“Abinci, Kudin Haya, Sufuri Sun Yi Tsada,” NLC Ta Nemi Karin Albashi zuwa N150,000

“Abinci, Kudin Haya, Sufuri Sun Yi Tsada,” NLC Ta Nemi Karin Albashi zuwa N150,000

  • NLC ta bukaci gwamnan jihar Legas ya ƙara mafi ƙarancin albashin ma'aikata daga N85,000 zuwa N150,000 saboda tsadar rayuwa
  • Kiran ya biyo bayan sanarwar gwamnatin Imo na ƙara albashi zuwa N104,000 yayin da Ebonyi ma ta kara albashi zuwa N90,000
  • Kungiyar kwadago ta ce lokaci ya yi da ma’aikatan Legas za su samu karin albashi da zai dace da halin tattalin arziki a jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Kungiyar NLC, reshen Legas, ta bukaci Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ƙara mafi ƙarancin albashi daga N85,000 zuwa N150,000, bisa la’akari da tsadar rayuwa.

Shugabar NLC ta jihar, Hajiya Funmi Sesi ce ta yi wannan kira a ranar Alhamis yayin da take mayar da martani kan ƙarin albashin da gwamnatocin Imo da Ebonyi suka sanar kwanan nan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kutsa cikin gida, sun sace malamin addini kuma ma'aikacin asibiti

NLC ta bukaci gwamnan Legas ya kara albashin ma'aikata daga N85,000 zuwa N150,000
'Ya'yan kungiyar kwadago ta kasa (NLC) suna zanga-zanga a wani yanki na Najeriya. Hoto: @NLCHeadquarters
Source: Twitter

Ta bayyana cewa kudin haya, sufuri, abinci da sauran buƙatun yau da kullum sun fi tsada a Legas fiye da sauran jihohin ƙasar, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta bukaci karin albashi a Legas

A cewarta, ƙarin albashin da aka yi a jihohin Imo da Ebonyi ci gaba ne ga ma’aikata a Najeriya, kuma ya kamata sauran gwamnatoci su yi koyi da hakan.

Ta kara da cewa ma’aikatan Legas sun cancanci ingantaccen yanayin aiki da albashi da ya dace da halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.

“Lokaci ya yi da za a duba mafi ƙarancin albashi a Legas. Aƙalla an sami wasu gwamnoni da suka fara ɗaukar matakai irin wannan, fatanmu sauran gwamnoni su bi sahu.
"Ba za a zargi Gwamna Sanwo-Olu idan ya amince da mafi ƙarancin albashi mafi tsada a Legas ba, domin mu ma’aikata muna bukatar albashi da ya dace da rayuwar jihar."

Kara karanta wannan

"PDP na buƙatar ɗan takara Kirista daga Kudu,' Gwamna Bala ya yi magana kan 2027

- Hajiya Funmi Sesi.

NLC ta roki Legas ta bi sahun Imo & Ebonyi

Jaridar The Cable ta rahoto shugabar 'yan kwadagon ta ci gaba da cewa:

"Ba za mu iya jira ba har sai mun shiga tattaunawa da gwamnati domin samun walwala mai kyau ga ma’aikatan Legas, ina so gwamnati ta dauki mataki yanzu."
'Yan kwadago sun bukaci Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas da ya kara albashin ma'aikata zuwa N150,000
Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu yana jawabi a dakin taro na gidan gwamnati. Hoto: @jidesanwoolu
Source: Facebook

Kiran na zuwa ne, yayin da Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, a wannan makon ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi na N104,000 ga ma’aikatan jihar.

Ya sanar da haka ne a wani taro da shugabannin ƙwadago a fadar gwamnati, Owerri, a daren Talata. Zaman ya sa aka kara albashin daga N76,000 zuwa N104,000.

Da wannan, NLC reshen Legas ta nuna bukatar Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bi sahun wadannan jihohi wajen ƙara albashi domin dacewa da tsadar rayuwa a jihar.

An kara albashin ma'aikata a Ebonyi

Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Ebonyi ta sanar da ƙarin mafi ƙarancin albashi daga N70,000 zuwa N90,000 ga ma’aikatantan jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kara mafi karancin albashi, karamin ma'aikaci zai samu N90,000 duk wata

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Cif Ikeuwa Omebe, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai kan sakamakon zaman majalisar zartarwa ta jihar.

A cewar Omebe, sabon mafi karancin albashi na N90,000 zai fara aiki nan take kuma ya shafi dukkan rukunan ma’aikatan gwamnatin Ebonyi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com