NiMet: Za a Sheka Ruwan Sama a Kano, Neja da Wasu Jihohin Arewa 14 Ranar Juma'a
- Kano, Kebbi, Neja da wasu jihohi a Arewa 13 za su sha ruwan sama da tsawa a ranar Juma'a, 29 ga Agusta, 2025, a cewar NiMet
- Hukumar hasashen yanayin ta kasa, ta ruwaito cewa da yawan jihohin Arewa za su samu ruwan sama tun daga safe har dare
- Bugu da ƙari, NiMet ta yi kira ga al’ummomi da ke zaune a yankunan da ambaliya ke yawan faruwa da su kasance cikin shiri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama hade da tsawa a wasu jihohin Najeriya a ranar Juma’a, 29 ga watan Agusta, 2025.
Rahoton da hukumar ta saki a ranar Alhamis, 28 ga watan Agusta, ya shafi yanayin da ake hasashen faruwarsa daga ƙarfe 00:00 zuwa 23:59 na ranar Juma'a.

Source: Original
Ruwan sama da tsawa a yankunan Arewa
A cewar rahoton da NiMet ta fitar a shafinta na X, sassan Arewacin Najeriya za su fuskanci ruwan sama mai yawa a ranar Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da safe, ana sa ran ruwan sama mai matsakaicin karfi amma tare da tsawa a jihohin Gombe, Bauchi, Adamawa da Taraba.
Bayan haka kuma, da yamma zuwa dare, ana sa ran karin ruwan sama da tsawa a Kano, Kaduna, Kebbi, Katsina, Gombe, Bauchi, Adamawa, Yobe, Taraba da Borno.
Hasashen yanayi a Arewa ta Tsakiya
A Arewa ta Tsakiya kuwa, hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama kadan a wasu sassan yankin.
Da safe, ana sa ran ruwan sama a wasu bangarorin babban birnin tarayya Abuja, jihohin Neja Benue, Kogi, Nasarawa da Filato.
Bayan haka, da yammaci zuwa dare, ruwan sama kadan zai ci gaba da suka a Abuja da wasu sassan jihohin Nasarawa, Benue, Kwara, Neja da kuma Filato.
Za a yi ruwan sama kadan a Kudu
A safiyar Juma'a, hukumar NiMet ta yi hasashen saukar ruwan sama kadan a Cross River da Akwa Ibom.
Bayan haka kuma, daga yamma zuwa dare, ana sa ran ruwan sama na gajeren lokaci zai sauka a Ondo, Edo, Abia, Imo, Oyo, Anambra, Enugu, Ogun, Cross River, Akwa Ibom, Delta da Bayelsa.

Source: Twitter
NiMet ta gargadi jama’a
NiMet ta shawarci jama’a su dauki matakan kariya, musamman saboda yiwuwar saukar ruwan sama da iska mai karfi da zai iya kai jawo asarar rayuka da dukiya.
Hukumar ta kuma ja hankalin masu ababen hawa da su kula yayin tuki saboda hanyoyi na iya yin sulbi a lokacin ruwan sama, wanda hakan zai iya jawo hadurra.
Bugu da ƙari, NiMet ta yi kira ga al’ummomi da ke zaune a yankunan da ambaliya ke yawan faruwa da su kasance cikin shiri.
Rahoton ya nuna kokarin NiMet na ci gaba da samar da bayanan yanayi cikin lokaci ga ’yan Najeriya domin taimaka musu wajen shiryawa da kare kansu daga kalubalen yanayi.
Ambaliya za ta shafi yankuna 14
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta fitar da gargadi cewa jihohi tara da yankuna 14 a Arewa na iya fuskantar ambaliya.
Cibiyar gargadi kan ambaliya ta ce ambaliyar na iya faruwa tsakanin 25 zuwa 29 ga Agustan 2025, inda aka gargadi mazauna yankunan gabar kogin Jebba zuwa Lokoja.
Jihohin da abin zai shafa sun hada da Adamawa, Borno, Gombe, Kano, Katsina, Sokoto da Zamfara, inda aka bayyana kauyuka da dama cikin hatsarin ambaliya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


