Tinubu Ya Hada Kai da Kungiyar Kasashen Musulmi, Za a Tallafawa Mata Miliyan 10 a Najeriya

Tinubu Ya Hada Kai da Kungiyar Kasashen Musulmi, Za a Tallafawa Mata Miliyan 10 a Najeriya

  • Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta shirya bai wa mata miliyan 10 horo na musamman kan harkokin noma a duk fadin Najeriya
  • Ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman Ibrahim ta ce an bar mata a baya a fannin noma duk da gudummuwar da suke bayar wa
  • Ta ce gwamnatin tarayya ta dauki mata musamman masu yin noma a matsayin wani ginshiki mai tasiri wajen ci gaban tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon.shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin tarayya ta kaddamar da gagarumin shiri da zai bai wa mata horo kan harkokin noma a fadin Najeirya.

Hakan dai na daya daga cikin kokarin da gwamnati ke yi wajen kawar da rashin daidaito da mata ke fuskanta a harkar noma a Najeriya.

Ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim.
Hoton ministar mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim a wurin taro a Abuja Hoto: @hm_womenaffairs
Source: Twitter

Ministar Harkokin Mata, Imaan Sulaiman Ibrahim, ce ta kaddamar da shirin a wurin taron karawa juna sani na kwanaki biyu da aka shirya wa mata a Abuja, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.

Kara karanta wannan

China ta ba da tallafin ambaliya, za a raba Naira biliyan 1.5 a jihohin Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda mata za su amfana da shirin a Najeriya

Shirin zai bai wa mata damar samun ilimi da ƙwarewa a fannoni daban-daban na harkokin noma domin bunkasa tattalin arzikinsu.

An kirkiro wannan shiri ne tare da haɗin gwiwar Kungiyar Ƙasashen Musulmi (OIC), karkashin ajendar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A wajen taron, Ministan ta bayyana shirin a matsayin wani mataki da zai zama juyin juya hali wajen tabbatar da daidaiton jinsi a fannin noma.

Ta ce lokaci ya yi da za a rushe shingayen da suka dade suna hana mata cikakkiyar damar amfani da basirarsu, rahoton TVC News.

Gudummuwar mata a fannin noma

“Mata ne ke taka muhimmiyar rawa a harkar noma a Najeriya. A halin yanzu, mata sun mamaye kashi 70 cikin 100 na ma’aikatan noma, su na samar da kashi 80 cikin 100 na amfanin gona .
"Duk da haka, abin da suke samu ya yi kasa da kashi 30 cikin 100 idan aka kwatanta da maza, kuma kashi 10% na mata manoma ne kadai ke da filayen noma, sannan ba a ba su rancen kudi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kara kawo sabon shiri, za a taimaki matasa miliyan 7 a Najeriya

- Imaan Sulaiman Ibrahim.

Wannan shiri zai gudana ne karkashin Women Agro Value Expansion (WAVE) Initiative, wani shiri da aka tsara domin tallafa wa mata miliyan 10 a fannoni daban-daban na noma.

Shirin zai ba su horo kan noman gidan gona, lambu, adana amfanin gona bayan girbi, ilimin kasuwanci, da kuma sarrafa harkokin kuɗi.

Imaan Sulaiman tare da mata a Nasarawa.
Hoton ministar mata, Imaan Sulaiman Ibrahim tare da mata a lokacin da Tinubu ya kai ziyara jihar Nasarawa Hoto: @hm_womenaffairs
Source: Twitter

Gwamnatin Tinubu ta hada kai da kungiyar OIC

Ministar ta jaddada cewa karkashin ajendar Renewed Hope, gwamnati na kallon mata a matsayin masu tasiri wajen bunkasa tattalin arziki, ba wai masu jiran taimako kawai ba.

Haka kuma, an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar aiki tare (MoU) tsakanin Ma’aikatar Harkokin Mata da OIC domin tabbatar da aiwatar da shirin cikin hadin kai.

Za a taimakawa matasa miliyan 7 a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta bullo da shirin da za a dauki matasa miliyan bakwai domin horar da su kan fasahar zamani a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Jima: An tunawa gwamnoni 19 hanyar da za su samu 'makudan kudi' a Arewacin Najeirya

Matasa miliyan uku daga ciki za su samu horo da gogewa a fannoni kamar fasahar AI, tsaro na yanar gizo da kuma kirkiro manhajar kwamfuta.

Ministan matasa ya ce matasa suna taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban kasa kuma wajibi ne a ba su horon abubuwan zamani.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262