Dattawan Arewa Sun Yi Magana da Gwamnatin Legas Ta Yi Rusau a Kasuwar Alaba Rago
- Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta nuna damuwa kan rushe kasuwar Alaba Rago da gwamnatin jihar Legas ta yi da ya jawo asara
- Wannan rushe-rushe, a cewar ACF ta zama babbar barazana ga dubunnan ’yan Najeriya da ke dogaro da ita don rayuwarsu ta yau da kullam
- ACF ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Legas da ta kawo tallafin gaggawa ga wadanda abin ya shafa sannan a sake tattauna batun
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta bayyana damuwarta kan yadda gwamnatin jihar Legas ta rufe idanunta wajen rushe kasuwar Alaba Rago.
Kasuwar da ke karamar hukumar Ojo a jihar Legas, wuri ne da dubunnan 'yan kasuwa, musamman Hausawa daga Arewa ke kasuwanci.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa an fara rushe kasuwar ne dagar ranar Lahadi, 17 ga watan Agusta, har zuwa Laraba, 20 ga watan Agusta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dattawan Arewa sun koka da rusau a Legas
Tribune Online ta ruwaito cewa wannan rushe-rushe ya raba daruruwan ’yan kasuwa da wurin sana'arsu inda su ke samun damar rufa wa kansu asiri.
Kasuwar dai ta shafe kusan shekaru 50 a matsayin cibiyar cinikin kayan abinci, dabbobi da kuma sauran kayan bukatu.
A wata sanarwa da kakakin ACF na ƙasa, Farfesa Tanko Muhammad-Baba ya fitar ranar Laraba, kungiyar ta ce wannan mataki ya haddasa asarar kadarori da tsanantar talauci ga ’yan kasuwa.

Source: Facebook
Sanarwar ta ce:
“Rushe wannan kasuwa mai dimbin tarihi ya jawo durkushewar kasuwanci da kadarori, tare da rushe hanyoyin samun abinci ga dubunnan mutane."
Kiran dattawan Arewa ga gwamnati
ACF ta bayyana jin daɗinta ganin cewa babu asarar rayuka da aka yi a yayin rushewar, sannan ta yi jaje ga wadanda abin ya shafa.
Kungiyar ta ce:
“Muna sa ran juriya da aka san jama’an Arewa da shi za ta taimaka wa 'yan kasuwar wajen fuskantar kalubalen asarar da su ka yi."
Kungiyar ta kara da cewa ta fara tattara cikakkun bayanai kan abin da ya faru da dalilan da suka haifar da shi, tare da shirin tattaunawa da hukumomi da al’ummar da abin ya shafa.
ACF ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar Legas da gwamnatin tarayya da su dauki matakan gaggawa na kawo taimako da tallafi ga waɗanda suka yi asara.
'Yan Arewa sun yi asara a kasuwar Legas
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Legas ta kaddamar da rushe rushe a Kasuwar Alaba Rago, inda ta rusa sama da masallatai 40 da shaguna kusan 3,000 na ’yan Arewa.
Wannan kasuwa, wacce aka kirkira tun 1979, ta yi fice wajen kasuwancin kayan abinci, dabbobi, ƙarafa da sauran kayayyaki da akasari 'yan Arewa ne ke sana'arsu.
Gwamnatin ta fara wannan aiki ne tun watan Mayu 2024, kafin sabon rusau ya biyo baya daga 17 zuwa 20 ga watan Agusta, 2025, lamarin da ya jefa 'yan kasuwa a cikin takaici.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

