2027: INEC Ta Fadi me ya sa Osun ta fi Kano, Jihohi 34 Yawan Rajistar Katin Zabe

2027: INEC Ta Fadi me ya sa Osun ta fi Kano, Jihohi 34 Yawan Rajistar Katin Zabe

  • Hukumar INEC ta ce babu abin mamaki a cikin alkaluman rajistar katin zabe da aka samu daga Osun, kamar yadda jam’iyyar ADC ta yi zargi
  • Kakakin shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ya ce tun a baya Osun ke kan gaba wajen yin rajista ta yanar gizo tun daga shekarar 2021
  • INEC ta ce dole ne duk masu yin rajista ta yanar gizo su je cibiyoyinta domin tabbatar da bayanansu tare da amfani da tsarin tantancewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar INEC ta mayar da martani kan zargin jam’iyyar ADC na cewa akwai abubuwan da ba su dace ba a cikin bayanan rijistar masu kada kuri’a ta yanar gizo.

ADC ta bayyana cewa alkaluman da aka samu daga jihar Osun sun saba wa tarihi da kuma halin al’ummar yankin, inda ta ce sama da mutum 390,000 sun yi rajista cikin mako guda.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Sarkin da ya 'kunyata' Najeriya a Amurka

Shugaban hukumar zabe ta kasa, Mahmud Yakubu
Shugaban hukumar zabe ta kasa, Mahmud Yakubu a ofis. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

The Cable ta rahoto cewa kakakin shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ya ce hakan ba sabon abu ba ne, domin a shekarun baya Osun ta sha yin zarra wajen rajistar masu kada kuri’a ta yanar gizo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

INEC ka kare kanta daga zargin ADC

Oyekanmi ya ce alkaluman da ADC ta kira da abin mamaki sun taba faruwa a baya, musamman a shekarar 2021 lokacin da aka fara rijistar CVR ta yanar gizo.

Rahoton Daily Post ya nuna cewa Oyekanmi ya ce tun daga kwanaki na farko, Osun ta kasance kan gaba.

Ya tuna cewa cikin kwanaki 24 na farko a 2021, sama da mutum 59,000 ne suka yi rajista a dandalin yanar gizo, inda Osun ta riga sauran jihohi da adadi mai yawa.

Har zuwa watan Satumban 2021, ya ce Osun ta kai kusan mutum 402,000 cikin sababbin masu rajista.

Oyekanmi ya ce hakan ya nuna cewa ba sabon abu ba ne idan Osun ta sake fitowa kan gaba a rijistar bana.

Kara karanta wannan

Kudin fansa: 'Yan bindiga sun dauke mutum 4700, an ji biliyoyin da aka rasa a shekara 1

INEC za ta tantance bayanan masu rajista

Hukumar INEC ta kara bayyana cewa duk wanda ya yi rajista ta yanar gizo, dole ne ya je cibiyar hukumar domin tabbatar da bayanansa da daukar hoto da bayanan yatsa.

Oyekanmi ya ce hukumar INEC tana amfani da tsarin ABIS domin gano masu yin rajista fiye da sau daya.

Ya kara da cewa wannan tsari ne da ya taimaka wajen tabbatar da ingancin kundin zabe a shekarun baya.

Kakakin jami'yyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi
Kakakin jami'yyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Zargin da jam'iyyar ADC ta yi wa INEC

ADC ta bayyana mamakinta ne ganin yadda Osun kadai ta samu rajistar mutane sama da 393,000 a mako guda, yayin da gaba daya yankin Kudu maso Yamma ya tara 67% na rajistar da aka yi.

Kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya ce wannan ba al’ada ba ce ta yankin, yana mai kira da a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Ya ce abin mamaki ne ganin cewa jihohi biyar na Arewa maso Gabas ba su wuce 6% na masu rajista ba, yayin da wasu jihohi kamar Ebonyi, Enugu da Adamawa suka samu adadi kadan sosai.

Kara karanta wannan

2027: Jihohin Kudu na jan ragamar rajistar katin zabe, na Arewa sun biyo baya

CAN ta bukaci a yanki katin zabe

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN reshen Arewa ta bukaci a yanki katin zabe da INEC ta fara rajista.

Rahotanni sun nuna cewa kungiyar CAN ta ce katin na da matukar muhimmanci ga 'yan kasa wajen zaben shugabanni.

CAN ta yi kira ga dukkan 'yan Najeriya da su nisanci sayar da katin zabensu ga 'yan siyasa, domin shi ne yancinsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng