Fusatattun Matasa Sun Yi Ajalin Mata a Najeriya Kan Zargin Batanci Ga Manzo SAW

Fusatattun Matasa Sun Yi Ajalin Mata a Najeriya Kan Zargin Batanci Ga Manzo SAW

  • Wata mai sayar da abinci mai suna Ammaye ta rasa ranta a hannun matasa a Mariga da ke jihar Niger a Arewa ta Tsakiyar Najeriya
  • Shaidu sun ce lamarin ya fara ne bayan cece-kuce tsakaninta da wani saurayi a Igwama, inda ta fadi kalaman da aka dauka batanci
  • Duk da an kai ta gaban hakimi, matasa sun kwace ta daga hannun jami’an tsaro suka jajjefe ta har ta mutu, daga bisani an samu zaman lafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Mariga, Niger - Mutane sun ga tashin hankali bayan wasu matasa da suka fusata sun hallaka wata mata mai sayar da abinci a jihar Niger.

An hallaka matar mai suna Ammaye a karamar hukumar Mariga da ke jihar, bayan matasa sun zarge ta da batanci ga Annabi Muhammad.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci da Kirista sun 'karyata' ikirarin da Tinubu ya yi a Kasar Brazil

Matasa sun hallaka mata a Niger kan zargin batanci
Taswirar jihar Niger da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Mata ta rasa ranta kan zargin batanci

Lamarin ya faru ne a Kasuwan Garba cikin yankin, inda shaidu suka ce cece-kuce ya fara ne a Igwama tsakaninta da wani saurayi ɗan uwanta, cewar rahoton AIT.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce saurayin ya yi mata wasa da cewa yana so ya aure ta don “raya Sunnah”, sai ta fadi kalamai da aka dauka batanci.

Rahotanni sun ce an kai karar zuwa fadar Hakimin Kasuwan Garba, inda aka yi mata tambaya kuma ta maimaita kalamanta da ake kallo a matsayin batanci ga Manzo SAW.

Daga nan Hakimi ya mika ta ga jami’an tsaro don ci gaba da bincike, amma gungun matasa suka nace cewa a kashe ta nan take.

Ko dayake jami’an tsaro sun yi kokarin kare ta, sai taron matasan ya rinjaye su, inda suka jajjefe ta da duwatsu har ta mutu.

Daga bisani an samu dawowar zaman lafiya a yankin duk da har yanzu babu wani bayani daga hukumomi kan matakin da za a dauka.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Babbar mota ta murkushe Musulmi yana sauri zuwa masallacin Juma'a, an yi rikici

An yi ajalin mata kan zargin batanci ga Annabi SAW
Babban sufetan yan sanda a Najeriya, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Wane martani jami'an tsaro suka yi?

Shugaban karamar hukumar Mariga, Abbas Adamu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa an dawo da zaman lafiya a yankin bayan tashin hankali..

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan sakamako babu wata sanarwa daga jami'an tsaro kan wannan lamarin da ya faru a karamar hukumar Mariga.

A Najeriya dai an sha daukar doka doka a hannu musamman kan zargin batanci wanda wasu ke ganin bai dace ba yayin ake ci gaba da wayar da kan jama'a game da hakan.

Wannan ba shi ne karon farko ba da hakan ke faruwa musamman a Arewacin kasar da ba a daukar wani cin mutunci ko wasa da sunan fiyayyen halitta

An kashe Musulmi a Sokoto kan zargin batanci

Tun baya, kun ji cewa wasu mutane sun yi ajalin wani mahauci mai suna Usman Buda wanda ake zargin ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari Kano da dare, sun sace mata bayan kashe rai

Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin Usman Buda yana siyar da kayan ciki ne a mahautar da ke Sokoto.

Kakakin rundunar 'yan sandar jihar ya tabbatar faruwar lamarin inda ya ce sun dauki gawar zuwa asibiti domin bincike da kulawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.