Ba Dadi: 'Yan Bindiga Sun Kashe Mafarauta yayin Artabu a Neja

Ba Dadi: 'Yan Bindiga Sun Kashe Mafarauta yayin Artabu a Neja

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
  • Miyagun 'yan bindigan sun fafata da mafarauta a yankin bayan sun sace shanu a karamar hukumar Mariga ta jihar Neja
  • Musayar wutar da aka yi, ta jawo an samu asarar rayukan mafarautan da suka sadaukar da ransu wajen kokarin hana 'yan bindigan tafiya da shanun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - 'Yan bindiga sun hallaka mafarauta yayin wani artabu da suka yi a jihar Neja.

Akalla mafarauta takwas ne suka rasa rayukansu a lokacin musayar wuta tsakaninsu da wasu ‘yan bindiga a karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.

'Yan bindiga sun kashe mafarauta a Neja
Hoton jami'an 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun kashe mafarauta a Neja

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: 'Yan majalisar PDP sun taso Tinubu a gaba kan tsadar rayuwa

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, 26 ga watan Agustan 2025.

Wasu gungun ‘yan bindiga masu yawa dai sun mamaye kauyen Hunyo/Sabon Wuri da ke cikin gundumar Dusai Mahoro a karamar hukumar Mariga, inda suka yi awon gaba da wani adadi mai yawa na shanu.

Majiyoyi sun bayyana cewa bayan da ‘yan bindigan da suka sace shanun, kuma sai suka yi kokarin tserewa da su.

Sai dai, mafarautan yankin sun yi masu kwanton ɓauna tsakanin kauyukan Kakihum da Kumbashi.

Hakan ya janyo artabu mai zafi, inda aka yi musayar wuta tsakanin bangarorin biyu. A yayin artabun, mafarauta guda takwas sun rasa rayukansu.

Majiyoyin sun kara da cewa har yanzu ba a tantance sunayen waɗanda suka mutu ba, haka kuma ba a samu cikakken bayani kan gidajen da suka fito ba.

'Yan bindiga sun kai hari a Neja
Taswirar jihar Neja, tarayyar Neja Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sandan Neja sun kai dauki

Bayan samun labarin faruwar lamarin, jami’an ‘yan sanda na Mobile Force da aka tura a Bangi, tare da tawagar sintirin sashen ‘yan sanda da ‘yan sa-kai na yankin, a karkashin jagorancin DPO sun nufi wurin cikin gaggawa domin tabbatar da doka da oda.

Kara karanta wannan

Ana jimamin hatsarin jirgin kasa, 'yan bindiga sun kashe mutane a Kaduna

Bayan jami'an tsaron sun isa wurin, an dauki gawarwakin waɗanda suka mutu aka kai su babban asibitin Bangi, inda za a gudanar da binciken gawa.

Karanta wasu labaran kan hare-haren 'yan bindiga

'Yan bindiga sun kashe mutane a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a wasu kananan hukumomi guda biyu na jihar Kaduna.

'Yan bindigan wadanda suke dauke da makamai sun hallaka mutane takwas tare da raunata wasu daban, bayan sun bude wuta kan mai uwa da wabi.

Gwamnatin jihar Kaduna ta jajantawa iyalan wadanda lamarin ya ritsa da su, ta dora alhakin harin kan 'yan bindigan da ke jihohin da ke makwabtaka da ita.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng