Jerin halaye guda 8 na Manzo Allah (S.A.W) wadanda Yahudu da Nasara suka aminta da su

Jerin halaye guda 8 na Manzo Allah (S.A.W) wadanda Yahudu da Nasara suka aminta da su

- Akwai wasu halaye na manzon Allah da wadanda ba musulmai ba suka aminta da su

- Mun samu mun nemo guda takwas daga cikin su

Manzon Allah (S.A.W) an sanshi mutum ne mai dabi'u kyawawa, wanda har yau a tarihi ba a samu kamar shi ba, kuma baza'a samu ba.

Saboda tsabar kyawawan halayenshi yasa Yahudu da Nasara wadanda su ba ma addininshi suke koyi dashi ba suka aminta da wasu kyawawan dabi'u irin nashi.

Manzon Allah (S.A.W) an tabbatar da cewa duk duniya ba a taba yin adalin mutum irinshi ba kuma baza ayi ba.

A wani bincike da muka yi mun gano wasu kyawawan dabi'un Annabi Muhammadu (S.A.W) wanda masu bincike irin na kimiyya suka aminta da su.

1. Tashi da wuri

Manzon Allah (S.A.W) yana kwanciya bacci da wuri, kuma yana tashi da asuba a kowacce rana. Bincike ya nuna cewa tashi da wuri yana da mutukar muhimmanci ga lafiyar dan adam.

2. Cin abinci sama-sama

Cin abinci ba da yawa ba yana maganin ciwuka da dama, hakan ya samo asali ne daga wurin Manzo (S.A.W), inda a yanzu kuma masana fannin kimiyya suka tabbatar da hakan.

3. Cin abinci a hankali

Mun san da cewa jikin mu na daukar minti 20 ne kacal ya aikawa kwakwalwar mu cewa mun koshi. Cin abinci a hankali yana sawa mutum yaci abinci ba da yawa ba, kuma yana taimakawa mutuka wurin narkar da abinci. Annabi yayi hakan kuma ya bukaci mutane suyi koyi dashi.

4. Cin abinci tare da 'yan uwa da abokai

Manzon Allah (S.A.W) ya bukaci mutane su dinga yin hakan, kuma masana sun yi bincike sun gano cewa cin abinci tare da mutane yana kawo raguwar damuwa, kuma yana sanya ladabi na cin abinci ga iyalai da yara kanana.

KU KARANTA: Wani matashi da ya kashe kanshi ya bar wa iyayenshi wasika mai ratsa zuciya

5. Shan ruwa

Masana sun bada sanarwar cewa idan mutum yasha ruwa da yawa a cikin lokaci kalilan, yakan kamu da ciwon kai, da jiri. Shan ruwa a hankali yana taimakawa jikin dan adam matuka.

6. Azumi

Wani bincike ya nuna cewa ba wai cin abinci ne kawai yake kara mana lafiya ba, hatta lokutan da muke cin abin yana taimakawa matuka wurin samun lafiyar mu. Azumi al'adace ta Annabi Muhammadu (S.A.W).

7. Cin dabino

Dabino shine abu mafi muhimmanci da mutum ya kamata ya karya azumi dashi, suna rage yawan siga a jikin mutum, sannan suna warware hanjin ciki, kafin kaje mawar cin abinci.

8. Motsa jiki

Manzo (S.A.W) ya umarci mutane da su dinga motsa jikinsu. Hakazalika sallah tana daya daga cikin abubuwan da suke sanya mutum ya motsa jikinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng