'Yan Bindiga Sun Sha Wuta hannun Sojojin Sama, Sun Sako Mutanen da Suka Sace a Zamfara
- Dakarun sojoji na ci gaba da kokarin ganin an samu tsaro a jihar Zamfara wadda ke fama da matsalar 'yan bindiga da 'yan ta'adda
- Sojojin sama na rundunar Operation Fansan Yanma sun kai dauki bayan da 'yan bindiga suka yi awon gaba da mutane masu yawa a wasu kauyuka
- Ruwan wutan da jiragen sojojin saman suka yi wa 'yan bindigan, ya tilasta musu tserewa domin tsira da rayukansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Dakarun sojojin sama na rundunar Operation Fansan Yanma sun ragargaji 'yan bindiga a jihar Zamfara.
Jiragen sama na rundunar sojojin sun tilasta wa ’yan bindiga sako mutum 70 da suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.

Source: Getty Images
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Yayin da Assadus Sunnah ke kiran sulhu, Hatsabibin ɗan bindiga ya kuma sakin mutane 142
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojojin sama sun kubutar da mutane a Zamfara
Majiyoyi sun tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Asabar, 30 ga watan Agustan 2025.
Sun bayyana cewa ’yan bindiga sama da 150 dauke da makamai ne suka dauke mutanen a wasu kauyuka na karamar hukumar Bukkuyum ranar Alhamis.
Kauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Ruwan Jema, Yashi, Gasa Hula, Kurfan Danya, Rafin Maiki, Ruwa Rana da Barikin Daji.
Majiyoyin sun bayyana cewa ’yan bindigan dauke da manyan makamai sun yi kokarin tserewa da mutanen bayan sun nemi makudan kudin fansa, amma dakarun sojoji sun hanzarta tura jiragen sama zuwa yankin.
"Lokacin da ’yan bindigan suka hangi jiragen sojojin sama, sai suka rikice. Sai suka saki mutanen a cikin dazuzzuka suka kuma yi kokarin gudu da baburansu."
"Mata shida sun samu nasarar tserewa a wannan ranar.”
- Wata majiya
Dakarun Sojojin sama sun ragargaji 'yan bindiga
Majiyoyin sun kara da cewa hare-haren bama-bamai da aka ci gaba da kai wa a yankin daga baya, sun tilasta wa ’yan bindigan su saki dukkan mutanen da suke tsare da su.
Idan ba manta ba dai a makon da ya gabata, dakarun sojoji sun kai mummunan farmaki a maboyar ’yan bindiga da ke cikin dajin Gyado, inda aka kashe fiye da mayaka 100 ciki har da wasu manyan kwamandojinsu.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan hare-haren sojojin sama
- Jiragen sojojin sama sun saki bama bamai a dajin Zamfara, an hallaka miyagu 100
- Sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta a garin Raan, an rasa rayukan ƴan bindiga 30
- Jiragen yaki sun kona 'yan bindiga kurmus suna bikin aure a dajin Zamfara
- Sojojin sama sun yi barin wuta kan 'yan ta'addan ISWAP, an tura kwamandoji zuwa lahira
Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yanma, sun samu nasarar dakile wani harin 'yan bindiga a jihar Zamfara.
Dakarun sojojin sun samu nasarar dakile harin ne a wani kauye mai suna Tashar Gemu da ke karamar hukumar Malumfashi.
Sojojin sun samu nasarar hallaka dan bindiga guda daya tare da ceto wasu mutane da suka yi yunkurin tafiya da su zuwa cikin daji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
