Nafisa: Bayan Korafi, Gwamnatin Tarayya Ta Karrama Dalibar Yobe da Kyautar Kudi
- Gwamnatin Tarayya ta gudanar da liyafa ta musamman ga daliba daga jihar Yobe, Nafisa Abdullahi wacce ta lashe gasa ta duniya
- Nafisa ita ce yarinya ‘yar Yobe da ta lashe gasar 'TeenEagle' a London da ke kasar Birtaniya a Nahiyar Turai
- Tun bayan sanar da nasarar dalibar, an yi ta kiran Bola Tinubu ya karrama ta kamar sauran yan wasan ƙwallon kafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Bayan korafe-korafe zuwa ga gwamnatin tarayya kan karrama Nafisa Abdullahi, an ba ta kyauta.
Gwamnatin Tarayya, a ranar Alhamis 28 ga watan Agustan 2025 ta karrama dalibar daga jihar Yobe.

Source: UGC
Rahoton Punch ya ce ma'aikatar ilimi ta ba Nafisa Abdullahi, yarinya ‘yar shekara 17 daga Yobe kyautar N200, 000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya karrama daliban jihar Yobe

Kara karanta wannan
'Yar Najeriya, Hajara Yakubu ta doke yan kasashe da dama, ta samu kyaututtuka a India
Tun da farko, Gidauniyar Atiku Abubakar ta riga ta bai wa Nafisa, Rukaiya Fema da Khadija Kalli cikakkiyar tallafin karatu saboda nasarorin da suka samu a gasar.
‘Yan matan sun fito a matsayin zakaru na duniya a fannoni daban-daban na gasa mai daraja, inda gidauniyar ta yaba musu bisa abin da ta kira gagarumar nasara.
Nafisa ta wakilci Najeriya ta hanyar Makarantar Nigerian Tulip International College, inda ta doke sama da mahalarta 20,000 daga kasashe 69 a gasar.
Gasar 'TeenEagle' wata gasa ce ta duniya wacce ke tantance iyawa a harshen Turanci, tunani mai zurfi da kuma basirar sadarwa tsakanin matasa.
Gwamnatin tarayya ta karrama Nafisa Abdullahi
A wani biki na musamman a Abuja, Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa tare da karamar minista, Farfesa Suwaiba Ahmad, sun taya Nafisa murna bisa wannan babbar nasara.
Sun bayyana ta a matsayin abin koyi ga matasan Najeriya saboda yadda ta nuna cewa Najeriya na da matasa masu fasaha da hazaka.

Source: Facebook
Ma'aikatar ilimi ta sha alwashi gyara ilimi
Da yake jawabi, Alausa ya ce gwamnati na daukar wasu matakai domin inganta ilimi da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
“Ina gaya muku, ku ne makomar Najeriya, kuma kun saka mu alfahari, shugaba Tinubu na goyon bayan ilimi fiye da duk wani lokaci a tarihinmu.
“Kowane lokaci da muka nemi tallafi daga gare shi a fannin ilimi, amsarsa ita ce ‘eh’, domin ya yarda da ku, yaran Najeriya.”
- Cewar Alausa
Ministan ya kuma sanar da bai wa Nafisa da sauran dalibai da suka yi fice a sauran fannoni kyautar fiye da N100,000, Aminiya ta tabbatar da labarin.
Abin da Nafisa ta fada game da Tinubu
A jawabinta, Nafisa ta gode wa Tinubu da ministoci saboda samar da yanayi da ya ba ta damar yin fice, tare da godewa makarantar da iyayenta.
Kwamishinan Ilimi a Yobe, Farfesa Abba Idris, ya gode wa ministoci bisa wannan karamci, yana mai cewa gwamnati na ci gaba da murna da irin wannan nasarori.
Teen Eagle: 'Dan kasuwa ya karrama 'Yan Yobe
Kun ji cewa dan kasuwa, Alhaji Kashim Tumsah ya shiga jerin wadanda suka karrama daliban jihar Yobe da suka fito da Najeriya a idon duniya.
Tumsah, wanda ya yi fice a rajin kawo ci gaba ya ba su kyautar N1.5m da kwamfutoci, domin yabawa da irin bajintar da su ka yi.
Ya danganta nasarar da ƙoƙarin gwamnatin Yobe a fannin ilimi, yana mai cewa Gwamna Mai Mala Buni yana kokari sosai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

