nan
- El-Rufai ya yi zargin cewa akwai sakacin gwamnatin tarayya kan yadda matsalar ke kara tabarbarewa
- Tsohon gwamnan ya nuna cewa gwamnati na daukar wasu matakai, wadanda maimakon su shawo kan matsalar, sai suka kara ruruta wutar ta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi zargin cewa gwamnati na biyan kuɗi ga ‘yan bindiga domin su daina kashe ‘yan Najeriya.
Nasir El-Rufai ya jaddada cewa bai kamata a tattauna da ‘yan bindiga ba, sai dai a kashe su gaba ɗaya.

Source: Twitter
El-Rufai ya bayyana hakan ne a shirin 'Politics Today' na tashar Channels TV a ranar Lahadi, 31 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane zargi El-Rufai ya yi kan gwamnatin Tinubu?
Tsohon gwamnan, wanda ya yi mulki daga 2015 zuwa 2023, ya yi ikirarin cewa shirin tattaunawa da ba wa kungiyoyin ta’addanci diyya wata manufa ce ta kasa wadda ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro (NSA) ya jagoranta.
"Abin da ban taɓa yi ba shi ne biyan ‘yan bindiga. Amma suna biyan ‘yan bindiga kudi. Suna karawa ‘yan bindiga karfi. Wannan shi ne abin da wannan gwamnati ta yi."
"Muna da hujjoji. Suna biyan ‘yan bindiga. Suna karfafa su. Wannan manufa ce ta kasa da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro ke jagoranta, kuma Kaduna na cikinta. Jihohi da dama suna adawa da hakan. Amma wannan shi ne tsarin yanzu.”
- Nasir El-Rufai
El-Rufai ya soki sulhu da 'yan bindiga
El-Rufai ya dage cewa tattaunawa da ‘yan ta’adda babban haɗari ne.
“Ra’ayina tun da farko shi ne cewa tubabben ɗan bindiga shi ne wanda aka kashe. Mu kashe su gaba ɗaya. Mu share su. Mu yi musu ruwan bama-bamai har sai sun kare. Sai kashi 5% da suke son a sauya musu tunani a gyara su."
- Nasir El-Rufai

Source: Twitter
Ya ce wannan tsarin da ake kira dabarar zaman lafiya ba tare da amfani da karfi ba, ba abin da yake yi sai karfafa kungiyoyin ta’addanci.
"Ba a taɓa tattaunawa da abokin gaba daga fuskar rauni ba. Ba a karawa abokin gaba karfi. Ba za ka ba shi kuɗi domin ya sayi karin muggan makamai ba. Wannan shi ne dalilin da yasa matsalar tsaro ba ta kau ba. Kuma ba za ta kau ba muddin wannan manufa ta ci gaba."
- Nasir El-Rufai
2027: El-Rufai ya ce Tinubu zai sha kashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi hasashen kan yadda zaben shugaban kasa na 2025, zai kaya.
El-Rufai ya bayyana cewa akwai yiwuwar sai zaben shugaban kasan ya kai zuwa ga zagaye na biyu.
Hakazalika, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ba zai kai labari ba, domin ko na biyu ba zai zo ba a zaben.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

