An Nemi Amurka da Isra'ila Su sa Baki a 'Tsaron' Najeriya domin Sakin Nnamdi Kanu

An Nemi Amurka da Isra'ila Su sa Baki a 'Tsaron' Najeriya domin Sakin Nnamdi Kanu

  • Shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya rubuta wa shugabannin ƙasashe da ƙungiyoyin duniya don neman a sake shi
  • Mazi Kanu ya ce tsaresa tun daga 2021 ya saba wa dokar ƙasa da ta duniya tare da keta haƙƙinsa a matsayin ɗan ƙasa
  • 'Dan ta'addan ya zargi kotunan Najeriya da nuna son rai da karya kundin tsarin mulki wajen ci gaba da tsare shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya nemi taimakon shugabannin ƙasashen waje da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin ganin an sakesa daga hannun gwamnati.

Kanu, wanda ke tsare tun daga watan Yuni 2021, ya ce abin da ya faru da shi ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya da yarjejeniyoyin duniya kan kare ‘yancin ɗan adam.

Kara karanta wannan

2027: Kungiyar kiristoci ta CAN ta fitar da sanarwa kan yankan katin zabe

Nnamdi Kanu a wani zaman kotu da aka yi a Abuja tare da Trump da Netanyahu
Nnamdi Kanu a wani zaman kotu da aka yi a Abuja tare da Trump da Netanyahu. Hoto: Imrana Muhammad|Getty Images
Source: Facebook

Jaridar the Guardian ta wallafa cewa Kanu ya bayyana haka ne cikin wata wasika da ya aike ga shugabannin ƙasashe da dama ciki har da Donald Trump.

Nnamdi Kanu ya ce an zalunce shi

A cikin wasikar, Kanu ya ce shigar da shi Najeriya daga Kenya ya sabawa doka, kuma ya kamata hakan ya sa a rushe shari’ar da ake yi masa a kotun tarayya.

Ya yi nuni da cewa kotun daukaka ƙara ta riga ta yanke hukunci a 2022 cewa an tsare shi ba bisa ƙa’ida ba ce, amma daga bisani kotu ta amince da wani matakin da ya sa aka cigaba da tsare shi.

A cewarsa, wannan mataki ya nuna rashin amincewa da kundin tsarin mulki da kuma gazawar tsarin shari’a na Najeriya.

Zargin keta kundin tsarin mulki

Kanu ya bayyana cewa an tsare shi sama da wata 14 ba tare da tuhume-tuhume ba, lamarin da ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya da yarjejeniyar kare haƙƙin ɗan adam ta duniya.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: NNPCL ya gano hannun kungiyoyin kasashen waje a satar man Najeriya

Ya ƙara da cewa hukuncin kotun koli a ranar 15 ga Disamba, 2023, wanda ya rushe sakin da kotun daukaka ƙara ta yi masa a baya, ya zama babban keta doka.

Kanu ya zargi kotunan Najeriya da nuna son rai da amfani da shari’a wajen cimma manufar siyasa.

Nnamdi Kanu tare da wasu lauyoyinsa a kotu
Nnamdi Kanu tare da wasu lauyoyinsa a kotu. Hoto: Imrana Muhammad
Source: Twitter

Kanu ya yi kira ga Amurka da Isra'ila

Shugaban IPOB ɗin ya yi kira ga ƙasashen duniya da su matsa wa Najeriya don ta mutunta dokokinta, ta kuma bi hukuncin kotun daukaka ƙara na shekarar 2022.

Sahara Reporters ta rahoto cewa ya bukaci a soke matakin tsare shi da ya ce ba bisa doka ba ne, tare da tabbatar da sakin sa cikin gaggawa.

Kanu ya nemi taimakon kasashen duniya da suka hada da Amurka Canada, Jamus, Faransa, EU, Netherlands da kuma Sweden da Kenya.

Haka zalika ya yi kira da Afrika ta Kudu, Norway, Denmark, Japan, Brazil, Isra'ila, Finland, da kasar Austria da su shiga lamarinsa.

Har ila yau, jagoran na IPOB ya yi kira har ga kungiyoyin Amnesty International, Red Cross, AU da ECOWAS ta kasashen yammacin Afrika.

Kara karanta wannan

Makari: An fara ruguza yunkurin hada kai tsakanin malaman Izala da Darika a Najeriya

Amurka ta daure basaraken Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa wata kotun Amurka ta bayar da umarnin daure wani basaraken Najeriya daga jihar Osun.

Rahotanni sun nuna cewa an tsare basaraken ne bayan kama shi da laifin karkatar da kudin tallafin annobar Korona.

Baya ga tura shi kurkuku, kotun ta bayyana cewa za a kwace wasu muhimman kadarorin da ya mallaka da kudin da ya sace.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng