Dino Melaye Ya Shiga Matsala, Gwamnati na Tuhumarsa da Kin Biyan Harajin N509m
- Ana zargin cewa tsohon sanatan Kogi, Dino Melaye ya shafe shekaru biyu yana guje wa biyan harajin kudaden da ya samu
- Hukumar haraji ta Abuja (FCT-IRS) ta ce Dino Melaye ya ki biyan harajin fiye da Naira miliyan 509 na kudaden shigarsa
- Yanzu haka dai an gurfanar da Dino Melaye gaban kotu, kuma zai iya fuskantar hukuncin biyan harajin da wasu tara da za a ci shi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An gurfanar da tsohon sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Melaye, a gaban kotun majistare ta Abuja bisa zargin kauce wa biyan harajin kuɗin shiga da ya kai N509,608,000.
A cewar bayanan kotu, Melaye bai biya harajin kuɗin shigarsa na 2023 da 2024 ba, inda bashin ya kai N234,896,000 a 2023 da kuma N274,712,000 a 2024.

Source: Facebook
Bayani game da harajin Dino Melaye
N509,608,000 shi ne jimillar kuɗin da hukumar haraji ta FCT (FCT-IRS) ta tantance kamar yadda rahoton TVC News ya nuna.
Hukumar FCT-IRS ta kuma ce a shekarun 2020, 2021 da 2022, Melaye ya rage kuɗin harajin da ya kamata ya biya, duk da irin kuɗaɗen da ya bayyana.
Misali, a 2020 Melaye ya bayyana cewa ya samu N1,383,334 amma ya biya haraji na N100,000.08 kacal. Haka ma a 2021 ya ce ya samu N1,550,000 amma ya biya N120,000.
A 2022 kuwa ya bayyana cewa N6,541,666.67 ya samu amma ya biya haraji na N1,000,000. A 2019 ma, lokacin yana sanata, ya ce ya samu N1,258,334 amma ya biya N85,000.08 kawai.
An yi karar Dino Melaye a kotu
Kotun majistare ta bayar da sammaci a ranar 21 ga Agusta 2025 inda ta umurci Melaye ya bayyana a gabanta a ranar 5 ga Satumba, 2025 a Wuse Zone II, Abuja.

Kara karanta wannan
Kudin fansa: 'Yan bindiga sun dauke mutum 4700, an ji biliyoyin da aka rasa a shekara 1
Rahoton Premium Times ya ce hukumar haraji ta aika wa tsohon sanatan takarda game da bashin haraji da ake binsa a 2023 da 2024, amma ya gaza yin martani cikin kwanaki 30.
Hukumar ta kuma bayyana cewa an manna masa dukkanin tuhume-tuhumen da ake yi masa a gidan sa dake Maitama ranar 9 ga Yuli 2025 bayan an ce ya ki karɓar takardun.
Hukumar FCT-IRS ta yi gargadi cewa rashin bin dokar da tsohon sanatan ya yi ya saba wa Sashe na 41 na Dokar Harajin Kuɗin Shiga ta 2011.

Source: UGC
Hukuncin da Dino Melaye ka iya fuskanta
Dokar Harajin Kuɗin Shiga ta 2011 (PITA) ta tanadi hukunci mai tsanani ga wanda ya kauce ko ya ɓoye kuɗin shigar da yake samu.
Idan hukumar ta ci nasara a kotu, Dino Melaye na iya biyan harajin N509.6m na kudin 2023 da 2024, sannan da ƙarin tarar shekarun 2020–2022, da tarar karya doka da za ta iya haura wannan adadin.
Rahotanni sun ce ba a samu damar yin magana da shi ba a safiyar Laraba, domin bai ɗauki kiran waya ko mayar da sakon da aika aika masa ba.
Dino Melaye ya yi bankwana da PDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Dino Melaye ya fice daga PDP a hukumance, yana mai cewa ba zai iya ci gaba da zama a cikinta ba.
A cikin wasikar da ya aikawa shugaban PDP na mazabarsa, Melaye ya zargi wasu manyan jam’iyyar da jawo lalacewar tsari da tasirinta.
Ficewar Melaye ta nakasa PDP a Kogi, yayin da ake hasashen zai koma jam’iyyar APC ko kuma ya shiga ADC domin takara a 2027.
Asali: Legit.ng

