Allahu Akbar: Babbar Mota Ta Murkushe Musulmi Yana Sauri Zuwa Masallacin Juma’a, an Yi Rikici
- Wani mutum ya rasa ransa bayan babbar motar kaya ta murkushe shi yayin da yake hanzarin zuwa sallar Juma’a a yau
- Shaidu sun bayyana cewa motar kirar SUV ce ta buge shi, daga nan kuma tirela da ke gudu ta murkushe shi a kan hanyar East- West
- Wannan al’amari ya ta da hankula, inda Musulmi suka toshe hanya suna zanga-zanga, kafin ‘yan sanda su shawo kan lamarin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Al'ummar Musulmi a Rivers sun tare babbar hanya a jihar bayan buge wani dan uwansu yayin sallar Juma'a.
Babbar mota a birnin Port Harcourt, dauke da kaya ta murkushe Musulmin da ke hanzarin zuwa sallar Juma’a a yau 29 ga watan Agustan 2025.

Source: Original
Musulmi ya rasu a kokarin tafiya sallar Juma'a

Kara karanta wannan
Borno: Mayakan boko haram sun yi wa matafiya kwantan bauna, sun bude wa motarsu wuta
Rahoton Vanguard ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya abin takaicin ya afku ne a kwanar Nkpolu, hanyar East-West da ke birnin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya auku a karfe 2:05 na rana a karamar hukumar Obio/Akpor, inda hanyar ta kasance cike da zirga-zirga sosai.
An ce lokacin da yake kokarin tsallaka titin, wata mota kirar SUV cikin sauri ta bugi mutumin, daga baya tirela ta murkushe shi har lahira.
Mutane sun tabbatar da lamarin a Rivers
Shaidu sun ce matashin na biye da wasu musulmai abokansa da suka nufi masallaci, amma bai lura da zirga-zirgar titi sosai ba.
Wani da ya shaida hadarin mai suna Tunde ya ce:
"Sauran masu ibada sun riga sun tsallaka, amma shi bai tsaya duba titi sosai ba."
Wani shaidan gani da ido ya kara tabbatar da lamarin inda ya ce abin bakin cikin ya faru yayin da mutumin ke gudu zuwa sallar Juma'a inda motar ta yi kaca-kaca da jikinsa.
Ya ce:
"Lokacin da SUV ta bugi mutumin, tirela da ke kan hanyar cikin gudu ta wuce ta kkansa, ta ragargaje jikinsa."

Source: Facebook
'Yan sanda sun kawo dauki bayan buge Musulmi
Bayan faruwar hatsarin, sauran musulman da suke tare da shi suka toshe hanya suna zanga-zanga, lamarin da ya jawo rudani sosai.
Lamarin ya fara girma duba da yadda ran mutane ya baci da wasu ke ganin akwai sakaci game da faruwar hakan kafin zuwan jami'an tsaro wurin.
Sai da jami’an ‘yan sanda suka iso wurin domin dawo da doka da oda, sannan musulman suka dauke gawar domin jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Mota ta bi kan masu sallar Juma'a a Kano
A baya, mun ba ku labarin cewa an shiga wani irin yanayi bayan wasu masallata sun rasa ransu suna tsaka da sallah a masallacin Juma'a bayan tirela ta hau kansu.
Lamarin ya faru ne a garin Imawa da ke karamar hukumar Kura a jihar Kano a ranar Juma'a 28 ga watan Yunin 2024 da ta gabata.
Hukumar kiyaye hadura ta kasa, FRSC ita ta tabbatar da haka inda ta ce akalla mutane 14 sun mutu sanadin hatsarin motar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
