An Rage Mugun Iri, Jami'an DSS da Sojoji Sun Hallaka Rikakkun Ƴan Bindiga 50
- Rundunar jami'an farin kaya ta DSS tare da Sojojin Najeriya sun kashe yan bindiga da dama a Arewacin Najeriya
- Akalla yan bindiga 50 aka tabbatar sun mutu a karamar hukumar Mariga da ke Jihar Niger a Arewa ta Tsakiya
- Kakakin majalisar Jihar Niger, Abdulmalik Sarkin-Daji, ya yaba da jarumtar jami’an tsaro yana cewa sun nuna kwarewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Minna, Niger - Al'umma da dama sun samu sauki bayan hadin gwiwar jami'an tsaro sun yi fata-fata da yan bindiga.
Hukumar DSS da rundunar sojojin Najeriya sun samu nasara a yaki da ‘yan bindiga a Niger da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya.

Source: Twitter
An hallaka yan bindiga da dama a Niger
Rahoton Zagazola Makama shi ya tabbatar da haka a yau Laraba 27 ga watan Agustan 2025 da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun ce harin ya yi sanadin mutuwar akalla yan bindiga 50 inda suka kubutar da wadansa aka sace.
Lamarin ya faru ne ranar 26 ga watan Agusta a kauyen Kumbashi, Mariga, inda aka ce wannan shi ne mafi nasara cikin kwanakin nan.
Kakakin majalisar Jihar Niger, Abdulmalik Mohammed Sarkin-Daji, ya bayyana aikin a matsayin wanda aka nuna fasaha yana jinjina musu.
Shaidu sun shaida cewa yan bindiga 300 dauke da manyan makamai sun yi yunkurin mamaye Kumbashi da misalin karfe 3:00.
Sai dai jami’an tsaro sun fatattake su bayan musayar wuta, inda suka kashe fiye da 50, wasu kuma sun gudu da raunuka, Vanguard ta ruwaito.
“Mutanena sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kwashe gawarwakin abokanansu, suka saka a buhuna sannan suka dauke su da babura."
- In ji Sarkin-Daji
Kakakin majalisar, wanda ke wakiltar Mariga, ya kara da cewa an ceto mutum bakwai, tare da dawo da shanun da aka sace daga barayin.

Source: Original
Yadda aka cafke hatsabibin dan bindiga
Wannan ya biyo bayan nasarar hukumar DSS a Wawa, inda aka kama Abubakar Abba, shugaban kungiyar Mahmuda, daya daga cikin kungiyoyin ta’addan da aka fi tsoro.
A cewar mazauna yankin, wannan nasara ta kara musu kwarin gwiwa, ganin jami’an tsaro sun fafata da makiyaya masu rinjaye sau shida.
“Sun tsaya tsayin daka duk da cewa daruruwan yan bindiga sun kewaye su, da jarumtarsu, Kumbashi ya tsira."
- Cewar wani mazaunin gari.
Sarkin-Daji ya yi kira ga al’ummar jihar su ci gaba da ba da bayanai ga jami’an tsaro domin ci gaba da murkushe kungiyoyin miyagun.
Ya kuma tabbatar da cewa majalisar za ta ci gaba da tallafawa tsare-tsare na tsaro don tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar Niger.
Sojoji sun kashe yan bindiga a Sokoto
Mun ba ku labarin cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu 'yan ta'adda na kungiyar Lakurawa a jihar Sokoto.
Sojojin sun yi wa 'yan ta'addan kwanton bauna ne a karamar hukumar Tangaza lokacin da suka je sayen kayan abincin da za su yi amfani da su.
Karamar hukumar Tangaza na daga cikin wuraren da 'yan ta'addan Lakurawa suke addaba da kai hare-haren ta'addanci a jihohin Sokoto da Kebbi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


