Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Maza Ta Tanka El Rufa'i bayan Kalamansa kan Faduwar Tinubu Zabe
- Fadar Shugaban Kasa ta mayar wa da Malam Nasir El-Rufa’i martani a kan hasashen zaben 2027 da ya yi a karshen makon jiya
- Daniel Bwala, hadimin Bola Tinubu, ya ce ikirarin tsohon gwamnan Kaduna game da zaben Shugaban Ƙasa ba zai yi tasiri ba
- Bwala ya yi zargin cewa Nasir El-Rufa’i yana ɗaukar kansa a matsayin wani babban ɗan siyasa, alhali ba shi da tasiri
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Fadar Shugaban Kasa ta yi tsokaci mai zafi kan kalaman tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i.
Kalaman tsohon gwamnan da su ka yamutsa hazo sun yi hasashe ne a kan rashin nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Source: Facebook
A cikin wani sako da ya wallafa shafinsa na X a ranar Lahadi, Bwala ya bayyana maganganun El-Rufa’i a matsayin shaci faɗi kawai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalaman El-Rufa'i da su ka fusata Bwala
A hira da aka yi da shi a Channels TV, Nasir El-Rufa'i ya ce Shugaba Bola Tinubu zai ƙare a matsayi na uku a zaben Shugaban Ƙasa mai zuwa.
A martaninsa, Daniel Bwala ya zargi El-Rufa'i da ɗaukar kansa fiye da kima a siyasance.
Bwala ya ce:
"Kalaman Malam Nasir El-Rufa'i da ke cewa Shugaban Kasa Bola Tinubu zai zo ta uku a zaben 2027 na daga cikin abin da mu ke kira shaci faɗi."
Bwala na ganin babu wani abu da zai tabbatar da kalaman tsohon Gwamnan, wanda da shi aka yi fafutukar tallata Tinubu a zaɓen 2023 da ya gabata.
Bwala ya caccaki Malam El-Rufa'i
Bwala ya zargi tsohon gwamnan Kaduna cewa ba ya iya cin zabe da kansa, sai ya dogara da wani fitaccen ɗan siyasa.
Ya ce:
“A tarihi, El-Rufa’i ba ya iya cin zabe sai ya jingina ga wani babban ɗan siyasa. Kuri’un Buhari ne suka sa ya zama gwamna da sake komawa kan mulki a baya."

Source: Facebook
Ya ci gaba da cewa lokacin da El-Rufa’i ya samu dama ya nuna karfinsa a zaben 2023, jam’iyyar APC ta sha kaye a jihar Kaduna.
A cewar Bwala:
“A zaben 2023, lokacin da ake bukatar ya nuna farin jininsa, APC ta sha kaye a kujerun majalisar dattawa, majalisar wakilai da ma kujerar shugaban kasa."
Hadimin Shugaban Ƙasa na ganin har yanzu gigin ubangida a siyasa na ɗibar El-Rufa'i yayin da tasirinsa ya riga ya yi rauni a Najeriya.
El-Rufa'i ya yi hasashen 2027
A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya sake tada cece-kuce a fagen siyasa bayan da ya yi hasashe kan yadda zaben shugaban kasa
A cewarsa, yanayin zaben mai zuwa zai yi zafi sosai, lamarin da zai sa babu wanda zai iya samun rinjaye a karon farko, har sai an tafi wani zagaye domin raba gardama.
Tsohon gwamnan ya ce akwai alamar cewa Shugaba Bola Tinubu ba zai iya samun damar lashe zaben ba, duba da manufofin gwamnatinsa a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

