Shaidu Sun Bayyana, An Fara Jin Yadda Hadimin Gwamnan Kano Ya Karkatar da N6.5bn
- An kara samun bayanai kan badakalar Naira biliyan 6.5 da ake zargin hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Rogo da aikatawa
- Wasu yan kasuwar canji sun tabbatar wa jami'an bincike cewa an yi amfani da su wajen canza sama da Naira biliyan daya zuwa Dalolin Amurka
- Wannan bayanai na fitowa ne bayan gwamnatin Kano ta wanke Abdullahi Rogo daga zargi, inda ta ce ofishinsa na aiki ne bisa tsarin doka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - An fara samun shaidu kan zargin da ake wa hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Rogo na karkatar da Naira biliyan 6.5 daga baitul-mali.
Wasu 'yan canjin (BDC) sun bayar da shaidar da ke nuna Abdullahi Rogo, mai kula da tsare-tsare da ayyukan gwamna na da hannu a wannan badakala da ake kan bincike.

Source: Facebook
Premium Times ta ruwaito cewa hukumomin yaki da rashawa na Najeriya, EFCC da ICPC na ci gaba da bincike da tattara bayanai kan zargin da ake wa hadimin Abba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan baku manta ba, gwamnatin Kano ta fito ta wanke hadimin gwamnan daga zargi, tana mai cewa babu wasu kudi da aka fitar ba a kan tsarin kasafin kudi ba.
Sai dai a bayanin da yan canji suka yi wa EFCC da ICPC, sun nuna yadda aka yi amfani da su wajen cire makudan kudi da yawun Abdullahi Rogo.
'Yan canji sun ba da shaida kan hadimin Abba
Wani dan canji mai suna Gali Muhammad ya shaida wa jami'an bincike cewa Abdullahi Rogo da kansa ya tuntube shi yana son Dalolin Amurka.
Sai kuma wani mai suna, Nasiru Adamu, wanda shi ne shugaban Kazo Nazo da Namu Nakune, ya ce a ranar 9 ga Nuwamba, 2023, Muhammad ya zo wajensa yana bukatar Daloli.

Kara karanta wannan
Malaman Musulunci da Kirista sun 'karyata' ikirarin da Tinubu ya yi a Kasar Brazil
Nasiru ya ce an turo wa kamfanoninsa Naira biliyan 1.17 kai tsaye daga asusun da gwamnatin Kano ke karbar kasonta daga gwamnatin tarayya a wannan rana.
Ya ce daga nan ya musanya kudin zuwa Daloli, ya bai wa Muhammad, wanda ya kai wa Rogo a Ofishin Gwamnatin Jihar Kano da ke Asokoro, Abuja.
A wata sanarwa daban, Muhammad ya tabbatar da wannan magana, inda ya ce hannu da hannu ya mika Dala miliyan daya ga hadimin gwamnan a Abuja.
An fara gano masu hannu a badakalar Rogo
Bayan yan canji sun bada bayanansu, jami'an bincike sun gayyato Akanta Janar na Kano a wancan lokacin da ake zargin an yi sama da fadi da kudin watau Abdussalam Abdulkadir.
Bayanan ICPC sun nuna cewa Abdulkadir ne ya bada umarnin fitar da Naira biliyan 1.17 ta hanyar amfani da takardun bogi na “izini”, da aka yi kamar kamfanonin A.Y. Mai Kifi Oil and Gas Ltd. da Ammas Petroleum Company Ltd. suka sanya hannu.

Source: Twitter
Shugabannin wadannan kamfanonin daga baya sun shaida wa ICPC cewa kwangilolin duk na bogi ne, kuma sun sanya hannu bisa umarnin Abdulkadir.

Kara karanta wannan
Jerin ayyukan Naira tiriliyan 3.9 da aka amince a yi a Lagos a shekara 2 na Tinubu
Ko da yake ya amince da bada umarnin biyan kudin, Akanta Janar din bai iya bayyana dalilin da ya sa aka karkatar da kudin zuwa wurin yan canji ba.
Binciken ICPC ya gano cewa Abdulkadir ya hada baki da Abdullahi Rogo wajen karkatar kudin gwamnati ta hanyar amfani da yan canji.
Abdullahi Rogo ya maka Jafar Jafar a kotu
A wani labarin, kun ji cewa hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Rogo ya kai karar Jaafar Jaafar gaban wata kotun Majistire kan zargin bata masa suna.
Kotu ta ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da Rogo ke yiwa Jaafar, mawallafin jaridar Daily Nigerian.
Wannan umarni ya fito daga kotu ta 15 da ke Nomansland, karkashin jagorancin Alkalin kotu, Malam Abdulaziz M. Habib da ke Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
