Reno Omokri: Tinubu Ya Kawo Tsaro a Titin Abuja zuwa Kaduna da Ke Fama da 'Yan Ta'adda
- Reno Omokri ya bayyana cewa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi namijin kokari a hanyar Abuja-Kaduna bayan an shafe shekaru kan matsalar tsaro
- Tsohon mai taimakawa shugaban kasa ya ce ya yi tafiya a hanyar tare da jarumin Nollywood Wale Ojo da wasu ‘yan jarida ba tare da fargabar komai ba
- Reno Omokri ya bayyana cewa za a fara daukar fim ɗin ‘Lagos Heist’ a kan hanyar domin tabbatar da cewa an dawo da tsaro kamar yadda ya yi ikirari
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Tsohon mai taimakawa shugaban kasa, Reno Omokri, ya tabbatar cewa hanyar Abuja-Kaduna a mulkin Bola Ahmed Tinubu fiye da gwamnatin baya.
Omokri ya yi wannan magana ne a ranar Alhamis, 28 ga watan Agusta, lokacin da ya kai ziyara tare da jarumin fina-finan Nollywood, Wale Ojo, da kuma wasu ‘yan jarida yankin.

Kara karanta wannan
Borno: Mayakan boko haram sun yi wa matafiya kwantan bauna, sun bude wa motarsu wuta

Source: Facebook
A bidiyon da ya wallafa a Shafinsa na X, ya bayyana cewa manufar wannan ziyara ita ce nuna wa ‘yan Najeriya da sauran duniya cewa tsaro ya samu a hanyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Reno Omokri ya yabi aikin Bola Tinubu
Reno Omokri ya bayyana cewa aiki tukuru da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke yi a kan harkokin tsaro ya haifar da 'da mai ido a kan titin.
A cewarsa:
“Hanyar Abuja zuwa Kaduna tana da tsaro. A kowace kilomita akwai wuraren tsaro na sojoji. Ba wai kawai addu’a aka dogara da ita ba, gwamnati ta yi aiki a nan. Gwamnatin Tinubu ta yi abubuwa masu yawa a kan wannan hanya.”

Source: Facebook
Reno Omokri ya bayyana cewa ya gayyaci Wale Ojo zuwa wannan ziyara, kuma jarumin ya yanke shawarar ɗaukar wani ɓangare na fim dinsa mai suna Lagos Heist a wurin.
Dalilin Reno na ziyartar hanyar Kaduna-Abuja
A kalaman tsohon hadimin Shugaban Kasar, sun kai ziyarar ne domin a fito wa da duniya irin aikin da aka yi na kawar da 'yan ta'adda daga yankin.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi gaskiyar abin da ke kai shi kasashen waje bayan dawowa daga Brazil
Ya ce:
“A baya an tsara fim ɗin a yi shi a Las Vegas, amma na ce a yi shi nan Najeriya. Wale Ojo ya kawo tawagarsa mai mutum 100 domin ɗaukar hotuna."
Ya ƙara da cewa hanyar da ake gina yanzu tana da inganci saboda an yi amfani da ƙarafa da siminti mai ƙarfi, wanda zai iya ɗaukar shekaru 50 kafin ta lalace.
Omokri ya kuma jaddada cewa tafiyarsa ba tare da tsaro ba a kan hanyar ta zama shaida ga al’ummar Najeriya cewa an samu ci gaba.
Reno ya shawarci 'yan Arewa
A baya, mun wallafa cewa Tsohon mai taimaka wa shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya yi kira ga al’ummar Arewa da su mara wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu baya.
Tsohon hadimin ya kara da gargadin cewa Najeriya kasa ce mai rauni, don haka bai kamata a bar burin wasu ‘yan siyasa ya haddasa rikici ko rushewar zaman lafiya a ƙasar ba.
Omokri ya kafa hujja da cewa yankin Arewa na cin gajiyar ayyukan gwamnatin Bola Tinubu, saboda haka bai kamata su dakile burin shugaban kasa na sake neman wa’adi na biyu ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng