Ta Faru Ta Kare, ASUU Za Ta Tsunduma Yajin Aiki, Ta Aika Sako ga Dalibai da Iyaye
- Kungiyar ASUU ta shirya yajin aiki a duk fadin Najeriya, inda ta gargadi dalibai da iyaye kan tsaikon karatu da za a iya fuskanta
- ASUU ta zargi gwamnatin tarayya da kin aiwatar da yarjejeniyar 2009, tana mai cewa gwamnati ce abar zargi idan ilimi ya tabarbare
- Wannan na zuwa ne yayin da ministan ilimi ya musanta sanya hannu kan wata yarjejeniya da ASUU, lamarin da ka iya tunzura kungiyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya (ASUU) ta kammala shirin shiga yajin aikin sai baba ta gani, wanda zai shafi dukkanin Najeriya.
Kungiyar ASUU ta aika muhimmin sako ga iyaye da dalibai, cewar yaji aikin zai jawo babban tsaiko ga karatu a jami'o'in kasar.

Source: Twitter
KungiyarASUU za ta tsunduma yajin aiki
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa kungiyar ta nuna fushinta sosai kan gazawar gwamnatin tarayya ta mutunta yarjejeniyar da aka yi da ita a 2009.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ASUU ta bukaci 'yan Najeriya da ka da su ga laifinsu a abin da zai faru, su tuhumi gwamnatin tarayya idan har ilimi ya lalace a nan gaba.
Kungiyar dai ba ta bayyana ranar da za ta shiga wannan babban yajin aikin ba, amma hankulan dalibai sun tashi game da makomar karatunsu.
'Mun shirya yajin aiki mafi muni' - ASUU
Tun da fari, jaridar Vanguard ta rahoto cewa ASUU ta yi barazanar tsunduma yajin aikin da ta kira da "uwar dukkanin yajin aiki" idan gwamnati ta ki biyan bukatunta.
Shugaban ASUU na reshen jami'ar Calabar (ASUU-UCB), Dr. Peter Ubi, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a sakatariyar kungiyar.
Dr. Peter Ubi ya ce kungiyar ta ba gwamnatin tarayya wa'adin karshe, zuwa yau (Alhamis, 28 ga Agusta) ta biya bukatun kungiyar.

Source: Twitter
Kalaman gwamnati na iya fusata ASUU
Wannan matsaya ta ASUU na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayya ta fito karara ta ce, ita ba ta taba rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ASUU ba.
A ranar Alhamis, This Day ta rahoto ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa ya ce kungiyar ASUU na ta hankoro kan wata yarjejeniya da ba ta taba wanzuwa ba tsakaninta da gwamnati.
Ya ce sabanin abin da ASUU ke fadawa 'yan Najeriya, gwamnati ba ta sanya hannu kan yarjejeniya da kungiyar ba, kuma takardun da ASUU ke gabatar wa, daftarin tattaunawa ne kawai ba yarjejeniya ba.
Sai dai, wasu na ganin cewa, kalaman ministan na ranar Alhamis, na iya tunzura ASUU su tsunduma yajin aikin da ba a san ranar janyewarsa ba, kamar yadda suka yi a shekarar 2020, inda aka shafe watanni kusan tara babu karatu.
Malaman jami'a sun fara zanga-zanga
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar ASUU ta gudanar da zanga-zanga a yau Talata 26 ga watan Agusta, 2025 a dukkan jami’o’in kasar nan.
Malaman jami'ar sun ce zanga zangar alama ce ta nuna rashin jin daɗinsu bisa sakacin gwamnati wajen aiwatar da bukatun su na dogon lokaci.
ASUU ta jaddada cewa tilas gwamnati ta mutunta yarjejeniyar 2009 da sauran alƙawura idan ana son kaucewa sake fadawa cikin yajin aiki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

