Mazauna Katsina Sun Nema wa Kansu Mafita, Sun Kulla Yarjejeniya da 'Yan Ta'adda

Mazauna Katsina Sun Nema wa Kansu Mafita, Sun Kulla Yarjejeniya da 'Yan Ta'adda

  • Shugabannin al’ummar Kurfi sun nema wa kansu mafita a kan harin da ’yan bindiga a jihar Katsina ke kai masu
  • Fitattun shugabannin ’yan bindiga sun yi alƙawarin daina kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma satar shanu da su ka saba
  • Al’ummar Kurfi sun kulla yarjejeniya da 'yan bindiga da fatan a kawo karshen dauki daidai da 'yan ta'adda ke masu a yankin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Rahotanni sun tabbatar da cewa shugabannin al’umma a ƙaramar hukumar Kurfi ta jihar Katsina sun kulla yarjejeniya da ’yan bindiga da suka dade suna addabar yankin.

An ɗauki wannan mataki ne domin kawo ƙarshen shekaru na zubar da jini, satar shanu da kuma garkuwa da mutane.

An yi zaman sulhu da 'yan ta'adda a Katsina
Wasu mazauna garin Katsina (H), Shugabannin 'yan bindiga (D) a wani zama a Katsina @Dankatsina50
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta wallafa cewa majiyoyi sun tabbatar da cewa yarjejeniyar ta gudana ne a ranar Alhamis a dajin Wurma, ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin rashin tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

An kwashi gawar 'yan bindiga a buhu bayan sojoji sun kashe 'yan ta'adda 50

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Katsinawa sun tattauna da 'yan ta'adda

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi yarjejeniyar ta hannun Maradin Katsina kuma Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, tare da shugaban ƙaramar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi.

A jawabin sa, Hakimin, Alhaji Amadu Kurfi ya bayyana wannan mataki a matsayin sabon babi ga mutanen yankinsa, musamman ta fuskar zaman lafiya.

Ya bayyana cewa:

“Mun zaɓi zaman lafiya, kuma za mu kiyaye wannan amana don jin daɗin jama’armu."

Katsina: ’Yan bindiga sun yi alƙawarin daina ta’addanci

Alhaji Amadu Kurfi ya kuma roƙi shugabannin ’yan bindiga da su naɗa shugabannin gargajiya a tsakaninsu domin ƙara wa kansu martaba.

Fitattun shugabannin ’yan bindiga da suka haɗa da Usman Kachalla Ruga, Sani Muhindinge, Yahaya Sani wanda aka fi sani da Hayyu, da kuma Shu’aibu sun halarci zaman.

Sun baiwa jama'ar Kurfi tabbacin cewa sun dakatar da kashe-kashe, satar shanu da kuma garkuwa da mutane da su ke yi a yankin.

Kara karanta wannan

Ba dadi: 'Yan bindiga sun kashe mafarauta yayin artabu a Neja

Sun tabbatar da cewa daga yanzu, manoma za su iya komawa gonakinsu ba tare da tsoro ba kamar yadda ake fama da shi a baya.

Taswirar jihar Katsina
Taswirar jihar Katsina Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce:

“Daga yau mun zubar da makamanmu. Muna son zaman lafiya, kuma za mu saki mutanen da ke hannunmu."

Shugaban ƙaramar hukumar Kurfi, Hon. Abdullahi, ya bayyana farin ciki bisa wannan yarjejeniya, yana mai cewa hakan zai kara inganta zaman lafiya.

Ya kuma sanar da cewa makiyaya Fulani yanzu za su iya yin zirga-zirga da kasuwanci a Kurfi ba tare da tsangwama ba.

An zauna da 'yan ta'adda a Katsina

A baya, mun wallafa cewa 'yan siyasa da sarakuna sun zauna da 'yan bindiga a karamar hukumar Safana, jihar Katsina, inda suka kafa sharuɗɗa 20 na zaman lafiya.

Yarjejeniyar ta ba manoma damar shiga gonaki cikin kwanciyar hankali, yayin da Fulani za su iya zuwa kasuwa da asibiti ba tare da tsangwama ba daga mazauna yankin.

A karin hasken da ya yi, Malamin addinin Islama, Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya soki tattaunawar, ya ce Musulunci ya umarci a yi yaƙi da 'yan bindiga ba tare da bata lokaci ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng