Jerin Ayyukan Naira Tiriliyan 3.9 da aka Amince a Yi a Lagos a Shekara 2 na Tinubu

Jerin Ayyukan Naira Tiriliyan 3.9 da aka Amince a Yi a Lagos a Shekara 2 na Tinubu

  • A cikin shekaru biyu kacal, gwamnatin tarayya ta amince da ayyuka a Lagos da suka kai darajar Naira tiriliyan 3.9
  • Adadin ya fi duk abin da jihohi 18 na Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas suka samu
  • Ayyukan sun haɗa da gina gadar Carter, titin bakin teku, filin jirgin sama da kuma ayyukan inganta wutar lantarki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Rahotanni sun nuna cewa Lagos ta fi kowace jiha amfana da amincewar kwamitin zartarwa na tarayya (FEC) a cikin shekara biyu na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Bincike ya nuna cewa jimillar ayyukan da aka amince da su a jihar Lagos ya kai na Naira tiriliyan 3.9.

Shugaba Bola Tinubu na jawabi a wani taro
Shugaba Bola Tinubu na jawabi a wani taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Daily Trust da ta fitar da binciken ta ce adadin ya ninka abin da aka bai wa Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas, inda aka ware musu Naira tiriliyan 3.56 kacal.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari Kano da dare, sun sace mata bayan kashe rai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu wanda shi ne ke jagorantar FEC kuma dan asalin Lagos ne, ya jagoranci amincewa da manyan ayyukan da suka shafi jiragen sama, hanyoyin mota, gine-gine da sauransu.

Ayyukan filin jirgin sama a Legas

Daya daga cikin manyan ayyukan da aka amince da shi shi ne sabunta filin jirgin saman Murtala Muhammed a Lagos da zai lashe Naira biliyan 712.26.

Punch ta wallafa cewa wannan aikin na cikin shirin gyara kayayyakin jiragen sama na kasa baki daya da darajarsa ta kai Naira biliyan 900.

Bugu da kari, an amince da Naira biliyan 49.9 domin kewayen shinge a filin jirgin saman, tare da na’urorin CCTV, fitilu masu amfani da hasken rana da kuma hanyar sintiri domin inganta tsaro.

Haka kuma, a watan Mayu 2024, an amince da Naira biliyan 4.2 don samar da kayan ceto da ake amfani da su wajen janye jirgin da ya samu matsala a filin jirgin sama na Lagos.

Kara karanta wannan

Abubuwa sun dauki zafi, an fara yunkurin tsige Sarki mai martaba a Najeriya

Ayyukan hanyoyi da gine-gine a Legas

A bangaren hanyoyi, majalisar ta amince da aikin gina gadar Carter a Lagos da zai ci Naira biliyan 359.

Gwamnatin ta amince da gyaran bakin teku na Ebute-Ero/Outer Marina da zai lashe Naira biliyan 176.5 domin dakile lalacewar da ke barazana ga sansanonin soji.

Haka kuma, a watan Fabrairu 2024, an amince da Naira tiriliyan 1.06 domin gina sashen farko na hanyar bakin teku ta Lagos-Calabar daga Victoria Island zuwa Eleko a Legas.

A watan Agusta 2024 kuma, majalisar ta amince da daya sashen hanyar mai tsawon kilomita 55 daga tashar jiragen ruwa ta Lekki zuwa kan iyakar Ogun da darajar Naira tiriliyan 1.6.

Shugaba Tinubu a taron maja;lisar zartawa ta FEC a Abuja
Shugaba Tinubu a taron maja;lisar zartawa ta FEC a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ayyukan wutar lantarki a Legas

A yunkurin inganta wutar lantarki, majalisar ta amince da Naira biliyan 13 a matsayin diyya ga wadanda aka shafa wajen mallakar filaye a cikin aikin Lagos Industrial Transmission Project.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa aikin zai taimaka wajen sabunta tsofaffin kayayyakin wuta, kara dorewar lantarki da sauransu.

Kara karanta wannan

Ana hallaka jama'ansa, Gwamna Radda zai kashe Naira miliyan 680 a gyaran maƙabartu

Bincike ya kuma nuna cewa jimillar ayyukan da FEC ta amince da su a yankin Kudu maso Yamma sun kai Naira tiriliyan 5.97, inda Lagos ta samu kaso mafi tsoka.

Za a yi cibiyar kayan gini a Legas

A wani rahoton, kun ji cewa an ware fili mai fadin hekta 200 domin kafa cibiyar samar da kayan gini a Legas.

Rahotanni sun bayyana cewa ministan gidaje na kasa, Ahmed Dangiwa ne ya bayyana haka yayin da ya zyarci jihar.

Ministan ya sanar da cewa akwai shirin kafa irin cibiyar a sauran yankunan Najeriya da za su biyo baya nan gaba kadan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng