Ministan Tinubu Ya Ware Jiha 1 a Najeriya, Zai Rabawa Mutane Naira Miliyan 500 Kyauta

Ministan Tinubu Ya Ware Jiha 1 a Najeriya, Zai Rabawa Mutane Naira Miliyan 500 Kyauta

  • Karaminin minista a gwamnatin tarayya ya ware Naira miliyan 500 daga aljihunsa domin tallafa wa masu kananan sana'o'i
  • Za a raba wannan tallafi ne ga kananan yan kasuwa da masu sana'o'in hannu a kananan hukumomi 18 na jihar Kuros Riba
  • Ministan, Sanata John Owan Enoh ya ce wannan tallafin kyauta ne ba rance ba, kuma ya yi haka ne domin taimakawa jama'arsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Cross River - Karamin Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Sanata John Owan Enoh, ya ƙaddamar da shirin raba tallafin Naira miliyan 500 ga mutanen Kuros Riba.

Ya ce za a raba wannan tallafi ne ga kananan yan kasuwa da masu sana'o'in hannu a fadin kananan hukumomin jihar.

Karamin ministan masana'antu, Sanata John Owan Enoh.
Hoton karamin ministan masana'antu, Sanata John Owan Enoh a wurin kaddamar da shirin tallafi a Kuroa Riba Hoto: Senator John Owan Enoh
Source: Facebook

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wani taron tattaunawa da ’yan jarida a cibiyar kungiyar NUJ da ke Kalaba, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Yadda N8,000 ta jawo asarar rai a kasuwar Legas

Ministan Tinubu zai raba N500m daga aljihunsa

Sanata Enoh ya ce wannan shiri ba na gwamnatin tarayya ko ta jiha ba ne, daga aljihunsa ya ciro kudin domin ƙarfafa gwiwar masu kananan kasuwanci na gargajiya da na zamani a Kuros Riba.

Ministan ya bayyana cewa wannan yunkuri ya samo asali ne daga ƙudurinsa na yiwa al'umma hidima ga al’umma tare da burin tallafa wa fiye da mutane 1,000 a matakin farko.

Ya ce za a ba yan kasuwa na zamani damar cike fam a yanar gizo yayin da masu sana'o'in hannu kamar makera, masu sayar da abinci sa sauransu, za a raba masu fam su cike.

Manufar kirkiro shirin tallafin ministan

“Wannan tallafi kyauta ne, ba rance ba. An tsara shi ne domin bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da taimakawa matasa da masu sana’a wajen gina rayuwarsu."
"Fatan mu shi ne wannan ƙoƙari da muka yi duk bai da yawa,, zai sa jama’armu su gane cewa ba dole sai sun jira aikin gwamnati ba.

Kara karanta wannan

An kama 'dan daban da ya fito da wani salo domin firgita Kano da makamai

-John Owan Enoh.

A nasa jawabin, ɗan gwagwarmaya kuma ɗan jarida Agba Jalingo, wanda ke cikin kwamitin aiwatarwa, ya tabbatar da cewa za a gudanar da shirin cikin gaskiya, in ji Punch.

Sanata John Owan Enoh da kwamitin aiwatar da shirin tallafinsa.
Hoton karamini minista, Sanata John Owan Enoh tare da kwamitin aiwatar da shirin tallafin da ya kirkiro Hoto: Senator John Owan Enoh
Source: Facebook

Yadda za a gudanar da shirin a Kuros Riba

Ya bayyana cewa za a gudanar da shirin ne a rukuni huɗu, inda kowane kashi zai dauki mutum 150 daga ɓangaren yan kasuwar zamani da 325 daga ɓangaren sana’o’in gargajiya a dukkan kananan hukumomi 18.

Ya ce kowanne mutum daya zai karɓi N100,000 zuwa N500,000 gwargwadon rukuninsa, bayan kammala horon sana’a na mako guda da za a shirya a kowace mazabar sanata.

"Wannan ba kuɗin gwamnati ba ne, minista ne ya ciro daga aljihunsa. Ba za a sace ko sisin kobo ba. Aikin mu shi ne tabbatar da cewa kowane kobo ya kai hannun wanda ya fi bukata,” in ji Jalingo.

Bola Tinubu zai tallafawa matasa miliyan 7

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana shirin horas da matasa miliyan bakwai a fannin fasahar zamani a fadin jihohin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kudin fansa: 'Yan bindiga sun dauke mutum 4700, an ji biliyoyin da aka rasa a shekara 1

A cewar gwamnatin, matasa suna taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban kasa kuma wajibi ne a ba su horon abubuwan zamani, dabi’u da tunani domin su ne shugabannin gobe.

Matasa miliyan uku daga ciki za su samu horo da gogewa a fannoni kamar fasahar AI, tsaro na yanar gizo da kuma kirkiro manhajar kwamfuta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262