Shettima Ya Isa Kaduna Tare da Manyan Kasa domin Daurin Auren Jikar Buhari

Shettima Ya Isa Kaduna Tare da Manyan Kasa domin Daurin Auren Jikar Buhari

  • Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya isa Kaduna domin halartar ɗaurin auren ’ya ’yan Kyaftin Junaid Abdullahi da Alhaji Shehu Muazu
  • Rahotanni sun bayyana cewa za a gudanar da ɗaurin auren ne a Masallacin Juma’a na Yahaya Road da ke Ungwan Rimi a birnin Kaduna
  • Amaryar, Halima Amira Junaid ita ce jikar marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, yayin da ango Walid Shehu Muazu ɗan Iyan Katagum ne

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Za a gudanar da babban bikin aure a Kaduna da ya haɗa manyan jami’an gwamnati, abokai da dangin tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari.

Auren da za a daura shi a Masallacin Juma’a na Yahaya Road, Ungwan Rimi, ya zama wani gagarumar taro da ya jawo hankalin jama’a saboda matsayin dangin da abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Tinubu, Abba da manya sun halarci auren ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa a Kano

KAshim Shettima a lokacin auren jikar Buhari a Kaduna
KAshim Shettima a lokacin auren jikar Buhari a Kaduna. Hoto: @stanleynkwocha
Source: Twitter

Hadimin mataimakin shugaban ya walllafa a X cewa Kashim Shettima ya isa Kaduna domin halartar ɗaurin auren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tarbi Kashim Shettim a jihar Kaduna

Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, tare da wasu mambobin majalisar zartarwa ta jihar sun tarbi Sanata Kashim Shettima a filin jirgin sama.

Taron ya kasance al’amari na musamman domin girmama marigayi Buhari, wanda ya rasu a watan jiya a London.

Bikin ya zo ne kwanaki bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasa, lamarin da ya sanya wannan aure ya zama abin tunawa da girmamawa ga rayuwarsa.

Cikin tawagar mataimakin shugaban kasa Shettima har da mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia.

Sauran wadanda suka tarbi Kashim Shettima

A filin jirgin saman, Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya jagoranci maraba da shi, tare da wasu ministoci da manyan ’yan siyasa.

Daga cikin ministocin da suka halarci bikin akwai Ministan Sufuri, Sanata Ahmed Sa’idu Alkali, da Ministan Muhalli, Alhaji Balarabe Abbas Lawal.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala, Sheikh Tukur Kola ya rasu a jihar Kebbi

Haka kuma, an ga Hon. Usman Ali Zannah, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kaga/Gubio/Magumeri.

Labarin daura auren jikar shugaba Buhari

Amaryar, Halima Amira Junaid, ita ce jikar marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, ta hanyar mahaifiyarta Zulai wanda ta auri Kyaftin Junaid Abdullahi.

Angon kuwa, Walid Shehu Muazu, ɗan Iyan Katagum ne, wanda iyalinsa suka shahara a yankin Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Bikin ya kasance lokaci na farin ciki, duk da cewa ana ci gaba da jin baƙin cikin rashi, bayan mutuwar Muhammadu Buhari a watan jiya.

Shettima ya ziyarci shugaba Buhari a gidansa na Kaduna.
Shettima ya ziyarci shugaba Buhari a gidansa na Kaduna. Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

A makon da ya gabata aka yi kwana 40 da rasuwar tsohon shugaban na Najeriya.

Shettima, wanda ya jagoranci jigilar gawar Buhari daga Landan zuwa Najeriya, ya halarci dukkan harkokin jana’iza da aka gudanar a Daura, Katsina.

Bayan jana’izar marigayi Buhari, iyalan tsohon shugaban kasar sun koma Kaduna, inda suka zauna don ci gaba da rayuwarsu.

Shettima ya je daurin aure jihar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya je jihar Kano daurin aure.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dauki mataki yayin da masu Mauludi suka fara zagayen gari a Jigawa

Bayanai sun tabbatar da cewa an daura auren dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Arch. Namadi Sambo.

Baya ga Sanata Kashim Shettima, rahotanni sun nuna cewa manyan 'yan siyasa sun halarci daurin auren, ciki har da mataimakin gwamnan Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng