Tirkashi: Sanata Ya Maka Gwamnan Kaduna a Kotun Duniya, Yana So a Cafke Uba Sani

Tirkashi: Sanata Ya Maka Gwamnan Kaduna a Kotun Duniya, Yana So a Cafke Uba Sani

  • Gwamnan Kaduna, Uba Sani, na fuskantar kamu daga kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya (ICC) kan "cin zarafin ‘yan adawa"
  • Sanata Lawal Usman ne ya maka Uba Sani a kotun ICC, inda yake zargin gwannan da sa EFCC su cafke jami'ai da 'yar takarar PDP
  • Yayin da Sanata Usman ya zargi gwamnan da murkushe 'yan adawa a Kaduna, ya ce ayyukan sun ba da Dokar Rome Statute

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Lawal Adamu Usman, ya shigar da karar gwamnan Kaduna gaban kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya (ICC) da ke Hague.

Sanata Lawal Usman ya bukaci kotun ICC ta bayar da sammacin kama Gwamna Uba Sani bisa zargin aikata laifuffuka kan ‘yan adawar siyasa a jihar.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Ana zargin Sanata ya yi barazanar 'kashe' gwamnan Kaduna

Sanata Lawal Usman ya maka Uba Sani a kotun ICC, inda ya bukaci a cafke gamnan kan cin zarafin 'yan adawa.
Hoton Gwamna Uba Sani ya na jawabi a Kaduna, da Sanata Lawal Adamu a ginin majalisar datawa, Abuja, da kotun ICC. Hoto: @IntlCrimCourt, @ubasanius, @mrla7411
Source: Twitter

Sanata ya kai Uba Sani kotun duniya

'Dan majalisar dattawan ya wallafa takardar korafin da ya shigar kotun ICC a shafinsa na X a ranar Alhamis, 28 ga watan Agusta, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan mataki ya biyo bayan cafke ‘yar takarar PDP a zaben cike gurbi na Chikun/Kajuru da aka gudanar a ranar 16 ga Agusta.

An ce hukumar EFCC ce ta cafke 'yar takarar, Princess Esther Asheu Velli Dawaki, da kuma daraktan yakin neman zaben jam’iyyar, Alhaji Shehu Aliyu Patange.

Sanata Usman, a cikin takardar korafin mai dauke da kwanan wata 26 ga Agusta, 2025, ya ce ya na wakiltar ‘yar takarar PDP da har yanzu ake tsare da ita bisa umarnin Gwamna Uba Sani ba bisa ka’ida ba.

Ya bayyana cewa, a safiyar ranar zaben, jami’an tsaro dauke da makamai sun mamaye masaukin ‘yan jam’iyyar PDP, inda suka kama ‘yar takarar da wasu shugabannin jam’iyyar tare da kwace masu sama da Naira miliyan 26 da aka tanada don ayyukan zabe.

Kara karanta wannan

Harin masallaci: Gwamna Radda ya ziyarci kauyen Mantau, ya dauki alkawura

Ana zargin Uba Sani da murkushe 'yan adawa

A cewar korafin, sama da manyan PDP 25 ciki har da sakataren jam’iyya na jiha, shugaban yakin neman zabe, shugabannin mata da wani dan majalisar jiha aka cafke, domin tsoratar da ‘yan adawa da kuma karkatar da sakamakon zabe.

Sanatan ya ce wannan mataki ya sabawa yarjejeniyar zaman lafiya da jam’iyyu suka rattabawa hannu a jihar, kuma ya zamo zalunci da take hakkin siyasa.

Haka kuma, ya zargi Gwamna Uba Sani da yin amfani da karfin gwamnati ta hanyar karkatar da ayyukan rundunar ‘yan sanda, DSS da EFCC domin “durkusar da ‘yan adawa da hana cikakkiyar dimokuradiyya a Kaduna.”

Sanata ya bukaci ICC ta cafke Uba Sani

Sanata Usman ya yi nuni da cewa, bisa ga Sashe na 7 na Dokar Rome Statute, wadannan kame-kamen da tsare tsare sun shiga cikin nau’in “laifuffukan yaƙar ɗan adam,” musamman azabtar da jama’a ta fuskar siyasa.

Sanata Sanata Lawal Usman ya zargi gwamnan Kaduna, Uba Sani da sa jami'an tsaro su cafke jami'ai da 'yar takarar PDP
Sanata Sanata Lawal Usman a ofishinsa da ke majalisar datttawa. Hoto: @mrla7411
Source: Twitter

Ya bukaci kotun ICC ta fara bincike, sannan ta bayar da umarnin cafke Gwamna Sani domin hana sake amfani da karfin gwamnati wajen tauye ‘yancin ‘yan adawa a jihar.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Sarkin da ya 'kunyata' Najeriya a Amurka

Wani bangare na korafin sanatan ya ce:

“Gwamnan Kaduna ne ke da alhaki na kai tsaye a kan wadannan laifuffuka, domin hukumomin tsaro da na binciken cin hanci sun yi aiki ne a karkashin umarninsa."

Ya tabbatar da wannan korafi a karkashin rantsuwa, tare da mika shaidu, rahotannin kafafen yada labarai da wasu hujjoji da ke danganta Gwamna Uba Sani da matakan murkushe ‘yan adawa a lokacin zaben cike gurbi.

Ana zargin Sanata zai kashe Uba Sani

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan sanda sun gayyaci Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Lawal Usman bisa zargin yi wa Gwamna Uba Sani barazana.

Hakan ya biyo bayan korafin da Gwamna Uba Sani ya shigar gaban yan sanda, yana zargin sanatan da yunkurin tayar da tarzoma a Kaduna.

Kwamishinan yan sanda ya gayyaci Sanata Lawal Adamu, wanda aka fi sani da LA domin amsa tambayoyi ranar 1 ga watan Satumba, 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com