Majalisa Ta Yi Doka, An Kafa Sharadi ga duk Masoyan da Za Su Yi Aure a Musulunci
- Majalisar dokokin Kebbi ta amince da dokar gwajin lafiya kafin aure, 2025, wacce za ta kawo sauyi a tsarin daura aure a fadin jihar
- Dokar dai ta wajabtawa duka masoyan da za su yi aure su yi gwaje-gwajen lafiya kamar nau'in kwayoyin halitta, jini da cutar kanjamau
- Bayan haka dokar ta tanadi hukunci ga malamai ko sarakuna da suka yi kunnen kashi, a halin yanzu ana jiran gwamna ya sa hannu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, wacce galibin al'ummarta musulmai ne tana shirin kafa dokar gwajin lafiya kafin aure.
Majalisar dokokin jihar Kebbi ta amince da kudirin doka na gwajin lafiya kafin daura aure.

Source: Facebook
Majalisa ta kafa dokar gwajin lafiya kafin aure
Tashar Channel tv ta tattaro cewa dokar ta wajabta yin gwajin lafiya ga duk mace da namijin da ke shirin yin aure a fadin jihar Kebbi.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kutsa cikin gida, sun sace malamin addini kuma ma'aikacin asibiti
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudirin, wanda kwamitin majalisa kan harkokin lafiya ya gabatar, ya samu amincewa bayan karatu na farko, na biyu da na uku.
Bugu da kari, shugaban majalisar dokokin Kebbi, Rt. Hon. Muhammad Usman, ya amince da kudurin dokar a hukumance.
Sharadin da aka kafa wa masoya kafin aure
A karkashin wannan doka, duk masoyan da ke shirin yin aure dole ne su yi wasu muhimman gwaje-gwaje, ciki har da gwajin jini da nau’in kwayoyin halitta (genotype) da na cututtuka.
Dokar ta tanadi cewa za a yi wadannan gwaje-gwaje ne a cibiyoyin lafiya da gwamnati ta amince da su, watanni uku da makonni biyu kafin daura aure.
Idan Gwamna Nasir Idris ya rattaba hannu a kan dokar, za a bukaci takardar shaidar lafiya daga likita kafin a iya kammala daura aure a hukumance.
Hukuncin wadanda suka karya dokar a Kebbi
Kudirin ya kuma tanadi hukunci ga wadanda suka yi kunnen kashi, watau suka ki bin wannan doka yayin aure.
Malamai, sarakuna ko jami’an da suka daura aure ba tare da shaidar lafiya da aka tabbatar ba, na iya fuskantar tara har ₦200,000 ko kuma daurin watanni shida a gidan yari.
Haka kuma, ma’aikatan lafiya da suka bayar da sakamakon gwaji na bogi za su iya fuskantar tara har ₦1,000,000 ko kuma daurin shekara guda.

Source: Facebook
Za a aiwatar da dokar tare da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya da ta kula da harkokin addini, tare da shugabannin al’umma.
Haka zalika za a dora wa alkalan kotunan Majistire da na kotunan shari'a alhakin sauraro da yanke hukuncin kararrakin da suka shafi wannan doka
A halin yanzu, an mika kudirin dokar ga gwamnan jihar Kebbi domin ya sanya han nu inji rahoton TVC News.
Gwamnan Kebbi ya nada Sarkin Zuru
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris ya amince da nadin Sanusi Mikailu a matsayin sabon sarkin Zuru.
Majalisar masu zaɓen sarki ce ta gabatar da sunan Sanusi Mikailu ga mai girma gwamna bayan tantance waɗanda suka nemi sarautar Zuru.
Rahotanni sun bayyana cewa mutane uku ne suka tsaya takarar sarkin, kuma Sanusi ya samu mafi rinjayen kuri, da ya ba shi nasara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
