Yadda Gini Ya Rikito kan Maƙwabta a Zariya, An Kwashi Gawarwaki 4 nan Take
- Jama'an Zariya a jihar Kaduna sun shiga jimami bayan rushewar gini ya yi ajalin uwa da ‘ya’ya uku a unguwar Karauka
- Lamarin ya auku ne da 3:30 zuwa 4:00 na Laraba a lokacin da bangon gidan makwabcinau ya fāɗa kan ɗakin da iyalan su ke kwance
- Nan take mutum hudu suka rasu, yayin da aka dauki mijinta marigayiyar, Mallam Nuhu Dogara, ranga-ranga zuwa asibiti
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kaduna – Rushewar katangar wani gida ya gigita mazauna Zariya a jihar Kaduna bayan lamarin ya jawo asarar rayuka.
Rahotanni sun tabbatar da cewa faduwar ginin ya yi sanadin mutuwar uwa tare da ‘ya’yanta uku.

Source: Original
Daily Trust ta wallafa cewa marigayiyar, Mallama Habiba Nuhu, ta riga mu gidan gaskiya tare da ‘ya’yanta biyu da kuma jikarta a unguwar Karauka.

Kara karanta wannan
Kudin fansa: 'Yan bindiga sun dauke mutum 4700, an ji biliyoyin da aka rasa a shekara 1
Yadda mutum 4 su ka rasu a Zariya
Wani ɗan uwa ga iyalan da suka rasu, Mallam Ahmed Ibrahim, ya bayyana cewa, lamarin ya faru a cikin dare.
A kalamansa:
“Lamarin ya faru tsakanin 3:30 zuwa 4:00 na safe a ranar Laraba lokacin da bango na gidan makwabcinsu na ginin kasa ya rufta ɗakin da suke.”
Ya ƙara da cewa:
"An ciro Malam Nuhu Dogara wanda shi ne mijin da kuma uban yaran da suka rasu da ransa, inda aka garzaya da shi asibiti don kulawar gaggawa. An sallame shi daga baya kafin a yi jana’izar matarsa da ‘ya’yansa.”
Lamarin ya jefa jama'a a cikin takaici da kunci yayin da aka yi jana'izar uwar da yaranta da jika kamar yadda Musulunci ya tanada.
Yadda mamakon ruwan sama ya jawo ruftawar gini
Mallam Ahmed Ibrahim ya danganta wannan mummunan hatsari ga mamakon ruwan sama da ake ta samu a Zariya.
Mutumin ya bayyana cewa mutanen da suka rasu sun riga mu gidan gaskiya nan take, domin tubalin gidan suka rufe su baki ɗaya.

Kara karanta wannan
Katsina: Yadda ƴan ta'adda su ka sace ɗiyar fitaccen ɗan kasuwar fetur da iyalinta
Ya bayyana sunayen yaran da jikansu da suka mutu kamar haka: Hauwa’u Nuhu, Aina’u Nuhu da kuma Za’uma.

Source: Facebook
A nasa bangaren, Bello Garba, wanda shi ne mai kula da shiyya ta daya na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA), ya ce bai samu cikakken labari kan batun ba.
Amma ya ce da zarar ya kammala samun rahoto, zai samar da jama'a cikakken bayanin yadda lamarin ya faru.
Gini ya rufta a kan dalibai a Yobe
A wani labarin, mun wallafa cewa mummunan hatsari ya auku a makarantar sakandaren mata ta gwamnati da ke Potiskum, jihar Yobe, inda bangon wani aji ya rushe.
Lamarin da ya afku ana tsaka da daukar darasi ya yi sanadin mutuwar wata daliba daga karamar hukumar Fika, yayin da wasu biyar suka jikkata.
Daliban da suka ji rauni a hatsarin su ne: Fatima Bala Adamu, wacce har yanzu ba ta farfado ba, Fatima Abba Idris, Hafsat Ahmed, Fatima Ibrahim da Hafsat Abubakar Maina.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng