Katsina: Yadda Ƴan Ta'adda Su ka Sace Ɗiyar Fitaccen Ɗan Kasuwar Fetur da Iyalinta
- Wani al'amari ya tayar da hankalin mazauna jihar Katsina bayan ‘yan ta'adda sun haura wani gida a cikin gari
- Lamarin ya faru da misalin 3:00 na dare a Filin Canada Quarters, Sabuwar Unguwa, a jihar Katsina
- Rahotanni sun bayyana yadda aka haura gidan, su ka kuma banƙara tare da garkuwa da su duka ƴan gidan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – A safiyar ranar Talata, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari a Filin Canada Quarters, Sabuwar Unguwa, birnin Katsina.
Yayin wannan mummunar ziyara, ƴan ta'addan sun sace mutum uku a wani gida tare da kashe wani ɗan sa kai da zai kai agaji.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 3:00 na dare a gidan Anas Ahmadu mai shekaru 33, inda aka sace shi, Halimat, da ɗiyarsu, Jidda Anas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan ta'adda sun kai farmaki Katsina
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Halimat mai juna biyun akalla watanni bakwai, ƴar wani shahararren ɗan kasuwa ce a jihar Katsina.
Rahotanni sun ce duk da cewa an samu hare-hare a sassan jihar, wannan shi ne karo na farko cikin kusan shekaru biyu da ake samun irin wannan lamarin a babban birnin.
A yayin harin, wani ɗan sa-kai mai suna Abdullahi Muhammad, mai shekaru 25, da aka harbe shi a yayin kai agaji ya rasu.
Wata majiya ta ce, matar Halimat ‘yar Alhaji Usman Turare ne, ɗan kasuwa mai zaman kansa a harkar man fetur wanda ke da gidajen mai da yawa a jihar.
Ta ce:
“Mijinta matashin ɗan kasuwa ne amma ba na ganin shi su ka kai wa harin.
Yadda ƴan ta'adda su ka kai hari
Wata majiya ta ce ‘yan bindigan da yawa ne suka mamaye gidan ma’auratan da misalin 3:00 na dare, sannan su ka sace su.

Kara karanta wannan
Mazauna Katsina sun karyata ikirarin gwamnati na kubutar da su daga hannun 'yan ta'adda

Source: Original
Ya ce:
"Wasu ƴan bindiga guda bakwai sun hau katangar gidan suka buga masu ƙofa suna cewa a buɗe.
Ya kara da cewa:
“Kafin su shiga, matar ta kira ɗan sa-kai domin neman taimako, amma wasu ‘yan bindiga da suka ɓuya a cikin duhu sun harbe shi har lahira.
“Ta shiga ban-ɗaki bayan ta fahimci za su shiga gidan da ƙarfin tsiya, yayin da mijin yake ƙoƙarin tserewa ta ƙofar baya."
“Sun shiga gidan, sun ɗauki mijin, sun buɗe ƙofar banɗakin da karfi, suka sace su, har da ɗiyarsu mai shekaru biyu."
Wani makwabcinsu ya ce sun ji ‘yan bindigan suna magana kasa-kasa kamar su na karbar umarni daga wanda ya yi masu jagora.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun tuntubi ɗan uwan matar da 9:00 na dare jiya.
Wata majiya ta ce:
“Amma, ban sani ko sun nemi kuɗin fansa ba."
Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya kuma ce ana ɗaukar matakin da ya dace.

Kara karanta wannan
'Yan Majalisa da Sanatoci 50 da suka dumama kujera, ba su da gudumuwa a shekara 1
Ɗan majalisa ya saya wa mutanensa bindigu
A wani labarin, mun wallafa cewa Ɗan majalisar jihar Katsina mai wakiltar mazabar Funtua, Hon. Abubakar Muhammad Total, ya sayawa mutanensa makamai.
Abubakar Muhammad Total ya bayyana cewa matakin wani ɓangare ne na aikin raya mazaba, inda jama’a suka nemi agajinsa bayan sun gaza jure hare-haren ‘yan ta’adda.
Game da yiwuwar sasanci, Abubakar Total ya ce mutanensa ba su da adawa da sulhu muddin hakan zai kawo zaman lafiya.mai dore wa ga mazauna yankuna daban daban.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
