Daga Kudu zuwa Arewa: Yadda Matatar Dangote Take Sauya Tattalin Arzikin Najeriya

Daga Kudu zuwa Arewa: Yadda Matatar Dangote Take Sauya Tattalin Arzikin Najeriya

  • A wani lokaci da man fetur ya yi tsada matuka, jama’a suka fara shakku kan makomar tattalin arziki, sai ga matatar man Dangote
  • Najeriya ta shafe shekaru tana shigo da mai daga waje, amma zuwan Dangote, ƙasar ta zama babbar mai fitar da mai a Afrika
  • A wannan rahoto, Legit Hausa ta yi bayani dalla dalla game da tasirin matatar Dangote ga Arewa da Kudu, da kalubalen da ake fuskanta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Babbar matatar mai mafi girma a nahiyar Afirka, watau matatar Dangote, ta zama ginshikin Najeriya na kawar da dogaro da shigo da man fetur.

Tun bayan kaddamar da ita a shekarar 2023, wannan matata, mai tace ganga dubu 650 a kowace rana ta fara sauya yanayin tattalin arzikin Najeriya.

Matatar Dangote ta taimaka wajen bunkasa tattali, samar da ayyuka da rage tsadar mai a Najeriya
Alhaji Aliko Dangote, da matatar Dangote da ke a birnin Legas. Hoto: Bloomberg/Getty Images
Source: Getty Images

Sauyin da matatar Dangote ta kawo

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Sarkin da ya 'kunyata' Najeriya a Amurka

Matatar ta rage farashin fetur, ta samar da ayyukan yi, ta kuma ba da damar bunkasar masana’antu da noman kasar, kamar yadda rahoton The Economic Summit.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Agusta 2025, bayan shekaru biyu da fara aikin matatar, aka fara ganin babban canji a farashin man fetur, inda Dangote ya sauke lita zuwa N820, sannan NNPCL da 'yan kasuwa suka sauke nasu zuwa N865 da N890.

Wannan sauyin ya kawo sauki ga al’umma da ke fama da hauhawar farashin kaya da ya kai kashi 34.19%, tare da hauhawar abinci da ya kai kashi 40% a shekarar 2024, kamar yadda NBS ta ruwaito.

Tasirin wannan matatar ya ratsa daga Kudu zuwa Arewa, daga mai kudi zuwa talaka, kuma ko ina na amfanuwa da matatar a kusan kowace rana.

Duk da tasirin matatar Dangote, akwai kalubale da suka lullube tasirin da kuma tattalin arzikin kasar, ciki har da rashin daidaito tsakanin yankuna.

Wannan rahoton na musamman ya zakulo yadda matatar Dangote ke sauya tattalin arzikin Najeriya, inda muka bayyana damar da ke akwai, kalubale da kuma hanyoyin da za a bi domin tabbatar da cewa kowane dan Najeriya ya amfana da matatar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya samu gagarumin goyon baya, ana so ya nemi takarar shugaban kasa a 2027

Sabon babi na tattalin arzikin Najeriya

Na tsawon shekaru da dama, Najeriya ce babbar mai fitar da danyen mai a Afirka, amma duk da haka ta dogara da shigo da man fetur daga kasashen waje.

A kowace shekara, kasar ta na kashe kusan dala biliyan 7 wajen shigo da mai, abin da ya yi ta raunana tattalin arziki da rage kudaden musayar kasashen waje, inji rahoton Arise News.

Cire tallafin mai a 2023 ya haifar da tashin farashin man fetur, inda lita ta haura N950, ya kuma kara tsananta radadin talauci da rashin aikin yi a kasar.

Wani bincike Research Gate ya nuna cewa a waccan shekarar, kashi 33.1% na matasa ba su da aikin yi, yayin da fiye da mutane miliyan 104 suka shiga cikin kangin talauci.

Sai dai matatar Dangote mai darajar dala biliyan 19 ta kawo sabon sauyi. Tace mai a gida ya rage bukatar shigo da man waje, ya tabbatar da wadatar man fetur, ya kuma saukar da farashi.

Kara karanta wannan

Kudin fansa: 'Yan bindiga sun dauke mutum 4700, an ji biliyoyin da aka rasa a shekara 1

A watan Agusta 2025, farashin fetur ya sauka zuwa N820 a matatar, yayin da ake sayar da lita kan N875 a Legas da N905 a Maiduguri. Wannan ya ba da damar saukin kudin sufuri, saukin noma, da kuma bunkasar masana’antu a fadin kasa.

Tasirin matatar bai tsaya kan rage tsadar mai a gida ba, har ma da ba Najeriya damar zama mai fitar da man fetur, da kuma yiwuwar kara GDP na kasar zuwa tsakanin dala biliyan 188.27 zuwa 193.39 a shekarar 2025.

Daga cikin tasirin matatar Dangote akwai rage farashin man fetur zuwa kasa da N900
Hoton wani bangare na matatar man Dangote, da wani ma'aikaci yana sayar da man fetur. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tasirin matatar Dangote ga Najeriya

  • Samar da fetur mai rahusa

Babban tasirin farko na matatar Dangote shi ne rage farashin mai. A watan Agusta 2025, farashin lita daya na mai ya koma tsakanin N875 da N905, wanda ya kawo sauki a rayuwar mutane musamman a lokacin da abinci ya yi tsada sosai.

A Legas, jiha mafi cunkuso, ma’aikatan ofis sun ga ragin kudin mota, abin da ya ba su damar adana kudi don yin sauran bukatu na rayuwar yau da kullum.

A Arewa, manoma kamar Awwalu Bala daga Daudawa, jihar Katsina, sun samu damar amfani da fetur mai rahusa don huda, haro da ban ruwa a gonakinsu, abin da zai taimaka wajen karuwar amfanin gona.

Kara karanta wannan

2027: Jihohin Kudu na jan ragamar rajistar katin zabe, na Arewa sun biyo baya

Awwalu Bala, ya shaida wa Legit Hausa cewa:

"An samu saukin fetur gaskiya, ba kamar shekarar bara ba. A bara, sai dai muka rika amfani da shanu wajen huda da haro, amma bana, mun yi amfani da tantan.
"Mu matsalarmu yanzu ta 'yan bindiga ce, domin ba ma iya noman masara, dawa da duk wani abu mai duhu a garinmu, dole sai wake, gyada, shinkafa."

Game da tasirin matatar Dangote, Awwalu ya ce:

"Toh, ka san mu nan muna karkara, ba za mu san wadannan labaran ba, amma dai tabbas an samu saukin mai, kuma muna godiya ga Dangote, idan shi ne dalilin faruwar hakan."
  • Samar da ayyukan yi

Matatar Dangote ta samar da ayyuka kai tsaye har dubu 40 ga ’yan Najeriya, tare da dubban ayyukan da ba na kai tsaye ba a bangaren jigila, dillanci, da sauran sana’o’i.

Masana sun yi hasashen cewa nan da 2026, matatar za ta haifar da akalla ayyuka dubu 100 ta hanyar ayyukan da ba na kai tsaye ba, wanda zai taimaka a rage rashin aikin yi da kashi 33.1.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ambaliyar ruwa ta shiga gidaje 4521 a jihar Yobe, an rasa rayuka

  • Taimakon masana’antu da noma

Daga Kudu zuwa Arewacin Najeriya, matatar Dangote ta taimaka wa wajen bunkasar masana'antu, saboda tana sayar da fetur da dizal mai rahusa.

Manoma a Kano da Jigawa, Katsina da sauran jihohi suna amfani da fetur da dizal don ban ruwa da noman shinkafa da alkama da sauransu.

Ta fuskoki da dama, matatar Dangote ta taimaka wa fannonin fasahar kasar nan, wanda ya sanya ake samun wasu abubuwan da araha.

  • Dogaro da kai

Matattarar Dangote ta kawo karshen dogaro da shigo da man fetur daga waje, abin da ya ceci Najeriya daga asarar biliyoyin daloli.

Wannan nasara ta haifar da alfahari ga ’yan kasa daga Arewa zuwa Kudu, inda suke kallonta a matsayin wata alama ta dogaro da kai.

Rahoton ThisDay ya nuna cewa, fitar da mai zuwa kasashen makwabta a Yammacin Afirka na kara daukaka matsayin Najeriya a matsayin jagora a fannin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

INEC: Abubuwan sani game da rijistar zabe da aka fara a kananan hukumomi 774

Dangote ya kawo sababbin motocin dakon mai, wanda hakan zai samar da karin ayyukan yi.
Alhaji Aliko Dangote, da sababbin motocin dakon man fetur da matatar Dangote ta shigo da su Najeriya. Hoto: Bloomberg/Contributor
Source: Getty Images

Kalubalen da ake fuskanta

  • Rashin daidaito tsakanin yankuna

Duk da cewa matatar ta kawo sauyi, ba kowa ke amfana da wannan sauyin dai dai wadai da ba.

Yankunan kudu kamar Legas da Rivers sun fi cin gajiyar matatar saboda sun fi kusanci da ita da kuma ingantaccen tsarin hanyoyi da rumbunan ajiya.

A Arewa, musamman Arewa maso Gabas kuwa, rashin isassun rumbunan ajiyar mai da matsalolin hanyoyi sun sa farashin ya fi tsada.

  • Hadarin tashin farashi

Ko da yake farashin mai ya sauka a 2025, akwai hadarin tashin farashi saboda sauyin kasuwar mai ta duniya da kuma faduwar darajar Naira.

Duk da wannan, har yanzu farashin fetur a Najeriya ya fi na kasashen da ke da arzikin mai sauki, irin su Libiya da Angola tsada.

  • Matsalar samun aiki

Yawancin ayyukan kai tsaye na matatar suna a Legas, abin da ke tilasta matasa daga Arewa da wasu jihohin Kudu yin hijira zuwa can domin samun aiki.

Kara karanta wannan

Kano: Jami'an NDLEA sun cafke matashi da tramadol 7,000 daga Legas

  • Gibin kayayyakin more rayuwa

Tsohon tsarin bututun mai da rashin isassun rumbunan ajiya suna rage saukin rarraba mai musamman a yankunan karkara.

A Arewa maso gabas, matsalar tsaro da ta’addanci tana kawo tsaiko ga jigilar mai, yayin da a gabas, matsalolin hanyoyi ke jinkirta isar da man.

  • Tsoron sauyin makamashi

A duniya ana ci gaba da komawa ga makamashin zamani mai tsafta. Idan Najeriya ta ci gaba da mayar da hankali ga mai kadai, akwai yiwuwar ta makale a tsohon tsarin tattalin arziki, yayin da sauran kasashe suka ci gaba da amfani da makamashin da ke dorewa.

Saboda zuwan matatar man Dangote, Najeriya ta daina dogaro da shigo da fetur daga kasashen waje.
Alhaji Aliko Dangote, shugaban rukunonin kamfanonin Dangote. Hoto: Bloomberg/Getty Images
Source: UGC

Hanyoyin magance matsalolin

  • Karfafa matasa da kananan kasuwanci

Ana bukatar kaddamar da shirye-shiryen horar da matasa a bangaren mai da gas, jigila da kuma harkokin noma.

Haka kuma, a samar da rancen tallafi ga kananan ’yan kasuwa a kasuwannin Onitsha, Kano, Ibadan da sauransu, don su ci gajiyar ragin kudin mai.

  • Zuba jari a kayayyakin more rayuwa

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An gano yadda ake amfani da siyasa wajen zafafa hare hare a Najeriya

A kara zuba jari a hanyoyi da bututun mai musamman a Arewacin Najeriya, domin rage gibin da ke tsakanin yankuna.

Haka kuma, gyaran tsofaffin matatu na gwamnati irin su Warri da Kaduna zai taimaka wajen kara wadatar man a cikin gida.

  • Tsarin farashi mai gaskiya

A kafa tsarin farashi na kasa domin tabbatar da gaskiya da daidaito. NNPCL ya rika sa ido domin hana ’yan kasuwa yin babakere ko boye man fetur domin kara farashi.

Dangote ya bude guraben ayyuka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kamfanin Dangote ya sanar da buɗe guraben aiki sama da 30 ga ‘yan Najeriya da suke da kwarewa a fannoni daban-daban.

Ana neman ma’aikata a sassa irin su wuraren sarrafa abinci, samar da siminti da sauran rassan kamfanin attajirin Afrikan, watau Aliko Dangote.

Daga cikin guraben da aka buɗe akwai shugabannin sassa, ma’aikatan tsaro, injiniyoyi da masu kula da jigilar kaya, kuma an bude kofa ga duk masu sha'awar aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com