Tinubu, Abba da Manya Sun Halarci Auren Ɗan Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa a Kano
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya halarci daurin auren dan tsohon mataimakin shugaban kasa a Kano
- Mataimakinsa, Kashim Shettima shi ya wakilci shugaban kasa a daurin auren ɗan Namadi Sambo da aka yi a Kano
- Daurin auren ya gudana a masallacin Al-Furqan tare da sadaki na N500,000 inda Shettima ya isar da sakon fatan alheri daga Tinubu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Shugabanni da yan siyasa da dama sun halarci daurin auren dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo da aka yi a Kano.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima a ranar Juma’a ya wakilci shugaba Bola Tinubu a daurin auren da aka gudanar a jihar.

Source: Twitter
Gwamnatin Kano ta tarbi Shettima a Kano
Hakan na cikin wata sanarwa da Kashim Shettima ya wallafa a shafinsa na X a yau Juma'a 29 ga watan Agustan 2025 da muke ciki.
An daura auren Abdullah, ɗan tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, a yau Juma'a a Kano da ke Arewa maso Yamma a Najeriya.
Da isarsa, Shettima ya samu tarba daga mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo wanda ya wakilci Gwamna Abba Yusuf, tare da Namadi Sambo, Sanata Danjuma Goje, da sauran manyan baki.

Source: Twitter
Kano: An daura auren dan Namadi Sambo
Daurin auren tsakanin Abdullah Sambo da ɗiyar Farfesa Abdullahi Umar ya gudana a masallacin Al-Furqan karkashin jagorancin limamin masallacin, Sheikh Bashir Umar, tare da sadaki N500,000.
A yayin da Shettima ya tsaya ga dangin ango, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, ya wakilci mahaifin amarya.
Shettima ya isar da sakon fatan alheri daga Shugaba Tinubu ga ma’auratan, tare da fatan samun albarka, natsuwa da nasara a rayuwar aure bayan yi musu addu'o'i na musamman.
Manyan baki da sun halarta sun haɗa da Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, Ministan Cigaban Yankuna, Abubakar Momoh, tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido da shugaban PDP, Umar Damagum.

Source: Twitter
Wani daurin aure da Shettima ya sake halarta
Bayan dawowarsa daga Kano, Shettima ya halarci daurin auren Khalifa Ishaq Baffa Jibrin da Maryam Amani Yahaya a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
Daurin auren ya gudana karkashin jagorancin limamin babban masallacin, Dr. Muhammad Kabir Adam, inda aka biya sadakin N500,000, Shettima ya bayar da amarya Maryam.
Baki da suka halarci bikin Abuja sun haɗa da Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, mataimakin gwamnan Borno, Umar Kadafur, tare da sauran manyan baki na ƙasa.
Shettima, Sanusi II sun halarci jana'izar Sarkin Zuru
Kun ji cewa mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya wajen halartar jana’izar marigayi Sarkin Zuru.
Marigayi Sarkin ya rasu a birnin London yana da shekaru 81, inda aka birne shi bayan sallar Juma’a a garin Zuru, jihar Kebbi.
Majiyoyi sun nuna cewa shugabanni da sarakunan gargajiya daga sassa daban-daban na ƙasar sun halarci jana’izar tare da yin ta’aziyya ga jama'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

