Abu Ya Girma: Jihohin Arewa da Aka Taso Tinubu a Gaba Ya Sanya Dokar Ta Baci
Rashin tsaro a Arewacin Najeria na kara kamari duk da kokarin jami'an tsaron domin ganin an kawo karshen lamarin.
Jihohin Arewacin Najeriya musamman Katsina, Zamfara, Kaduna, Sokoto sun fi shan fama da rashin tsaro da ke jawo rasa rayuka da dukiyoyi.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
An dauki shekara da shekaru ana fama da matsalar rashin tsaro a yankua dabam-dabam.
Sauran jihohin a Arewacin Najeriya sun hada da Niger, Benue, Kebbi, Sokoto, Taraba da wasu yankuna a jihar Adamawa.

Source: Facebook
Har ila yau, a yankin Arewa maso Gabas, jihohin Borno da Yobe na shan fama da matsalar Boko Haram yayin Bauchi ma aka rasa rayuwa saboda harin yan bindiga, cewar Punch.
Jihohin da ake son Tinubu ya sanya dokar ta-baci
Dalilin haka ya sa ake ta kiran gwamnatin Bola Tinubu ta yi gaggawar daukar matakai masu tsauri domin kawo karshe lamarin.
Daga cikin kiraye-kirayen da ake yi har da bukatar sanya dokar ta-baci a jihohin domin dakile matsalolin ta'addanci.
Legit Hausa ta duba muku jihohin Arewacin Najeriya da ake neman Tinubu ya kakaba dokar ta-baci a Najeriya.
1. Kiraye-kirayen dokar ta-baci a Zamfara
Yayin da ake ta surutu kan abin da ya faru a Rivers bayan dakatar da gwamnan da mukarrabansa, ƙungiyar CDD ta bukaci Bola Tinubu ya sa dokar ta ɓaci a jihar Zamfara.
Ƙungiyar mai rajin tabbatar da shugabanci na gari ta ce gwamnatin jihar Zamfara ta aikata laifukan da suka karya dokar kasa da kuma gagara dakile matsalar tsaro.
Daga cikin laifuffukan da kungiyar ta lissafo akwai batun dakatar da ƴan Majalisar Dokokin Zamfara kan nuna ɓacin ransu.
Har ila yau, wata ƙungiya a Arewa ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci a jihar Zamfara saboda tabarbarewar tsaro.
Kungiyar NCAJ ta zargi gwamnatin Zamfara da yin salon mulkin 'kama karya' yayin da ta ce jihar ba ta samun wani ci gaba a yanzu.

Kara karanta wannan
Jerin ayyukan Naira tiriliyan 3.9 da aka amince a yi a Lagos a shekara 2 na Tinubu
NCAJ ta ce garuruwa sun koma biyan haraji ga ‘yan bindiga, jami’an gwamnatin jihar na amfana da haramtacciyar hakar ma’adinai.

Source: Facebook
2. ADC ta bukaci dokar ta-baci a Zamfara, Katsina
Jam’iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya soke tafiyarsa da ya yake yi kasashen waje a wancan lokaci ya kuma ayyana dokar ta-baci.
ADC ta ce kashe-kashen al’umma a Malumfashi a Katsina da hare-haren Zamfara na nuni da rushewar tsarin tsaron Najeriya baki ɗaya.
Jam’iyyar ta kuma caccaki shugabannin PDP da suka gudanar da taron siyasa a Zamfara jim kaɗan bayan harin, tana kiran hakan rashin tausayi, Tribune ta tabbatar.

Source: Facebook
3. Cibiyar CJI ta roki dokar ta-baci a Benue
A Benue kuma, Cibiyar CJI ta nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da samun kashe-kashe a jihar sanadin hare-haren yan bindiga.
Cibiyar daga bisani ta roki shugaba Bola Tinubu ya yi gaggawar sanya dokar ta-baci a jihar da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
Gwamnatin jihar ta fusata da wannan kira inda ta yi gargadi tare da cewa gwamnatin jihar za ta iya magance matsalolin.
Sakataren yada labaran gwamnan Benue, Tersoo Kula ya caccaki masu kira da a ayyana dokar ta-baci a jihar, ya ke cewa ba su da masaniya game da abin da ke wakana a jihar.
Ya gargadi waɗanda ke ƙoƙarin tayar da husuma da fitina a jihar da su tattara su bar Benue, domin mutanen jihar ba za su amince da ƙirƙirarrun zarge-zarge da ha'inci na siyasa ba.

Source: Facebook
4. Dokar ta-baci a Yankin Arewa gaba daya
Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta bukaci Bola Tinubu ya dauki mataki mai tsauri kan rashin tsaro da ya addabi al'umma domin tabbatar da zaman lafiya.
Dattawan sun roke shi da ya ayyana dokar ta baci kan matsalolin tsaro da suka ki ci suka ki cinyewa a yankin wanda ya jawo asarar rayukan al'umma.
NEF ta ce kashe sojoji da fararen hula a jihohi kamar Benue, Niger, Zamfara da Sokoto na nuna gazawar gwamnati wajen kare rayuka.
Daga bisani, kungiyar ta bukaci Tinubu ya kakaba dokar ta-baci a yankin gaba daya musamman a jihohin da suka fi fama da matsalolin tsaro.

Source: Facebook
Rahoto ya jero jihohin da ke fama da ta'addanci
A baya, mun kawo muku cewa wani rahoton bincike ya bayyana cewa, a cikin shekara guda, ‘yan Najeriya sun biya biliyoyin kudi a matsayin kudin fansa ga masu garkuwa.
Binciken ya gargadi gwamnati ta dauki matakan gaggawa da lalata hanyar kudaden shiga na masu garkuwa, domin hana wannan sana’a ta zama babba.
An jero jihohin Zamfara da Kaduna da kuma Katsina a matsayin wadanda suka fi shan fama da matsalolin ta'addanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


