Gwamnatin Tarayya Za Ta ba Ƴan Najeriya Hutu a Watan Satumbar 2025, An Ji Dalili

Gwamnatin Tarayya Za Ta ba Ƴan Najeriya Hutu a Watan Satumbar 2025, An Ji Dalili

  • Ana sa ran gwamnatin tarayya za ta ayyana hutun Maulidi a Satumbar 2025 domin tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (SAW)
  • Kaduna, Kano da Legas sun saba gudanar da biki tare da kira ga Musulmi su yi addu’o’i da jaddada zaman lafiya a tsakaninsu
  • Legit Hausa ta jero wasu muhimman abubuwa biyar da ya kamata kowanne Musulmi ya sani game da Maulidin Annabi a bana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Idan babu wani sauyi, gwamnatin tarayya za ta ayyana hutu ga duk ma’aikatan gwamnati da al’ummar Najeriya a farkon watan Satumba don bikin Mauludin Annabi 2025.

Legit.ng ta ruwaito cewa Maulud hutu ne na Musulunci da ake yi domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

Ana sa ran gwamnatin tarayya za ta ba da hutun maulidi a watan Satumba, 2025
Yadda Sarki Ahmad Nuhu Bamalli, ya yi hawan Mauludi a masarautar Zazzau a 2023. Hoto:@Zazzau_Emirate
Source: Twitter

Ana sa ran gwamnati ta ba da hutun Maulidi

Kara karanta wannan

Siyasar Sanatan APC da ministan Tinubu na fuskantar matsala, an bukaci su ja baya

Ana gudanar da wannan gagarumin biki a ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal, watau watan uku na kalandar Musulunci na kowace shekara, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musulmi na gudanar da Maulud ta hanyar tunani kan rayuwar Annabi da koyarwarsa, yin addu’o’i da tarurruka na musamman, tare da zagayen gari na 'yan makaranta.

Bikin na karfafa al’ummar Musulmi su yi koyi da kyawawan dabi’un Annabi, tare da yada soyayya, hakuri da juriya, da kuma inganta kyautatawa da hadin kai a cikin al’umma.

Saboda haka, Legit.ng ta bayyana cewa Mauludin Annabi shi ne hutun jama’a na gaba daya kadai da za a samu a Najeriya a watan Satumba 2025, domin taimaka wa jama’a wajen gudanar da bukukuwansu.

Gwamnati ta ba da hutun Maulidi a 2024

Idan ba a manta ba, a ranar 13 ga Satumbar 2024, muka ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ba da hutun Maulidi ga 'yan Najeriya.

A lokacin, gwamnatin tarayyar ta bakin ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ta ayyana Litinin, 16 ga Satumba, 2025, matsayin ranar hutun.

Gwamnati ta bukaci al'ummar Musulmi su yi riko da koyarwar Annabi Muhammad (S.A.W) musamman hakuri, zumunci, tausayi da kaunar mutane.

Kara karanta wannan

Kudin fansa: 'Yan bindiga sun dauke mutum 4700, an ji biliyoyin da aka rasa a shekara 1

Muhimman bangarori 5 na maulidi

  • Tunawa da haihuwar Annabi:

Muhimmin ginshiƙi shi ne girmama ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW), Manzon Allah kuma Hatimin Annabawa da aka saukar wa Alkur’ani mai girma.

A al'adance, ma'aikatar harkokin cikin gida ce ke sanar da hutun Maulidi a kowacce shekara.
Ministan harkokin cikin gida, Dr. Tunji Alausa. Hoto: @BTOofficial
Source: Twitter
  • Yawaita tasbihi da yi wa Annabi salati:

Ga Musulmi, rayuwar Annabi da koyarwarsa cike suke da darasi da shiriya. Maulud dama ce ta musamman ta mayar da lamura da yin tasibihi ga Allah da yi wa Annabi salati.

  • Nazari kan koyarwar Annabi:

Mauludi lokaci ne na nazari a kan koyarwa da dabi’un Annabi, irin su adalci, tausayi, da jinƙai.

  • Ƙarfafa dabi’u nagari:

Musulmi na karɓar ƙarfafawa wajen kwaikwayon dabi’un Annabi, su nuna karamci, da yin ƙoƙari wajen inganta al’umma.

  • Ƙarfafa hadin kai da zaman lafiya:

Maulud na haɗa Musulmi su ƙara ɗaure zumunci, gina fahimta, da tabbatar da zaman lafiya a cikin al’ummomi daban-daban.

Maulidi: 'Yan sanda sun yi shiri a Jigawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar Zawiyya Islamiyya da rundunar 'yan sanda sun yi zama na musamman a Jigawa, yayin da aka shiga watan Mauludi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jigawa ta ayyana hutun rana 1 ga ma'aikata saboda 'wani muhimmin biki'

Tare da Zawiyya, akwai kuma kungiyar kabilun da ba 'yan asalin Jigawa ba, inda aka tattauna kan bukukuwan Maulidi a jihar.

Rundunar 'yan sandan Jigawa, karkashin CP Dahiru Muhammad ta fada wa kungiyoyin matakan da aka dauka kan Mauludi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com