Duniya Labari: Tsohon Shugaban Hukumar Kwastam, kuma Sardaunan Adamawa Ya Rasu
- Najeriya ta yi babban rashi, an sanar da mutuwar tsohon shugaban hukumar Kwastam wnada ya rasu a yau Alhamis
- An tabbatar da cewa Ahmed Aliyu Mustapha, ya rasu ranar Alhamis 28 ga watan Agustan 2025 da muke ciki
- Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya bayyana haka, inda ya yi jimamin rasuwar marigayin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yola, Adamawa - Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya sanar da rasuwar tsohon shugaban hukumar kwastam.
Gwamna Fintiri ya yi jimamin mutuwar inda ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da yan uwansa.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da gwamna Ahmadu Fintiri ya wallafa a shafin Facebook a yau Alhamis 28 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mukaman da marigayi Ahmad Aliyu ya rike
Ahmad Aliyu Mustapha ya yi ritaya daga hukumar kwastam a watan Disambar 2003 bayan ya yi hidimar sama da shekaru 30.
Marigayin babban ɗan’uwan Lamidon Adamawa ne, Dakta Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha da ke sarauta.
Har ila yau, marigayin yana rike da sarautar gargajiya ta Sardaunan Adamawa da ke Arewa maso Gabas a Najeriya kafin rasuwarsa.
Tsohon shugaban Kwastam ya fara aikinsa a matsayin karamin ma'aikaci a hukumar Kwastam da ke kula daya daga cikin hukumomin masu samar da kudin shiga ga gwamnatin tarayya.
Sannan ya rika taka wasu matsayi har zuwa zama shugaban hukumar a farkon jamhuriya ta hudu.

Source: Facebook
Fintiri ya sanar da rasuwar tsohon shugaban kwastam
Gwamna Fintiri ya ce tsohon shugaban hukumar kwastam ta Najeriya (NCS), Ahmed Aliyu Mustapha, ya rasu a yau Alhamis.
Mustapha wanda ya jagoranci hukumar tsakanin 1999 zuwa 2003, ya rasu ne ranar Alhamis, kamar yadda gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya tabbatar.
Sanarwar ta ce:
“Na yi matuƙar bakin cikin rasuwar Alhaji Ahmed Aliyu Mustapha, tsohon shugaban hukumar Kwastam a Najeriya.
"Mutum ne mai hidima, mutunci da jajircewa, wanda gadayyukan alherinsa za su ci gaba da wanzuwa.
"Addu’ata tana tare da Lamido Adamawa, dangin Mustaphada duk masu jimami.
"Allah ya jikan shi da Aljannah Firdaus."
Masu amfani da kafofin sadarwa musamman Facebook sun yi martani game da rasuwar Sardaunan Adamawa wanda Gwamna Fintiri ya tabbatar.
Mafi yawan wadanda suka yi martani sun yi masa fatan alheri da addu'o'i tare da rokon ubangiji ya saka masa da gidan aljanna firdausi.
Comr Jirbrill H Pella:
"Ina fatan Allah ya yafe masa kura-kuransa, ya gafarta masa, saka masa da gidan aljannar firdausi."
Abdullah Buba Lokuw:
"Allahu Akbar, ubangiji ya jikansa (RIP)."
Solomon S. Oaya:
"Ubangiji ya jikansa yallabai."
Tsohon gwamna daga Adamawa ya rasu
Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamna kuma Sanata da ya yi mulkin soja a jihar Plateau da ke Arewacin Najeriya ya riga mu gidan gaskiya.
Tsohon gwamnan soja na Plateau kuma Sanata da ya wakilci Adamawa ta Arewa, Kanal Muhammad Mana, ya bar duniya a Abuja ranar Juma’a 22 ga watan Agustan 2025.
Ɗan uwansa, Sarkin Fulani na Mubi, Abdurrahman B. Kwaccham, ya tabbatar da rasuwar, ya bayyana cewa marigayin ya bar mata da ’ya’ya da dama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

