Gwamnatin jihar Adamawa da Kamfanin Mai na NNPC zasu hada kai don samar da Makamashin zamani
- An sami karuwar bukatar a rage gurbata yanayi da muhalli a duniya, wanda ya haifar da neman sabuwar hanyar samo makamashi mai dorewa, maras guba.
- A Najeriya ma, dalibai da jami'o'i, sun fito da hazaqarsu, wajen samo wa Najeriya mafita, ta samar da ingatattun hanyoyin kona mai, maras guba.
- Jihar Adamawa, ta nuna sha'awar yin kan gaba, a harkar samo sabbin hanyoyi na samo makamashi domin habaka arzikin jihar.
A Jihar Adamawa, wani tsari na Mayine Sugar, na noma rake, matse shi ya zama suga, sannan a sarrafa sigan ya zamo mai me kama da na fetur, wanda ake kira ethanol, ya ja hankalin Kamfanin mai na kasa wato NNPC wanda har sun nuna zasu iya zuba jari na dala miliyan 100, $100m, Kwamishinan kasuwanci na jihar Alhaji Umar Daware, ya fadi hakan a tattaunawarsa da manema labarai a jihar. Ya kara da cewa, kwamitinsu da na kamfanin man na NNPC, zasu kafa alkalami domin ganin hakar ta cimma ruwa.
Ya kuma nuna cewa Gwamnatinsu a shirye take ta karbi masu zuba jari a harkar.
KU KARANTA KUMA: Dattawa sun maida martani game da kalaman gwamnan jihar Taraba
KU KARANTA KUMA: 2019: Mukaddashin shugaban kasa ya gana da shugaban INEC
Ita dai sabuwar hanyar samar da makamashin, ita ce take kokarin maye gurbin man fetur, wanda banda tsada, kuma da cewa ba'a iya sake juya shi, da zarar an kona shi, yawansa zai kare a rijiyoyin da ake hako shi a fadin duniya. Sabbin hanyoyin da a zamani aka gano zasu dore sun hada da kona makamashi kamar su man kade, sugar, da ruwan turare, wanda duk tsirrai ne ke iya samar dasu.
Ku biyo mu a shafin mu na twitter da Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Ko a Twitter https://twitter.com/naijcomhausa
An nemi Hukumar zabe ta karbe kujerar wani Sanata
Asali: Legit.ng